‘Yadda na zama dogariya a fadar Zazzau’

Kamar yadda jama’a suka sani kusan duk abin da namiji ya yi fice  a kai idan aka yi sa’a mata ma sukan yi fice a kai. Saboda da haka sanin kowa ne cewa a kusan duk masarautun da ke yankin arewacin kasar nan suna da Dogarai   maza ne, domin aiki ne na jaruntaka, amma abin […]

‘Yadda na zama dogariya a fadar Zazzau’

Aisha, Sarkin dogarai mataKamar yadda jama’a suka sani kusan duk abin da namiji ya yi fice  a kai idan aka yi sa’a mata ma sukan yi fice a kai. Saboda da haka sanin kowa ne cewa a kusan duk masarautun da ke yankin arewacin kasar nan suna da Dogarai   maza ne, domin aiki ne na jaruntaka, amma abin mamaki sai gashi an samu mace dogariya a fadar Mai martaba Sarikin Zazzau, Alhaji Shehu Idris da ke Zariya, mai suna A’ isha Usman. Wakilinmu ya tattauna da wannan dogariya wacce ita ce Sarkin Dogarai mata domin jin yadda aka yi ta zama dogariya mace:

Daga Aliyu Babankarfi a Zariya

Aminiya: Za mu so ki bayyana mana sunanki da kuma matsayinki.
 A’isha:  Da farko ina farawa da sallama, sunana Aisha Usman kuma ni ce Sarkin Dogarai mata.
Aminiya: Malama Aisha Sarkin Dogarai, ta yaya ga ki mace amma aka dauke ki a matsayin dogariya?
Aisha: To ni dai ina zaune ne sai aka ce za a yi  nadin dogariya mace ko ina sha’awa? sai na ce kwarai kuwa ina so, kuma kamar yadda suka ba ni labari cewa a masarautar Katsina akwai mata Dogarai , kuma Sarkin Dogaransu ma mace ce, kuma yadda aka yi mahaifinta shi ne Sarkin Dogarai  na Sarkin Katsina to ba shi da da namiji sai mace, don haka aka nada ta ta gaji mahaifinta,  kuma an ga irin yadda suke gudanar da aikinsu kuma suna bayar da gudumuwa kamar yadda ake bukata, don haka aka ce mu ma ya dace a yi Dogariya mace. Ka ji yadda aka yi aka nada ni Dogariya, kuma ni aka fara nadawa kafin a nada sauran matan.
Aminiya: To ranki ya dade Sarkin Dogarai  mata, yanzu shekarunki nawa da samun wannan sarauta Ta Dogariya?
 Aisha: Yanzu shekaruna za su kai akalla goma sha biyar ina wannan aiki na dogariya.
Aminiya: Sarkin Dogarai mata wane irin aiki kuke gudanarwa a fada?
Aisha: To aikinmu ya shafi cikin gida ne, kula da kai-komo da kuma bada tsaro wajen iyalan sarki, kuma indan za a aurar da ‘ya’yan sarki to nice nake bayan amarya duk inda za a je da ni za a, ina gaban mota, mune masu kula da sha’anin baki daya, kuma ko da da namiji ne kuwa, kusan mune masu kula da duk abin da ya shafi cikin gida.
Aminiya: Yanzu kun kai kamar ku nawa mata Dogarai?
Aisha: Yanzu mu mata mun kai mu goma sha biyu, kuma dukkanmu Dogarai ne.
Aminiya: Ko ke ma ana yi miki jinjina kamar yadda ake yi wa masu sarauta?
Aisha: kwarai kuwa, domin su ‘yan uwana mata Dogarai  suna zuwa har inda nake, wato dakina suna gaishe ni, suna yi mun jinjina kuma suna ba ni girmana a matsayin sarkin dogaransu.
Aminiya: Sarkin Dogarai Aisha ko kina sanya kayan Dogarai?
Aisha: kwarai kuwa ina sanya kayan Dogarai,  har ma ina rataya jamjami, watau wani maratayi ne wanda sarauniyar kyau ke ratayawa, shi ne kamar matsayin rawani, kuma shi jamjami yana da kwar-jini, watau yana kara darajar mutum, ai ka  ga rawani shine cikar sarauta, kuma yana kara darajar mai sarauta, ko a ina ne kuwa.
Aminiya: To sarkin Dogarai mata ko kina hawa doki?
Aisha: (ta yi dariya): Ai na tsufa, amma da ina da sauran karfi babu abin da zai hana in hau doki ni ma.
Aminiya: Yanzu shekarunki za su kai nawa?
Aisha: Yanzu shekaruna za su kai 66 da haihuwa.
Aminiya: To yaya iyali fa?
 Aisha: Ina da miji, shi ma yana da sarauta, domin shi ne Madakin kakakin Sarkin busa, yana busa kakaki ne, ina da iyali.
Aminiya: To Dogariya, daga karshe mai za ki fada wanda ban tambaye ki ba?
Aisha: To ni abin da zan fada shi ne ina yi wa Mai martaba Sarkin Zazzau fatan Allah Ya kara masa lafiya, Ya ja zamaninsa, Ya kuma yi masa  sakaiya da aljannarSa Amin, domin duk abin da ake yi wa dan adam sarkin ya yi mun, kuma ba ni da wata matsala yanzu illa fatan mu cika da imani, Allah Ya saka wa Mai martaba da alheri amin.

….Aikinta yana kyau   -Sarkin Dogaran Zazzau

Aminiya: Ko za ka fada mana sunanka da matsayinka a fadar Zazzau?
Sarkin dogarai: Assalamu Alaikun, sunana Suleman Idris Sarkin Dogaran Zazzau.
Aminiya: Ranka ya dade Sarkin Dogarai, me ne ne aikin dogari a fada?
Sarkin Dogarai: Aikin dogari dai aiki ne na tsaro da kula da lafiyar sarki da kuma duk abin da sarki ya mallaka, kuma muna tare da sarki a duk inda yake gida da waje, kuma wannan sarauta ni ma na gada ne a wajen mahaifina, domin mahaifina shi ne Sarkin Dogaran Zazzau kafin rasuwarsa, bayan ya rasu sai Mai martaba sarki ya nada ni na gaji mahaifina.
Aminiya: Kana da dogarai kamar nawa da suke karkashinka a yanzu?
Sarkin Dogarai: Ina da Dogarai kamar guda 270 yanzu haka a karkashina,
Aminiya: To ranka ya dade na ga dogariya mace, dama akwai dogarai mata ne?
Sarkin Dogarai: Akwai dogarai  mata wanda ake sanya su aikin gida wajen matan sarki, domin mu maza ba muna shiga gida ne ba. To sai a dauki dogarai mata masu kula da kai komo na gida da kuma kula da lafiyar duk wanda yake cikin gidan, idan sun ga abin zai fi karfinsu sai su yi maza su sanar da mu domin mu dauki mataki. Kuma su ke kula da kai komo da aike-aike  da duk wani sha’ani da ya shafi cikin gida. Muna da mata dogarai kamar goma sha biyu, kuma akwai Sarkin D                                                                                                                                            ogarai mace mai suna Aisha, wato ita ce sarkinsu, kuma kowane dakin matan sarki akwai dogariya mai kula da ita, ita wannan Aishan ita ce sarkin Dogarai mata amma tana karkashina ne, kuma ina yabawa da aikinta, domin babu wata matsala da ake samu, aikinsu yana yin kyau kwarai, ina yaba musu domin jaruntakarsu.
Aminiya: Daga karshe, ko kana da sako?
Sarkin Dogarai: Ina da sako, ina rokon duk wani wanda yake zaman fada ya san cewa fada wuri ne na baki, kuma wuri ne wanda yake bukatar natsuwa da kuma girmama manya da kula da baki da kyautatawa, kuma ina yi wa Mai martaba Sarki fatan Allah Ya kara masa lafiya, Ya kuma ja kwanansa, amin.