Yadda na yi jinyar COVID-19 har na warke —Minista
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Mista Geoffery Onyeama ya bayyana yadda ya kamu da coronavirus ya yi jiyyarta har tsawon makonni uku kafin ya warke. Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin jawabin kwamitin kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa don yaki da annobar karo na 57 a Abuja. Ministan dai ya bi sahun sauran fitattun […]
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Mista Geoffery Onyeama ya bayyana yadda ya kamu da coronavirus ya yi jiyyarta har tsawon makonni uku kafin ya warke.
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin jawabin kwamitin kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa don yaki da annobar karo na 57 a Abuja.
Ministan dai ya bi sahun sauran fitattun ’yan Najeriya da suka kamu da cutar inda aka tabbatar ya harbu a ranar 19 ga watan Yuli bayan an yi masa gwaji a karo na hudu.
Geoffrey ya ce, “A gaskiya zan iya cewa kwamitin nan na kar-ta-kwana kamar wani babban sashe ne a gidan sojoji. Da farko dai kusan babu wanda ya kamu da ita a cikin ’ya’yansa.
“Amma yanzu da daya daga cikinmu ya kamu za mu iya bayani kan abun da muka shaida da kanmu ba abun da muka ji daga bakin wasu ba.
“Tabbas cutar COVID-19 gaskiya ce. Nakan yi amfani da matakan kariya har hawa uku amma hakan bai hana ta kama ni ba.
“Babu wani dalilin da zai sa a kyamaci mutum don ya kamu da ita, saboda kowa ma zai iya kamuwa.
“Coronavirus ba tarkon mutuwa ba ce. A banagarena, ina jin sauyi a jikina ranar wata Juma’a na garzaya aka yi min gwaji washegari,” inji Geoffrey.
Ministan ya kuma yaba wa jami’an lafiyar da suka yi jinyarsa a cibiyar killace mutane, yana mai cewa abun alfahari ne kasancewarsu ’yan Najeriya kuma sun cancanci yabo.