Yadda na zama shugaban sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka- Leo Keyen
Mista Leo Keyen shi ne shugaban sashen Hausa na gidan Rediyon Muryar Amurka da ke birnin Washinton DC. Ya bayyana yadda ya zama shugaban sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka da kuma bambancin aikin jarida a Amurka da kuma Najeriya. Aminiya: Shin wane ne Leo Keyen?Leo: Sunana Leo Keyen, an haife ni a Jihar […]
Mista Leo Keyen shi ne shugaban sashen Hausa na gidan Rediyon Muryar Amurka da ke birnin Washinton DC. Ya bayyana yadda ya zama shugaban sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka da kuma bambancin aikin jarida a Amurka da kuma Najeriya.
Aminiya: Shin wane ne Leo Keyen?
Leo: Sunana Leo Keyen, an haife ni a Jihar Filato da ke Arewacin Najeriya kimanin shekara 59 da ta gabata. Na kammala makarantar firamare ta Yalwan Shendam a Jihar Filato a shekarar 1969, na kuma kammala sakandare ta Kuru (GSS KURU) a 1974, daga nan na wuce Jami’ar Bayero ta Kano mai reshe a Zaria, nan kuma na kare ne a shekarar 1979, sannan na yi hidimar kasa ta shekara 1.
Aminiya: Yaushe ka fara aikin jarida?
Leo: A lokacin da na yi digiri ba a fara kwas din koyar da aikin jarida ba, na yi digiri ne a kan harshen Faransanci da kuma Tarihi, bayan na kammala yi wa kasa hidima sai na fara aiki a gidan talabijin na Najeriya (NTA Jos). Ina wannan aikin ne aka kawo mu birnin New York da ke Amurka don mu koyi aikin jaridar na tsawon shekara guda, wanda ya kunshi aikin rediyo da na talabijin. Bayan mun kammala sai muka bude PRTb.
Aminiya: Mene ne PRTb?
Leo: PRTb na nufin Plateau Radio Telebision, wato gidan rediyo da talabijin mallakar Jihar Filato.
Aminiya: To a wane mataki kuka fara aikin ganin ku ne kuka bude wannan gidan rediyo?
Leo: Na fara ne a matsayin mai nemo labarai da rubutawa, daga nan na zama Shugaban sashen harkokin yau da kullum (News and Current Affairs), sannan na zama Babban Edita, to ina rike da mukamin ne aka fada siyasa sosai, wato a shekarar 1991, bayan mulkin Janar Babangida ke nan.
Aminiya: To tun da ka dawo karatu a New York shin akwai wani aiki da ka yi baya ga aikin jarida?
Leo: A’a, amma ka san aikin jarida idan har ya shige ka, to ba ka iya barin sa, bayan mun yi siyasa daga baya aka zo aka nada ni Shugaban gidan rediyon na PRTb. Ina rike da wannan mukamin na shugaban gidan Rediyon ne sai gwamnatin Marigayi Janar Sani Abaca ta karbe mulki, sai aka dakatar da mu, sai na koma na kafa gidan jarida mai suna ‘DETAILS’ a karkashin kamfanin MEDIA WAbE PRODUCTION, wannan kamfanin ya yi suna sosai a Jihar Filato a wancan lokacin. Muna cikin buga wannan jaridar sai muka koma samar da labarai ga gidajen rediyo da talabijin har da hotuna da na bidiyo, muna sayar wa wadannan gidajen yada labarai da ke cikin Jihar Filato.
Aminiya: Shekara nawa ka yi kana tafiyar da wannan kamfanin samar da labarai mai zaman kansa?
Leo: Shekara biyar na yi cur ina aikin dan jarida mai zaman kansa.
Aminiya: Shin wannan kamfanin mai zaman kansa naka ne kai kadai ko kuwa na hadin gwiwa ne?
Leo: Na samar da kamfanin ne ni kadai, amma na janyo wadansu ’yan uwana muke tafiyar da shi, sai muka yi rashin sa’a kamfanin bai yi tsawon rai ba, domin babu wanda zai tallafa mana, ba kamar kudancin Najeriya ba ne, domin mu nan ba ma samun tallace-tallace, abin da ya kawo durkushewar kamfanin ke nan. Mun kasa biyan kudin sauran mutanen da ke yi mana aiki.
Aminiya: Ita wannan jaridar iyakacinta cikin Jihar Filato ce kawai?
Leo: Ai mujalla ce, kuma ba kullum muke buga ta ba, kuma ka san harkar jarida abu ne da ke bukatar kudi masu yawa kafin ta mike.
Aminiya: To da yake ka yi aikin jaridar gwamnati, kuma ka yi na mai zaman kansa yau kai ne shugaban sashen Hausa na gidan rediyon muryar Amurka, shin wane lokaci aka faro wannan tafiya na shugabancin wannan sashen?
Leo: To bari in ba ka dan takaitaccen tarihi, a lokacin da na zo karatu a New York, ka san a nan Amurka ba za ka kammala aikin jarida ba sai an kai ka wata kafar yada labarai ka koyi ainihin aikin jarida, ka gane wa idanunka har ma ka bada taka gudunmuwar wajen gudanar da aikin, to ni da aka tashi turo ni irin koyon wannan aikin sai aka kai ni gidan wani rediyo mai suna W.A.J CHANNEL 7, yau ana kiransa Discobery Channel, a wannan wurin ne na kara samun sha’awar in sake dawowa Amurka domin in yi aikin jarida a Amurka, kai har lokacin da nake shugaban gidan rediyon Jihar Filato kullum ina tunanin yaya za a yi in sake dawowa Amurka domin in yi wannan aikin, ina nan Najeriya sai na samu labarin cewa wannan kujerar shugabancin sashen Hausa na wannan gidan rediyon babu kowa a kanta, kuma ana nema, sai na aiko da takardar nema, aka gayyace ni in zo , aka gwada ni aka kuma ce na cancanta, sai aka dauke ni, to ka ji yadda har na zo nan.
Aminiya: Kana nufin ba ka san kowa ba haka kawai daga gwada ka ne suka dauke ka?
Leo: Na san kowa mana, wato aikin jarida shi ne kowana, nan babu ruwansu da irin yadda ake yi a Najeriya, idan ka yi sai ka nuna musu ba ta da kumbuya-kumbuya, idan kuma ba ka iya ba duk za su gani, to idan ka san wadannan, to su ne mutanen da za su sa su ba ka aiki, amma ba wani mutum ba.
Aminiya: To ka yi shugabanci a gidan rediyo a Najeriya, yau kana yi a nan Amurka, wane bambanci za ka ce akwai na shugabanci kafin mu je ga shi kansa aikin?
Leo: Akwai bambanci sosai, na daya, ina son ka gane cewa duk wanda ka ga yana aiki a nan, to kwararre ne, don haka shugabantar kwararre da mai koyo ka san akwai bambanci, domin da kyar ake koyon aiki, ina nufin ba za ka zo nan ka ce a nan ne za ka koyi aikin ba, duk wanda ka ga an kawo to ka tabbata ya kware , sabanin irin namu na gida, idan ka zo ba ka san wannan aikin ba, to za ka sha bani, domin kuwa nan ba makaranta ba ne, kowa ka gani ya goge, don haka kai ma sai ka duba ka gani, domin ka san nan ba karamin gidan rediyo ba ne, da duniya kake magana, don haka tilas ma’aikata su kasance kwararru, to ashe ka ga shugabanci a irin wannan yanayi ya sha bamban da na wanda ka sani a gida Najeriya. Nan gidan nuna gwaninta ne, wani abu kuma ba ya ga iya aikin zunzurutunsa, akwai bukatar kwarewa a kwamfuta, idan wai don kana ganin ka iya aikin rediyo, amma ba ka iya sarrafa kwamfuta ba, to kana da sauran aiki, saboda haka dole ka hada biyu, domin babu mai lokacin koya maka, to abu na uku kuma shi ne, idan kana aiki nan kana da kariyar cin zarafi, ba kamar gida Najeriya ba, inda wani zai ce don me ka bari aka yi amfani da labari kaza alhali ka san ya shafi gwamnati, nan kuwa ko Shugaba Obama ya yi ba daidai ba sashen Hausa na da damar yada wannan labarin, akwai abin da ake kira da Turanci JOURNALISTIC WORLD, wato kariya daga cin zarafi daga wani ma’aikacin gwamnati ko dan kasuwa muddin labarinka na da tushe.
Aminiya: To na lura nan kai da ma’aikatan Sashen Hausa ba ku yi kama da ubangida da yaransa ba, domin sau tari sai in ga ka fita ofishinka kana ziyartar ma’aikata maimakon su rika zuwa ofishinka suna cewa ranka ya dade, shin yaya shugabancin yake nan da wanda ka yi a gida Najeriya?
Leo:Kai gida ai ba shugabanci ake yi ba, izza da nuna isa ake yi, ko kuma tsorata ma’aikaci, wannan ba ya kawo ci gaba, wannan aikin da muke yi nan na kwakwalwa da basira ne, don haka idan mai gidanka ya lallabe ka sai ya amfana da basirarka sosai, domin sai kana da kwanciyar hankali ne za ka iya bada gudunmuwarka a aikin.
Aminiya: Wacce shawara za ka bayar domin aikin jarida ya inganta a Najeriya?
Leo: Kai Ladan kada in bata maka lokaci ni ma in bata nawa, batu na gaskiya shi ne sai ire-irenmu da muka zo nan muka yi wannan aikin mun koma gida, mun bude irin kafafen yada labarai, domin mu mutunta wannan aikin, mu karrama shi, har wadansu su gani daga gare mu su koya, amma idan ba haka ba ni dai ban san wata hanya ba, domin muddin gwamnati na da muhimmiyar rawar takawa cikin wannan aikin, to gyaran sa sai ikon Allah.
Aminiya: Yaya batun bada dan abin ihsani nan wanda a Najeriya ake kira ‘Brown enbelope’ a Amurka?
Leo: Yaya za ka yi shi a nan, bari in ba ka wani labara, akwai wani Minista a Najeriya da ya zo nan gidan rediyo, bayan mun gama hira da shi muna yi masa rakiya, sai ya fito da kudi ya ba mu, muka tambaye shi na mene ne? Sai ya ce ya ba mu ne, muka ce masa, ai nan ba a karba, mun gode. Idan mutum ba mai hadama da zalama ba ne, ba ka bukatar wani ya zo nan ya ba ka sisin kwabo, domin an duba irin aikin da za ka yi, kuma an dubi matsalolinka bakin gwargwado, duk an san matsalolinka cikin albashinka har ka samu ragowar da za ka ajiye wani abu. Hanyoyi suna da kyawu, ga wuta, ga ruwa, abinci arha ba ka bukatar komai da za ka ce albashinka ba zai iya yi maka ba.
Aminiya: To amma ka san a Najeriya kafofin yada labarai da yawa ba sa biyan ma’aikatansu a irin wannan yanayi, yaya kake son mutum ya yi ke nan?
Leo: To kuma maganarka gaskiya ce, idan bera na da sata, to daddawa ma na da wari, sau tari sai ka ga cewa dan jarida cuku-cuku babu abin da iya yi wa kansa, to amma domin ba ka da aiki sai ka ce bari ka koma sana’ar sata? ai doka ba za ta kyale ba.
Aminiya: To ina mafita ke nan?
Leo: To batu na farko shi ne, ’yan jarida su rika neman ilimi, kada su gaji da neman ilmin aikin jarida, musamman abin da ya shafi kwamfuta, domin duniya canzawa take yi, idan ba ka kware a kanta ba, to wallahi wata rana sai a yi ba da su ba.
Aminiya: Batun iyali fa?
Leo: ’Ya’yana biyar. Biyu ne suke makaranta sauran sun kammala, akwai daya da za ta zo nan Amurka ta yi digiri na biyu a kan abin da ya shafi aikin jarida, sai dan autansu na ga ya matsa da daukar kyamarar daukar hoton bidiyo, ko shi ma aikin jaridar zai yi ban sani ba, idan abin da yake so ke nan sai in ce Allah Ya ba shi sa’a.