Yadda na xauki nauyin karatuna da sana’ar qere-qere – Injiniya Aliyu
Aminiya ta samu tattaunawa da wani matashi mai suna Injiniya Aliyu Musa wanda ya kammala karatunsa a vangaren injiniya a Jami’ar Amadu Bello da ke Zariya. Aliyu wanda yake gudanar da sana’ar Tinka wato Qere-qere a Abuja, ya bayyana yadda ya xauki nauyin karatunsa da sana’arsa ta qere-qere Aminiya: Za mu so ka gabatar da […]
Aminiya ta samu tattaunawa da wani matashi mai suna Injiniya Aliyu Musa wanda ya kammala karatunsa a vangaren injiniya a Jami’ar Amadu Bello da ke Zariya. Aliyu wanda yake gudanar da sana’ar Tinka wato Qere-qere a Abuja, ya bayyana yadda ya xauki nauyin karatunsa da sana’arsa ta qere-qere
Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Ni asalin iyayena ’yan garin Biu ne da ke jihar Barno ne, amma ni a unguwar Samarun Zariya aka haife ni a Jihar Kaduna shekaru 28 da suka gabata ke nan. Na fara makarantar firamare ta Ma’aikatan Jami’ar ABU bayan na kammala sai na tafi sakandaren gwamnati mai suna G.S.S Chindit Barrack da ke Sabon Garin Zariya. Bayan na gama sai na rubuta jarrabawa da ban sami gurbin karatu a jami’a ba sai na tafi na yi diploma a cibiyar ilimi ta jami’ar ABU. Bayan na kammala sai na sami gurbin karatun digiri a jami’ar, inda na karanta fannin injiya na sarrafa qarfe da dangoginsa wato Metallurgical and Materials Engineering. Yanzu har na kammala ina bautar qasa a garin Mangu da ke Jihar Filato.
Aminiya: Waxanne qalubale ka fuskanta a lokacin da ka haxa sana’arka da karatu?
Gaskiya na fuskanci qalubale iri-iri. Ka san ita rayuwa idan ka yi lissafin lokaci sai ka fi samun sauqi a ciki. Saboda haka na tsara lokutana yadda sana’ata ba za ta shafi karatuna ba. Yadda nake yi ina yin sallar Isha da misalin qarfe takwas zan yi karatun sa’a biyu. Sai na kwanta na yi barci idan na yi sallar asuba sai na sake yin karatu na awa biyu. Haka ma da rana idan na samu lokaci shi ma zan yi na sa’a biyu amma idan ban samu ba, ba na yi. Ba na kwana ina karatu. Sannan lokacin da nake sakandare ba na zuwa birek wato cin abinci sai na zauna a cikin aji na yi karatu. A rana ina yin karatun awa shida kem nan. Wani qalubale da na fuskanta a lokacin ina karatu a jami’a shi ne na yankewar kuxi. Dole na daina kwana a makaranta na dawo gida. Ina yin sana’ata a hannun xaya kuma ina karatu.
Aminiya: Kana nufin tun daga sakandare har jami’a kai ka xauki nauyin karatunka?
Eh haka ne. Ni na xauki nauyin karatuna tun daga sakandare har jama’i’a. Saboda tun lokacin da mahaifina ya yi ritaya a shekarar 1998 ni nake xaukar nauyin karatuna. Kuma na dage na yi karatu saboda na taimaki iyayena wata rana.
Aminiya: Me ya ba ka qwarin gwiwa ka yanke shawarar komawa karatu duk da kana da sana’a?
Tun lokacin da muke yara a unguwarmu a Samaru muna ganin mutane suna zuwa yin karatu Jami’ar ABU. Sukan fito mu yi mu’amala da su. A yanzu duk sun zama manya, wasu na koyarwa a jami’a wasu kuma na yin ayyuka a wasu wurare. Waxanda suke yin ayyuka a wurare daban-daban sukan kawo mana ziyara da manyan motoci. Sai na riqa tambayar mahaifiyata cewa ya nake ganinsu da manyan motoci bayan a da ba su da mota. Sai ta ce mani ai =kai ma idan ka yi karatu za ka iya zama kamar su har ka fi su. Sai ta riqa bani qwarin gwiwa. Ko kafin ta rasu wasiyyar da ta bar mini shi ne cewa na yi karatu. Wanna shi ya sa na dage na rufe ido.
Aminiya: Kana da sha’awar bayan ka kammala bautar qasa ka yi aikin albashi ko kuma za ka ci gaba da sana’arka?
Ni yanzu ina da burin idan na kammala bautar qasa na koma na yi digiri na biyu. Sannan idan na kammala zan nemi kuxi na buxe babbar masana’anta ta sarrafa qarfe yadda zan buqasa sana’ata sosai yadda za mu riqa qera abubuwa daban-daban. Amma qalubalen da nake fuskanta shi ne na rashin jari. Shi ya sa ina so idan na samu dama na yi aikin albashi ko da na shekaru 15, yadda zan samu fansho da kuma kuxin sallama mai yawa. Sai na yi amfani da shi na buxe babban kamfani. Kuma ina da burin na riqa zuwa qasar China na koyo yadda ake sarrafa qarfe ta hanyar zamani don na bunqasa sana’ata.
Aminiya: Wace shawara za ka bai wa matasa a yanzu da ba su son yin karatu?
Shi ilimi abu ne mai albarka kuma duk abin da ka sanya a zuciyarka cewa za ka yi to babu shakka za ka iya yinsa. Ka xauka cewar duk abin da xan Adam zai yi kai ma za ka iya. Kuma idan mutum ya rubuta jarrabawar WAEC ko NECO bai ci ba, to kada ya yi qasa a gwiwa ya sake rubutwa, ya yi ta gwadawa idan Allah Ya yarda zai yi nasara. Akwai mutane da yawa da suka yi fice a yanzu waxanda sai da suka zana jarrabawa sau da yawa sannan suka yi nasara. Ko Wole Soyinka an ce ya rubuta WEAC sau tara bai yi nasara ba a na taran ya ci jarrabawar.Yau gashi ya zama wani abu a duniyar karatun boko.
Aminiya: Wane abu ne ya faru da kai wanda ba za ka tava mantawa ba a lokacin da kake karatu?
Gaskiya ba zan tava mantawa da abin da ya auku da ni lokacin da muka zo qarshen karatunmu a jami’a. A lokacin da na fara rubuta binciken qarshe na samun digiri. A lokacin damina ne, ga shi babu ciniki ka san lokacin damina ba ma samun ciniki a sana’armu. Abubuwa duk sun tsaya mani, ba ni da kuxi, na rasa yadda zan yi. Wani lokaci sau xaya nake cin abinci sai dai na qarasa da ruwa. Saboda matsaloli na rashin kuxi sai na dakatar da rubutun littafin zuwa shekara ta gaba. Na tattara kayana na dawo Abuja na ci gaba da yin sana’ata, na tara kuxi na koma makaranta na ci gaba da rubuta bincikena. Na yi bincikena a kan yadda ake rage tsatsa a jikin qarfe da dangoginsa.
Aminiya: Ka ce idan ka kammala bautar qasa za ka ci gaba da karatu, a wane fannin kake so ka yi digirinka na biyu?
Ina so na yi karatuna na digiri na biyu a fannin da na yi na farko wato kan sarrafa qarfe da dangoginsa. Idan na kammala zan ci gaba na zama farfesa a vangaren sarrafa qarfe da dangoginsa.
Aminiya: Yaushe ka fara wannan sana’ar?
Na koyi sana’ar tun ina yaro. Kuma sha’awa ce ta sa na koya. Na koyi sana’ar a Zariya. Kuma ina qera abubuwa da yawa kamar injin gasa biredi daban-daban qanana da manya da risho da sauransu. Kuma ina samun alheri mai yawa.