Yadda na shafe wata 4 a gidan yarin Saudiyya bisa kazafin safarar kwaya – Abubakar Ibrahim

Malam Abubakar Ibrahim shi ne mutumin da kasar Saudiyya ta tsare shi tswon watannin hudu bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi. A wannan tattaunawa da Aminiya, ya bayyana irin ukubar da ya fuskanta a lokacin zaman gidan kaso.   Hukumar Saudiyya ta tsare ka tare da wata baiwar Allah mai suna Zainab Habib Aliyu tsawon watanni […]

Yadda na shafe wata 4 a gidan yarin Saudiyya bisa kazafin safarar kwaya – Abubakar Ibrahim

Malam Abubakar Ibrahim

Malam Abubakar Ibrahim shi ne mutumin da kasar Saudiyya ta tsare shi tswon watannin hudu bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi. A wannan tattaunawa da Aminiya, ya bayyana irin ukubar da ya fuskanta a lokacin zaman gidan kaso.

 

Hukumar Saudiyya ta tsare ka tare da wata baiwar Allah mai suna Zainab Habib Aliyu tsawon watanni hudu bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi zuwa kasa mai tsarki. Ko za ka fada mana yadda wannan al’amari ya faru?

Lamarin ya faru ne tun daga filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano lokacin da Alhaji Haruna wanda shi ne mai nusar da ni yadda zan aiwatar da lamarin tafiyar tawa zuwa kasa mai tsarki. Shi ya dauke ni zuwa filin jirgin saman na Malam Aminu Kano ya hada ni da wani mai suna Abdulkadir, wanda shi ne yake rike da fasfona. Ya ce masa ga ni ya kawo masa ni domin ya shirya min yadda zan tafi. Wannan tafiyar ita ce ta farko a gare ni don haka ina bukatar wanda zai nuna min yadda zan yi. To shi Abdulakadir shi ya sayo min wani kati da ake kira “Yellow Card” a turance. A lokacin da ya karbi kudin sai ya ce min in bi shi, don haka a nan na bar jakata muka je muka siyo katin da shi. Bayan da muka dawo ne sai ya yi min jagora zuwa wajen da jami’an tsaro ke binciken kayan matafiya; ya nuna min inda zan ajiye jakata, na kuma ajiye ta. Jakata na dauke da kayan sakawa ne guda uku sai kuma Alkur’anina bugun hannu a ciki.

Daga nana muka hau jirgi zuwa kasar Itofiya, muka sauka a babban birnin kasar wato Addis Ababa, sannan aka canza mana jirgi wanda zai kai mu kasar Saudiyya. A duk tsawon wannan lokaci jakata na tare da ni kuma duk inda ake bincike mun je an bincike ni babu wani abu na laifi a tare da ni.

A Jidda sai wani mutum ya tarbe mu ya ce mana mu bakinsa, ne don haka ya nuna mana motar safa wadda za ta kai mu Madina. Duk abin nan da ake muna tare da Zainab da ’yan uwanta amma duk ba mu san juna ba. Bayan mun isa Madina aka kai mu musaukinmu, muka kwanta bayan da muka yi Sallolinmu.

Can cikin dare sai na ji wani na buga mana kofa. Da na bude sai ga wannan mutumin da ya karbe mu a jidda tare da wasu mutane sanye da dogayen riguna. Suka tamabaye ni ko ni ne Abuabakar Ibrahim, na ce musu eh ni ne. Sai suka ce min in ba su fasfona, sai na ce musu yana cikin jakata. Juyawar da zan yi domin in dauko fasfon nawa sai kawai na ji daya daga cikin mutanen nan ya kama hannayena ya garkama min ankwa. Sai suka ce min wai na shigo da miyagun kwayoyi kasar Saudiyya, don haka za a tafi da ni domin a yi bincike. Haka aka tasa keyata zuwa ofishinsu a nan Madina.

Muna can sai ga wata mata mai suna Zainab Muhammad Ala, wadda ita ake zarginta da shigowa da miyagun kwayoyi. Sai dai a lokacin da ake shigo da wannan mata ta dage kan cewa ita fa ba ita ce wadda ake zargi ba, domin wadda ake zargi sunanta Zainab Habib Aliyu, ita kuma sunanta Zainab Muhammad Ala. Bayan da suka dade suna Turanci da ita sai aka sallame ta. Sai can daga baya aka zo da Zainab Habib Aliyu tana ta kuka. Da muka hadu sai na tambaye ta me ta yi ne sai ta fada min cewa wai ana zarginta ne da shigowa da miyagun kwayoyi, sai na fada mata cewa ni ma abin da ake zargina da shi ke nan amma ni ban aikata ba. Ita ma ta rantse min cewa ita ma ba ta aikata wannan laifi ba don haka sai na yi ta rarrashinta domin na ga hankalinta ya yi matukar tashi. Na ce mata ta yi hakuri ta dangana komai ga Allah. Haka muka kwana a ofishin ma’aikatan nan a zaune, ba tare da mun runtsa ba. Da safe sai aka dauke mu zuwa Jidda. A kan hanyarmu ta zuwa Jidda sai aka kira Zainab a waya, don haka suka mika mata wayar ta amsa, ashe babarta ce ta kira sai ta fada mata cewa an tafi da mu Jidda.

A Jidda ma dai ofishin masu yaki da fataucin miyagun kwayoyi aka kai mu, aka hannanta Zainab ga wata ma’aikaciya mace, ni kuma ga namiji. Aka karbe fasfo dina da sauran takarduna na tafiya da kudadena, aka sanya cikin wani babban ambulan aka ajiye a wurin jami’an tsaron. Daga nan aka kai ni gidan kurkuku bangaren maza, a inda na shafe kwanaki 93 ba tare da na san Zainab na cikin gidan ba, domin ita tana bangaren mata ne, ni kuma ina bangaren maza kamar yadda na shaida maka a baya. Amma Allah cikin ikonSa duk da cewa ban san Zainab na cikin gidan yarin ba ashe ita duk lokacin da suka yi magana da babanta sai ta jaddada masa cewa idan ya tashi yin kokarin fitar da ita, to ya hada da ni.

Bayan da na shafe wadannan kwanaki 93 a gidan kaso, sai aka dauke ni zuwa wani gidan yarin daban, wanda ke tsakanin Makka da Jidda da ake kira Hilesa, wanda aka yi musamman domin ajiye masu laifi ’yan kasashen ketare. A wanan gidan yari na shafe kimanin mako uku kawai. An saki Zainab a ranar 30 ga watan Afrilu ni kuma an sake ni a ranar 1 ga watan Mayu. Sai dai ita Zainab ta yi sa’a, domin lokacin da aka sallame ta, an danka ta ne a hannun jamai’an Ofishin Jakadancin Najeriya da ke kasar Saudiyya amma ni kuwa turin-jeka-ka-ka-mutu aka yi mini.

Abin da nake nufi da haka shi ne, ni sallamata aka yi kawai, aka ce min tafi an sallame ka ba tare da an hannanta ni ga wani jami’in Najeriya da zai kula da ni ba. An bayyana min cewa an yi min haka ne domin a lokacin da aka sallami Zainab, jami’an kasar Saudiyya ba su ji dadin yadda aka kwarzanta lamarin ba a kafafen watsa labarai, don haka da za a sallame ni sai da aka bari dare ya tsala sai aka fito da ni, aka ce min in tafi an sallame ni. Don haka lokacin da na fito daga gidan kason, ban ma san inda zan nufa ba kuma ga shi ba ni da ko kwandala kuma ga ba Larabci ba Turanci. Don haka ban san abin da zan yi ba kuma ba ni da wani mai taimakona in ban da Allah.

Allah cikin ikonSa a lokacin da aka salleme ni, an sallame ni ne tare da wani bawan Allah dan kasar Senegal, wanda shi kuma ya shafe shekaru biyar a gidan kason. Duk da bambancin yare amma sai da muka zama kamar ’yan uwan juna da wannan mutumin a wannan lokacin. Don haka muka fito tare da shi muka tsaya jiran mota har wani tsawon lokaci amma ba mu samu ba. Muna cikin wannan hali ne sai Allah Ya kawo wasu mutane su biyu cikin mota suka tsaya sai, dan Senegal yana bayyana musu halin da nake ciki kuma aka yi sa a daya dga cikin mutanen yana dan jin Hausa kadan. Don haka muka yi magana da shi. Ya fada min cewa za su je Makka ne amma sai na shaida masa cewa ban taba zuwa ba, hasali ma ban san ko’ina ba a kasar. Sai shi wannan bawan Allah ya nemi in ba shi lambar wayar dan uwana a Najeriya, na kuma ba shi. Ya kira shi ya ba ni muka yi magana da shi. Bayan da aka bayyana masa wurin da zai kai ni, sai aka yi sa’a daya daga cikinsu ya san wurin a Jidda. Don haka sai ya yi wa dan Senegal bayanin wurin kuma aka dace shi ma ya san wurin. Wadannan mutane suka rage mana hanya zuwa inda za mu samu motar haya, suka sauke mu. Ka ji rabuwar mu da su wadannan bayin Allah.

Bayan da muka sauka a Jidda muka nemi wannan wuri da aka yi wa dan Senegal kwatance wato Khartina, wanda kuma dandali ne na ’yan Najeriya. To daga nan ne fa na fara samun saukin damuwa a raina, domin na ga ’yan uwa ’yan Najeriya.

Da isar mu na bayyana musu halin da na sami kaina da kuma dalilin zuwana wurin, sai suka nuna farin cikinsu kuma suka kawo abinci suka ba ni na ci na sha na koshi. Bayan da na kammala cin abinci ne kuma sai muka fara yin hotuna da su kala-kala, domin nuna farin cikinsu. A wannan hali ne kuma Ofishin Jakadancin Najeriya ya sami labarina. Don haka aka aiko da jami’ai da mota aka dauke ni zuwa can. Bayan da aka kai ni sai aka nuna min makwanci mai kyau, na je na yi wanka na huta sannan Jakadan Najeriya a Saudiyya ya zo wurina tare da wani jami’i. Ya dauke ni zuwa gidansa na kwana, ya umarce ni da in huta. Ya kuma kawo tufafi kala biyu ya ba ni. Muka yi kalaci tare da shi sannan aka kai ni ofishinsa.

Amma wani abu guda da zan shaida wa duniya shi ne, ba zan taba yafe wa wadanda suka jefa ni a wannan mummunan hali da na sami kaina ba a kasa mai tsarki. Ina nan ina musu addu’a kuma ba zan fasa ba tsawon rayuwata, Allah Ya bi mini hakkina.

 

Shin ko ka sami sukunin yin aikin Umara bayan da aka salleme ka daga gidan yarin?

Ba sahkka na sami sukunin yin Umara, domin Jakadan Najeriya da kansa ya dauke ni tare da Zainab ya kai mu Makka domin gudanar da aikin Umra. Alhamdu lillahi, mun yi Umra bayan da aka sako mu daga gidan kaso.

 

Yaya rayuwa ta kasance a gidan yari?

Wai! Ai Allah kadai Ya tsare mu a cikin gidan yari, domin kuwa ba don kariyar Ubangiji ba da komai ma zai iya faruwa. Na farko dai tun da Allah Ya sa aka kai ni gidan kaso ban taba cin abinci na koshi ba, domin abincinsu bai dace da yanayina ba, don haka ban a iya ci in koshi. Ba dandano, ba gishiri, ba yaji, salaf yake ba wani dandano. Ni kuma ban saba da abinci irin wannan ba, don haka ba na iya ci sosai. Ni dai kawai na dukufa ne kan addu’o’i, Allah Ya kawo min sauki.

 

Kasancewarka Bahaushe yaya mu’amillarka ta kasance da sauran aboann zamanka na gidan yari?

Ba shakka ni kadai ne dan Najeria a bangaren da nake, sauran ’yan kasar Saudiyya ne da Pakistan da Bangaledash da dai sauransu. Duk sun iya yin magana da Larabci, in ban da ni kadai kuma ba wanda ke iya fahimtar harshen Hausa a cikinsu. Don haka zaman dai ba dadi domin ba ni da abokin hira a cikin abokan zamana.

 

Ko ka san laifin da ake zarginka da aikatawa a duk tsawon wannan lokacin?

Kwarai da gaske, domin kuwa an kai mu kotu lokuta da dama kuma ana kawo mai yi mana bayani da harshen Hausa, domin mu fahimci abin da ake tuhumarmu a kansa. A wannan hali ne aka fada min cewa ana zargi na ne da shigo da kwayoyin gudu 1000 kasar Saudiyya, wanda ni kuma na shaida musu cewa ban aikata wannan laifi ba; domin kuwa ban san wani abu makamancin haka ba kuma ban san wanda ya aikata haka da sunana ba.

 

Ko kana da sha’awar komawa kasa mai tsarki idan har ka sami wata dama ta yin hakan?

Gaskiya ba zan koma ba a yanzu. Hasalima ko da zan ce zan koma to mahaifiyata ba za ta amince ba, domin irin damuwar da ta shiga a lokacin da na tsinci kaina halin da na shiga a can kasa mai tsarki. Amma bayan wani lokaci zan iya komawa domin a matsayina na Musulmi ba ni da wani buri da ya wuce in ziyarci kasa mai tsarki. Amma a yanzu ba ni da niyyar komawa a nan kusa.