Yadda na zama cikin ’yan amshin Shata na farko – dan-Musulmi
Alhaji Sulaiman Usman wanda aka fi sani da dan-Musulmi dattijo ne da ya ga jiya ya ga yau, kuma shi ne marokin Firimiya na farko, sannan yana daya daga cikin yaran Mamman Shata na farko. Ya fadi yadda Shata ya fara yin suna da yadda ya sha da kyar. Yaya aka yi ka samu wannan […]
Alhaji Sulaiman Usman wanda aka fi sani da dan-Musulmi dattijo ne da ya ga jiya ya ga yau, kuma shi ne marokin Firimiya na farko, sannan yana daya daga cikin yaran Mamman Shata na farko. Ya fadi yadda Shata ya fara yin suna da yadda ya sha da kyar.
Yaya aka yi ka samu wannan suna dan-Musulmi?
Dalili shi ne kishiyar mahaifiyata A’isha ce ta sa min sunan tun ina goye. Cewa ake A’isha ce ta haife ni amma sunan mahaifiyata shi ne Adama. Kowane daki nawa ne. Tun ban da wayo har aka yaye ni. A da ana zama na mutunci ba irin na mutanen yanzu ba. Shi ne har yau duk inda ka ce dan-Musulmi an fi sanina da sunan.
Wato dai ba a bariki aka sanya maka wannan suna ba?
A’a da abina aka gan ni.
Kai mutumin ina ne?
Ni mutumin kauyen Alimawa ne da ke karkashin garin Uran a karamar Hukumar Dawakin Kudu da ke Jihar Kano. Daga nan kakannina suka dauko ni suka kawo ni Malladan a zamanin Sarkin Kano Inuwa yana Ciroma.
Na yi zama a Kano a Malladan da kul-kul da Kamfanin Gurasa da Fan Turawa.
Shekarunka nawa yanzu?
Za su kai shekara 106 da wata takwas.
Mene ne sirrin da gashi kana tafiya ba sanda?
Da ikon Allah, ina zuwa masallacin Juma’a a kasa. Ina zuwa Kabalan Gabas don yin zumunci, sannan in dawo gida amma fa ranakun Juma’a. Hakorina daya ne ya balgace. Sannan karfin ido ya ragu, don ina gani ne hazo-hazo. Amma har yanzu ina cin nama da kashi.
Wannan sana’a ta roko gado ka yi?
Sunan mahaifina shi ne Malam Usman dan Baza Wanzami. Gadon gidanmu wanzanci, kuma har yanzu ina da wukar (askar) gado. Ina iya yin aski. Na haifi wadanda suka yi aski har suka rasu. Ina da askar gado, amma ba na yin wanzanci.
Yaya aka yi ka shiga roko?
Wani aminina mai suna Muhammadu Kawule dankusa ne ya sa ni. Tun muna kanana na fara roko.
An ce kai ne marokin Sardauna, yaya aka yi kuka hadu?
Da na zo Kaduna lahirar makwadaita sai na fara bin Idi Na-Kumbo mai gogen Sardauna daga titin Katsina zuwa gidan Sardauna a kasa muna yin wasa har tsakar dare. Lokacin nan ba gida daga gari wato Doka zuwa Unguwar Sarki. Ba motar haya. Shi Idi yana goge ni kuma ina yi masa roko. Ta haka muka saba da Sardauna, ina yi masa kirari.
Wane kirari kake yi wa Sardaunan Sakkwato?
Ina cewa:
“Gamji dan kwarai dan Hamza, Sa Ahmadu Bello ikon Allah, Mujaddadi dan Mujdadddi jikan Mujaddadi Usmanu,
Shawarar Firayi Minista Abubakar Tafawa balewa, dan Yakubu, jikan Yakubu, Baban Bala da Binta, Bauchi ama (kamar) Yola, tauri naman kai Bagaruwa ta Yakubu.”
Mun yi yawo tun kafin a rarraba Najeriya. Da aka rarraba ta sai muka yi waka muna cewa ba don fushi aka yi ba, sai don a zauna lafiya. Kuma a yanzu daga cikin mutanen gidan Sardauna daga ni sai Ali Sarkin Mota muka rage a duniya.
Yaya aka yi kuka hadu da Shata?
Mu muna ce masa A-shata mai anini ne aka mayar da shi Shata. Tun daga Malamfashi muna zuwa Fawwa. Yana sanye da binjima (babbar riga) da gajeren wando yana talla yana asayyara. Da ni aka samu yaran. Da amshi nake har na dawo mai zaman kaina ina roko. Ina yi masa kirari ina cewa:
Tubli kabuli na Bilkin Sambo.
Babu sauran wani maroki a gabanka.
Babu saura sai kai kadai.
Shata Ikon Allah!
Da farko dan Auta ke yin sharar fage, bayan ya rasu sai na dauka. Ina yin sharar fage da wannan kirari. Shi dan Auta tare suka tashi a gidajen iyayensu tun suna yara a Musawa. A kwari inda kainuwa take. Har ya bar duniya. Duk inda Shata ya saka kafa da ni ake. Sannan aka zama mutane biyar. Da Abubakar da Ibrahim da Manya sai ni, sai dan Indo ya rasu. Sannan na fita daga amshi na koma maroki mai cin gashin kaina.
Mene ne abin mamaki da ya taba faruwa tsakaninka da Shata?
A gagarumin bikin ’yar Sarki a Kano, lokacin Sarki Sunusi muna tare lokacin ana waka da asiri, a zamanin shahararrun maroka da mawaka a Kano su ne Hamisu Maiganga da dan Ado da Abatta da Chaji da Dabalo. Da ya zo ya zauna zai yi waka, sai ya sunkuyar da kai bayan wani asiri ya zo kamar buzuzu ya makale shi, sai na mike ina yi masa kirari ina cewa:
“Shata ikon Allah,
Duna na Bilkin Sambo,
Yaya aka yi ka sunkuyar da kai,
Ka tashi ka yi waka.”
Da asirin ya warware sai ya fadi, nan da nan Shata ya tayar da kai ya ce
“Ni ne Shata ikon Allah,
Duna na Bilkin Sambo,
Na hana Hamisu, Na hana Chaji, na hana Dabalo ya daina”
Sai muka tafa hannu muka ce
“Har abadin abada”
Wane irin asiri ne?
Asirin shi ne wanda ake yi don neman Allah Ya karya abin da kake nema a sana’ar har ya lalace. Amma ni na dace don ba na fada, an dauki kowa abokin arzikina ne.
Ko kana da karin bayani dangane da wakokin Bakandamiya?
Dalilinta shi ne a bikin ’yar sarki a Kano inda ya yi wa kansa kirari. Sannan ya yi wa ’yan uwansa inda yake cewa Shata kanen idi yayan Yalwa. Sai kuma rigimarsu da abokinsa Sarkin Magana. Dalilan suna da yawa daya shi ne don Allah ya daga Sarkin Magana, na biyu kuma don sun rabu da mata mai suna Hajiya Yalwa, sannan Sarkin Magana ya aure ta. Ina daya daga cikin wadanda suka dauko Sarkin Magana a garin dandume inda kasuwa ke ci ranar Lahadi muka hada su da Shata. Da ni aka yi neman auren Hajiya Yalwan Shata.
Ka san harkar mawaki, shin ko ya yi wa Sarkin Magana zambo?
Lallai Shata ya yi wa Sarkin Magana zambo a cikin Bakandamiya inda yake cewa:
“Haka nan ne Mamman kanen Idi, wan Yalwa.
“In ka ga mutum yana burun-burun.
“Haka nan ne Mamman kanen Idi, wan Yalwa.
“Da babban riga kamar mahaukaci,
“Haka nan ne Mamman kanen Idi, wan Yalwa.
“Aminun mutum biyu, munafikin mutum daya.”
“Haka nan ne mamman kanin Idi, wan Yalwa
Ni amininsu ne, amma ba zan dauki zancen wannan in kai wa wancan ba, na sha hada su don a yi sulhu, amma ina, ina cewa su bar abin nan komai ka gani daga Allah ne.
Ko ka san shi Idin yayan Shata?
Na san shi, amma shi ba ya kida ko waka ko roko.
NEPU ka yi ko NPC ganin kai mutumin Malam Aminu Kano ne da Sardauna?
Lokacin ina gida ina NPC amma zan je wurin Malam Aminu Kano mu yi ta hira muna dariya tun bai san zai haihu ba. A lokacin nan za a dauko dan NEPU a zo kofar Mata a cire dararsa a yi masa aski a yanka darar a ce sai ya cinye, shi kuma dan NEPU ya yi ta kuka ya ce zai dawo NPC.
Me ya sa ka rabu da Shata ka dawo roko gadan-gadan?
Ba mu rabu da shi ba ko da ’ya’yansa. Har na daina yawo na dawo roko tare muke. In an gan ni a cikin garin Kaduna wato Doka ko a wani gari sai a ce Shata ya zo. Domin ni nake zagayawa ina yin shela idan Shata ya zo za a yi wasa. Ina cewa ‘Mai sisi mai taro in ma ba ka da kudi ka zo.’ Ni na hada Shata da Mammalo Shata da Musa danbade.
Me ya sa ake cewa ka na jin dadin zama a Kaduna?
Lokacin yakin Ojukwu an hana yawon dare, idan na dawo wasa da na isa inda masu damara ko soja ko ’yan sanda da na ce dan-Musulmi ne sai a gaishe ni a kuma rako ni har gida a Kabala.
An ce a da in an ba mutum fili balle ku masu yawo maroka sai mutum ya ce ba ya zo zama ba ne a Kaduna, yaya aka yi ka zauna?
Na je wajen wani, Malam Uba a Kabala lokacin ana ce mata Kabalan Kashi, sai ya ce min in sayi fili Naira hamsin, na saya amma ba da niyyar in gina in zauna ba, na ce yaushe zan zauna a Kabalan Kashi. Daga baya sunan ya rikide ya koma Kabalan Kwastin (Costain sunan wani kamfanin gine-gine ne). Domin lokacin nan ina zaune a cikin gari a Titin Katsina. Lokacin da na tare gonaki ne zagaye da gidana, sai gidan Alhaji Mati daf da rafin Kaduna.
Yaya ka ji rasuwar Shata?
Shata yana ziyartata da ’yarsa mai suna Lami, yana addu’ar Allah Ya sa ya mutu a Kano a gidan da Wamban Daura ya ba shi. Wata rana ina zaune a nan sai ’yarsa ta zo ta ce in shiga mota. Na ce dalili, ta ce in shiga mota kawai, sai na shiga. Ba mu tsaya ba sai a Kano, ta kai ni wurin gawar Shata. Na bude gawarsa na ce, “Allah Ya jikansa, na ce sai na zo.” Da ni aka yi jana’izarsa.
Yaya aka yi ka je Makka?
Sadik Mamman Legas da Kobon Wushishi suka biya min Makka har sau biyu daban-daban. Da na je wurin yin fasfo saura kwana biyu a rufe, nan da nan aka tsayar da mutane aka yi min don an san ni, ko kuma da an fadi sunana sai a ce in wuce ba bin layi. Na yi furi, na yi maimai, saura sassarya. In an biya min yanzu zan ce a ba ni kudin in gyara gidana don na yi gobara.
Iyali fa?
Ina da mata biyu, ta uku ta rasu. Duk kuma sunan mahaifiyata suke da shi wato Adama. Ina da ’ya’ya 13 masu rai da jikoki da sauransu da dama. dan autana sunansa Awwal shekararsa takwas.
Kana da magaji?
Ina rokon kada in samu magaji, mai yin roko don nan gaba in ka ce wa mutum “dan wane jikan wane!” Sai mutum ya ce ina ka san shi? Ba na fata dana ya yi roko, sai dai a roke shi.