Yadda na shirya majigin Baban Larai – Abdullahi Abubakar
Baban Larai suna ne da ya yi tashe a cikin wani majigi da aka fitar a lokacin mulkin mallaka da bayan samun ‘yancin kai a arewacin kasar nan. a wannan hirar da wakilinmu ya yi da Baban Larai, wanda sunan sa na asali shi ne Abdullahi Abubakar, kuma yanzu haka yana zaune a garin Yola […]

Baban Larai suna ne da ya yi tashe a cikin wani majigi da aka fitar a lokacin mulkin mallaka da bayan samun ‘yancin kai a arewacin kasar nan. a wannan hirar da wakilinmu ya yi da Baban Larai, wanda sunan sa na asali shi ne Abdullahi Abubakar, kuma yanzu haka yana zaune a garin Yola jihar Adamawa, ya yi bayanin yadda shi da wadansu turawan Ingila suka shirya majigi don wayar da kan manoman Arewa don bunkasa aikin noma a arewacin kasar nan, musamman noman auduga, a shekarar 1951.
Aminiya: Ka fada mana sunanka da kuma tarihinka?
Baban Larai: Sunana Abdullahi Abubakar, an haife ni a garin Song da ke lardin Adamawa a wancan lokaci, yanzu jihar Adamawa, kuma ina da shekaru sama da 81, na i makarantar elimantare a garin Song, na wuce zuwa makarantar “Middle” a garin Yola.
Daga nan na tafi Kongo a Zariya, a lokacin ana kiran makarantar Kongo “Clerical collage,” na gama makarantar a shekarar 1947, daga nan na kama aiki a Kaduna. Shi ya sa mu ‘yan Arewa na wancan lokaci muka san junanmu, domin duk wanda ya kammala makaranta Kaduna za shi a dauke shi aiki. Amma da yawa daga cikin mutane sun fi sanina da Baban Larai, kuma wannan sunan ya dauko asali ne shekaru masu yawa a can baya.
Aminiya: Me ya sa aka sa maka wannan suna?
Baban Larai: Wannan suna ne na sinima ku kuma na fim, watau da turanci ana nufin “script name,” a shekarar 1951 lokacin ina aiki a Kaduna sai turawan mulkin mallaka a Ingila suka fahimci cewa akwai karancin auduga a Manchester inda masakunsu suke. Saboda haka akwai matsala ke nan, domin idan babu auduga to babu abin da masaku za su sarrafa ke nan wajen yin tufafi. Ganin haka sai gwamnatin Ingila ta ce a bai wa kasashen da suke karkashin ikonta kuma masu noma auduga kudi don su farfado da noman auduga.
A wancan lokacin muna karkashin mulkin mallaka, kasashen da suke karkashin mallakar Ingila wadanda ke noman auduga sun hada da Sudan da Najeriya da Masar da sauransu. Sai aka raba kudade ga wadannan kasashe aka ce kowa ya yi dabarar yadda zai farfado da noman auduga. A Najeriya sai aka ga yakamata a yi fim, watau majigi (kamar yadda aka fi sani a can baya) na bunkasa noman auduga. A wancan lokacin ni ina aiki a sashin wayar da kan jama’a a Kaduna a matsayi akawu, watau “Clerk,” ana neman wanda zai yi wannan aiki tare da turawan Ingila wadanda aka turo kasar nan don wannan aiki. Turawa biyu suka zo, daya mai daukar hoto, watau “Camera man,” daya kuma darakta na yin fim, kuma sun zo da kayan aiki. Da suka iso Ikko sai aka ce su zo Kaduna domin a Arewa ne ake noman auduga.
Da turawan suka iso Kaduna sai aka ce a kai su sashin ayyukan wayar da kan jama’a, ni kuma a nan nake aiki, sai dai aikin akawu nake yi. Aka nemi wanda zai yi aiki da wadannan turawa amma ba a samu ba. Sai ni na ce ina son in yi wannan aiki, amma manyanmu suka ce ‘kai ba maganar wasa ake yi ba’.
Aka yi ta neman wanda zai yi wannan aiki amma aka rasa, ni kuma na adage cewa zan iya wannan aiki.To ganin ba a samu wanda zai iya wannan aiki ba sai aka ce ai Abdullahi Abubakar ya ce zai iya, sai aka kira ni aka ce to sai in bi wadannan turawan mu tafi mu gwada. Saboda haka sai tafi dakina, na tattara kayana muka tafi Zariya. Da kuma tafi Zariya sai aka hada ni da Abubakar Imam a nan gidansa a Tudun Wada, muka zauna kwana da kwanaki , ya tambaye ni, in tambaye shi.
To ni a wancan lokaci kaina bai waye ba, amma ka san shi Malam Abubakar Imam mutum ne haziki mai ilimi da basira mai yawan gaske. Muna nan dai har muka gama rubuta yadda fim din zai kasance, watau ‘Script.’ Kuma Malam Abubakar Imam ya ce sai a sanya wa fim din suna Baban Larai.
Yanzu kuma sai yaya tunda mun kammala rubuta script? sai wadanda za su yi fim, watau actors da kuma inda za’a dauki fim, watau locations. Amma samun wuraren da za a dauki fim babu wuya, abin da ya fi wahala shi ne mutanen da za a yi amfani da su wajen yin fim din. Da ’yan mata da manoma da gonakin auduga da za a su fita a cikin fim din duk ni zan nema.Wannan ba karamin aiki ba ne, sai nan dukufa wajen neman ’yan fim da gonakin auduga. Na tafi Gusau da Funtuwa da Bakori da Shika da dai sauran wurare. A wannan aikin ne na san marigayi Sarkin Zazzau Malam Ja’afaru, da shi muka fara wannan fim din. To sai na shiga neman wanda zai zama Baban Larai a fim din amma na gagara samu.Su kuma turawa sun fahimci cewa zan iya aikin mai jagoran fim din wanda zai amsa sunan Baban Larai, amma ba su da ikon su ce in yi. Sai su turawan suka tafi ofishin mu a Kaduna suka fad awa shugabana cewa ai zan iya rike wannan matsayi na Baban Larai. Sai shugabanmu ya kira ni ya tambaye ni cewa mai ya sa ba a fara fim din ba, ni kuma na fada masa samun wanda zai zama baban Larai watau “main character” ne ya gagara. A nan ne shi shugabanmu ya ce ai kai za ka iya, saboda haka ka tafi ka zama Baban Larai a wannan fim din, na ce to, amma abin akwai wuy, a domin turawan nan da su yarbawa da suka rako su daga Ikko zuwa Kaduna ko Hausa ba sa ji, ni ne zan yi komai da komai dangane da wannan fim.
Ta haka ne muka fara. Da farko sai muka tafi Funtuwa, ka san a wancan lokacin ta hanyar shiga garin Funtuwa daga Zariya akwai manya-manyan gonakin auduga. A Bakori kuma, garin ne wanda a tsare yake, ga layi-layi masu kyau.Dama irin wannan wuri muke so don daukar fim wanda zai bayar da sha’awa.
Mun yi zumunci da mutanen Bakori a dalilin wannan aiki kuma sun taimake mu wajen shirya wannan fim. Shi Hakimin Bakori na wancan lokacin, watau Tukur ya taimake mu da duk abin da muka nema don tafiyar da shi wannan fim daga nan ne na samu wannan suna na Baban Larai.
Aminiya: Me ya sa aka sawa wannan fim suna Baban Larai kuma wani abu ne ku ke son ku cimma, watau ina nufin manufarku?.
Baban Larai: Manufarmu ita ce mu wayar da kan manoma don su kara himma wajen aikin noma, masamman noman auduga, kuma mun ci nasara.Tun wancan lokacin har yanzu ba a sake fim irin wanda muka yi ba, kuma har yanzu yana nan kamar yau aka yi shi.Kuma ka san cewa a kowane fim akwai “main character,” to ka ji amfanin shi wannan suna na Baban Larai, wanda har yanzu mafi yawan mutane da wannan suna suka san ni.
Aminiya: To wane alfanu shi wannan fim ya bai wa aikin noma a arewacin kasar nan?
Baban Larai: Wannan fim ya kawo sanadiyyar bunkasa noman auduga wanda ya sa har kasar nan ta kasance tana sayar da auduga a kasuwanin duniya. Ta haka ne ya sa tattalin arzikin Arewa ya bunkasa gwamnatin Arewa ta samu kudin shiga masu yawan gaske.Kuma manoma suka saui arziki mai yawan gaske. A wancan lokacin an bude fulotin auduga a garuruwa masu yawan gaske ana hada-hadar kasuwar auduga, mutane kuma suka samu aikin yi.
Jama’a sun sami kudi, wadansu sun gina gidaje, wadansu sun sayi kekuna, wadansu Babura, sa’anan kuma idan ka je wurare kamar su Zariya da Funtua da Gusau, za ka iske dalar auduga wanda ake turawa zuwa kasuwannin kasashen waje da kuma wanda masana’antu gurza za su sarrafa. To wannan shi ne cigaba, kuma wannan shi ne manufar wannan fim na Baban Larai.
Na biyu kuma shi ne, masakun gida kamar su Arewa Tedtile da makamantansu, suka bunkasa, ’yan Arewa suka samu aikin yi. Amma yanzu haka abin yake? ina audugar? kusan dukkan masaku a rufe suke yanzu.
Aminiya: Gashin yanzu an bari aikin noma ya lalace a Arewa kuma babu wani yunkuri da ake yi don farfado da aikin noma a Arewa, me kake ganin yakamata a yi ?
Baban Larai: Duk gwamnatin da ta ce ba za ta inganta aikin noma ba to ta cuci Arewa. An ce wai Arewa ba mu da man fetur, kuma gashi kasashen Nijar da Chadi da Kamaru sun samu man fetur, amma an ce ba mai a Arewa. Amma muna da filayen noma a ko’ina a Arewa, kuma noman nan dai shi ne hanyar da za a samu arziki mai dorewa a Arewa da ma kasa baki daya. Saboda haka ya zama tilas a koma ga aikin gona, musamman a Arewa, don bunkasa tattalin arzikin kasa da cigaba mai dorewa.