‘Yadda na zama ’Yar Saudiyya ta farko mai daukar hoton wasanni’

Manal Al-Dabbagh, ita ce macen farko a kasar Saudiyya da ta fara daukar hoton wasanni. Wannan uwargida mai daukar hoto, tana da ’ya’ya biyar; maza biyu, mata uku. Ta yi aure tun tana ’yar shekara 16.A cewarta, yanzu ina aiki a matsayin shugabar sashen daukar hoto a jaridar Al-Watan da ke kasar katar. “Na kasance […]

‘Yadda na zama ’Yar Saudiyya ta farko mai daukar hoton wasanni’

Manal al-Dabbagh a bakin aikintaManal Al-Dabbagh, ita ce macen farko a kasar Saudiyya da ta fara daukar hoton wasanni. Wannan uwargida mai daukar hoto, tana da ’ya’ya biyar; maza biyu, mata uku. Ta yi aure tun tana ’yar shekara 16.
A cewarta, yanzu ina aiki a matsayin shugabar sashen daukar hoto a jaridar Al-Watan da ke kasar katar. “Na kasance mai kokarin aiki, gwargwadon iyawata. Kusan kodayaushe na kan yi kokarin ganin hoton da na dauka ya fassara wa mai kallonsa labarin abin da yake dauke da shi,” injita.
A cewarta, na samu kwarewa a aikina, bayan da na kara kokari wajen karance-karance kan yadda na’urar daukar hoto ta kyamara ke aiki. Na kuma halarci kwasa-kwasai a kan fannin daukar hoto.
Manala ta bayyana wa jaridar Arabnews, yadda ta fito neman aiki mai buga keken rubutu, amma daga bisani ta yi aikace-aikace da dama, wadanda suka hada da tallata haja, inda a karshe ta samu aikin daukar hoto, wanda har a yau take farin ciki da shi.
Saboda da karbuwar da ta samu a duniyar asanni kasashen Larabawa, an karramata da lambar yabo ta  “Muftaha,” a shekarar 2010.