Yadda na tsira a gobara da taci wanda ya dauko ni—Pamela Mamza

Misis Avohre Pamela Mamza, wata mata ce da ta tsira daga mutuwa a lokacin da ake goye da ita akan babur na achaba sa’ilin da shi kuma dan achabar ya kone kurmus a hadarin tankar man fetur a Unguwar Tumfure a jihar Gombe. Misis Pamela, ta ce da idon ta taga mutuwar domin ta hau […]

Yadda na tsira a gobara da taci wanda ya dauko ni—Pamela Mamza

Misis Avohre Pamela Mamza, wata mata ce da ta tsira daga mutuwa a lokacin da ake goye da ita akan babur na achaba sa’ilin da shi kuma dan achabar ya kone kurmus a hadarin tankar man fetur a Unguwar Tumfure a jihar Gombe.

Misis Pamela, ta ce da idon ta taga mutuwar domin ta hau achaba daga shataletalen kamfanin Mai na NNPC wato Damfon Mai zuwa Tumfure suna tafiya sai taji karar wannan tankar mai a bayan su tace, dan achabar ya tsaya a lokacin tsayarwa da yake yi sai tankar mai din taci karo da wani bodin babbar mota da aka ajiye a gefen hanya su kuma suka bugi bayan tankar suka zube ta tashi da kyar ta fita da gudu shi kuwa dan achaba ya kasa tashi wuta ta cinye shi.

Gobarar Unguwar Tumfure a jihar Gombe

Wani da lamarin ya faru akan idonsa Usman Saleh, ya ce wannan bodin babbar mota da ke gefen hanya shi ya jawo wannan hadarin da har dan achaba da fasinjar da ya dauko su, suka fadi Allah Ya kiyaye fasinjar mace ce bata mutu ba amma shi dan achabar ya rasa ransa a lokacin da suka yi ta kokarin ceto shi amma Allah bai nufa ba.

Sakataren Kungiyar agaji ta Red Cross na jihar Gombe UB Ahmed, ya ce su dai mutum daya suka ciro da suka kai asibiti dan likitoci sun duba ko ya mutu ko yana da rai domin Red Cross ba ta iya tantance gawa sai likita ya duba anan za’a gane ya mutu ko bai mutu ba.

Har zuwa aiko da wannan labarin bamu iya jin ta bakin Hukumar kare hadura ta kasa ba haka suma jami’an kashe gobara ba mu iya samun ji daga gare su ba.

Gobarar Unguwar Tumfure a jihar Gombe