Yadda na tsere da daga hannun ’yan bindiga —Mai shayarwa

Na’imah, ta ce tsalle ta yi tare da danta daga kan babur din ’yan bindigar

Yadda na tsere da daga hannun ’yan bindiga —Mai shayarwa

Wata mace mai shayarwa ta tsere tare jaririnta dan wata shida daga hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

Malama Na’imah Bashar ne daga cikin mata biyar da suka samu tserewa daga hannun masu garkuwa da mutane da suka sace su a kauyen Dan Isa da ke Karamar Hukumar Kaura Namoda a jihar.

Sakataren Hakimin yankin Dan Isa, Malam Hassan Isa ya ce matan sun koma kauyen ne a ranar Litinin.

Da take ba da labarin irin halin da ta tsinci kanta a ciki, Na’imah, ta ce tsalle ta yi tare da danta daga kan babur din ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita da sauran mutanen da suka dauka daga kauyen.

Ta ce: “’Yan bindigar sun yi mana dukan tsiya a lokacin da suke tafiya da mu a kan baburansu.

“Akwia wasu mutane biyu da suka samu raunukan harbin bindiga; An goge daya da harsashi a kai, dayan kuma ya samu rauni a ciki.

“Ina matukar godiya ga Allah sosai; wannan shi ne kawai abin da zan iya cewa. Da yardarSa na tsere.”

Yadda ’yan bindiga suka sace su

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kai hari kauyuka da dama a karamar hukumar suka sace jama’a gami da hallaka wasu.

Sakataren Hakimin yankin Dan Isa, Malam Hassan Isa, ya ce adadin wadanda aka kashe karu zuwa biyar sakamkon gano wata gawa a daji a ranar Litinin.

Malam Hassan, wanda aka fi sani da Yarima, ya ce: “Ya zuwa yanzu, an tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutane 99 a ranar Lahadin, amma muna ci gaba da tattara sunayen saboda an kai harin ne a kauyuka daban-daban.

“Wannan shi ne karo na uku da ’yan bindigar ke kai hare-hare a kauyukan yankin nan a cikin ’yan kwanakin nan.

“Sun kai hari wani kauyen Maguru da ke makwabtaka da mu a ranar Litinin, 8 ga Yuli, 2024, sannan a ranar Asabar suka kai wa Dogon Kade hari; washegari Lahadi 14 kuma suka kai hari kauyen Dan Isa.

“A Litinin sun zo sun harbe mutum daya wanda a halin yanzu yake jinya a babban asibitin Kaura Namoda.

“Sun sake dawowa sun yi awon gaba da dabbobi da kayan abinci da mutane da suka hada da mata da yara.

“Wannan shi ne hari mafi muni da muka taba gani a tarihin wannan kauyen.

“Bayan harin, babu mace ko daya da take kwana a kauyenmu.

“Yan kungiyar ’yan banga ne kawai da wasu maza suke kwana a kauyen, sauran kuma suka bar gidajensu domin tsira.”

Halin da ake ciki

Dangane da halin da kauyen ke ciki, Yarima ya ce: “Na rantse da Allah a halin yanzu ba mu da abincin da za mu ci a kauyen.

“Mun yi sa’a a safiyar yau (jiya), daya daga cikinmu da ke zaune a Legas ya ba mu gudummawar burodi 100 wanda muka raba wa ’yan tsirarun mutanen da suka dawo kauyen.”

Wani mazaunin kauyen ya ce an binne gawarwakin wadanda aka kashe a harin a ranar Litinin 15 ga watan Yuli.

“Dole sai da muka nemi kariya daga jami’an tsaro mallakar jihar Zamfara da aka fi snai da Askarawa da kuma ’yan banga don gudanar da jana’izar.

“Wasu mutane da dama sun samu raunuka a lokacin harin mara dadi, cikinsu har da wata mace mai ciki wadda ta samu karaya a kafarta.”

Daga ’yan sanda

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Zamfara kan harkokin yada labarai, Mustapha Jafaru Kaura, ya tabbatar da faruwar harin, ya kuma koka da yadda ake ci gaba da kai hare-hare duk da kokarin da gwamnatin jihar ke yi na dakile ’yan fashin daji.

“Gaskiyar magana, gwamnatin jihar Zamfara tana yin iya kokarinta, su ma mutane suna yin iya kokarinsu wajen kare kansu, amma lamarin shi ne a mafi yawan lokuta maharan sun fi yawan mazauna kauyukan da suke kai hari.

“Hukumomin tsaro su tashi tsaye su sauke nauyin da ke kansu.

“Gwamnatin jihar Zamfara na samar musu da bukatunsu amma duk da haka, ana ci gaba da kai hare-haren musamman a yankunan karkara.

“Don haka, jami’an tsaron da aka tura yankunan karkara dole ne su sauke nauyin da ke kansu na kare mutane,” in ji shi.

Ya tuna cewa gwamnatin jihar ta bullo da wasu tsare-tsare da nufin inganta tsaro, amma duk da haka ana ci gaba kai hare-hare.

“Misali, gwamnatin jihar, ta haramta zirga-zirgar babura daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe, daga ranar Litinin, 15 ga Yuli, 2024 da nufin dakile hare-haren ’yan bindiga da daddare, kuma saboda da babura suke amfani wajen gudanar da ayyukansu.

“A baya, gwamnati ta sanya dokar hana zirga-zirga da dare a kan iyakokinta da jihohin Katsina da Sokoto, kuma hakan ya rage yawan sace-sacen mutane a kan manyan hanyoyin Funtua-Gusau da Gusau-Sakkwato.

“Gwamnatin jihar ta kuma haramta sayar da man fetur a jarkoki da  kuma rufe kasawannin da barayin shanu ke zuwa a fadin jihar.”

Kaura, wanda ya jajanta wa wadanda harin ya rutsa da su ya kuma yi kira da su rika kai rahoton duk wani motsin da ba su gamsu da shi ba ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin da ya dace.