‘Yadda na yi kwana guda a tsare ba tare da laifi ba’

Wani magidanci da ke zaune a birnin Ibadan da wasu jami’an tsaro suka kama shi ba tare da ya aikata laifin komai ba, suka kai shi hedikwatar ’yan sanda ta Legas, ya bayyana yadda suka nemi ya ba su Naira miliyan 5 a matsayin kudin beli daga hannunsa. Magidancin da aka sakaya sunansa saboda wasu […]

‘Yadda na yi kwana guda a tsare ba tare da laifi ba’

Wani magidanci da ke zaune a birnin Ibadan da wasu jami’an tsaro suka kama shi ba tare da ya aikata laifin komai ba, suka kai shi hedikwatar ’yan sanda ta Legas, ya bayyana yadda suka nemi ya ba su Naira miliyan 5 a matsayin kudin beli daga hannunsa.

Magidancin da aka sakaya sunansa saboda wasu dalilai, ya shaida wa Aminiya irin yadda ya gane wa idanunsa mutanen da aka kama cunkushe a cikin babban dakin tsare mutane, inda wasu ma a tsaye suke yin barci saboda babu wurin kwanciya.

Bayanan da magidancin ya yi wa Aminiya sun shafi kamen da aka yi masa ne da irin cunkoson mutane a cikin sel da aka tsare shi na tsawon kwana daya kafin a sallame shi, ba tare da biyan ko kwabo kudin beli ba. Ya ce, hakan ya biyo bayan tsoma bakin wani babban jami’in ’yan sanda ne wanda ya bayar da umarnin a hanzarta sallamarsa domin babu laifin da ya aikata.

Da yake karin bayanin yadda abin ya faru, ya ce: “Haka kawai ina zaune a cikin kasuwarmu, a Unguwar Sabo Ibadan sai wadannan jami’an tsaro dauke da bindigogi suka zo suka kama ni, suka ce suna neman wasu na’urorin sanyaya daki guda 8 da janareta 5 da aka sace, aka sayar mani a matsayin kayan sata. Na nemi sani da ganin barawon da suka ce ya sayar da kayan gare ni amma suka kasa nuna shi. Suka sanya mani ankwa a hannayena, suka tafi da ni zuwa hedikwatar ’yan sanda da ke Ikeja a Legas suka garkame ni a cikin dakin tsare mutane. Sun nemi kudi Naira miliyan 5 a matsayin kudin beli.

“Babban abin da ya ba ni mamaki da ban haushi, shi ne yadda wadannan jami’an tsaro suka kasa kawo mutumin da suka ce ya sayar mani da wadannan kayan sata. Wannan ya nuna gaskiyar zargin da ake yi wa jami’an tsaro a Najeriya na kamen mutane domin karbar kudi a hannunsu ba tare da sun aikata laifin komai ba. Ya kamata mahukumta su dauki matakan yin gyara a kan irin wannan al’amari na cin hanci da rashawa da yake bata sunan jami’an tsaro a kasar nan.”

Ya ce wasu abokan sana’arsa ne suka hanzarta mika wannan matsala ga wani babban jami’in ’yan sanda, wanda ya yi bincike ya gano cewa babu kamshin gaskiya ko kadan dangane da kamen da aka yi masa. Shi ne ya bayar da umarnin a sallame shi ba tare da bata lokaci ba. “An sallame ni ba tare da biyan ko kwabo ba. Babu wani yunkuri da na yi na zuwa kotu domin neman hakkina, sai dai na bar komai ga Allah da mika godiya ga wannan jami’in dan sanda wanda ya kubutar da ni,” inji shi.

A kan irin yadda ya samu kansa a cikin dakin tsare mutane (cell) tare da wasu manyan mutanen da aka kama ake zarginsu da aikata laifuka, sai magidancin ya kada baki ya ce: “A lokacin da aka ingiza keyata zuwa cikin wannan daki, na tarar da mutane fiye da 70 a ciki. Wasu a zaune wasu kuma a kwance tare da wadanda suke tsaye suna barci a jikin bango. Akwai shugaban tsararrun da ake ba shi kudi ya sama wa sabon zuwa wurin kwanciya da ake manne kamar kifin gwangwani. “Daga cikin mutanen da na tarar a cikin wannan daki, har da fitaccen mutumin nan Ebans da aka kama, ake zarginsa da satar mutane da garkuwa da su da neman kudin fansa.”