Yadda na zama zakaran kokuwa na duniya – Sale Mamman Zariyaa
Aminiya: Mene ne tarihinka?An haife ni ranar 20 ga watan Disambar 1947 a Tudun Wada Zariya, yanzu shekaruna 69. Na yi karatun firamare a Tudun wada da Sabon Gari da kuma Bosso. Na yi Sakandare a Abuja (Suleja) da ke Jihar Nija, don yayana yana aikin dansanda kuma ana yi masa sauyin wurin aikin. ‘Yan […]
Aminiya: Mene ne tarihinka?
An haife ni ranar 20 ga watan Disambar 1947 a Tudun Wada Zariya, yanzu shekaruna 69. Na yi karatun firamare a Tudun wada da Sabon Gari da kuma Bosso. Na yi Sakandare a Abuja (Suleja) da ke Jihar Nija, don yayana yana aikin dansanda kuma ana yi masa sauyin wurin aikin. ‘Yan ajinmu a Zariya sun hada da Mai Shari’a Usman Kusherki da Maikudi da Muhammadu Alhaji Tulu Tudun-Wada da Ibrahim da sauransu.
Aminiya:Yaya aka yi daga kurtu ka zama hafsa?
Na shiga aikin soja a shekarar 1963 a matsayin kurtu mai ilimi, bayan an korkiro makarantar horar da kananan hafsosin soja (NDA) sai aka kai mu na samu horo na zama hafsa a shekarar 1968. Abokan aikin sojana sun hada da Iya Mashal Idi Musa da Mashal Nsikak Uduok da Emmanuel Edem da Janar Idris Garba da Olagunsoye Oyinlola da Kanar Mike Ture da Win Kwamanda Dan Ekele -Martin Lurther, wanda aka kashe a juyin mulkin da Janar Mamman batsa ya jagoranta da Emmanuel Mbu da Janar Ojo Kojo da Janar Musa Abba, mutumin Kagoro da sauransu. Na yi aiki a runduna ta daya da ke Kaduna a karkashin Janar Muhammadu Shuwa da runduna ta biyu a karkashin Janar Murtala Muhammad a Ikeja da kuma runduna ta uku ta Kwamando a karkashin Benjamin Adekunle, wanda aka fi sani da suna ‘Black Scorpion,’ watau “Bakar Kunama.” Lokacin da nake kurtu, ina bangaren aikin asibiti ne, da yakin basasa ya barke, sai na zama dakare mai yaki da bindiga (infantiri), sannan na zama mai yaki dan leken asirin makiya da sharar fage (RECCE) da kuma na masu motar yaki mai sulke (Amo). Da aka kawo sabbin manyan bindigogin yaki kamar Panhart mai lamba 60 da kuma mai lamba 90 daga Faransa, sai Janar Adekunle ya kwashe mu ba tare da an yi takarda ba, domin a aikin soja kuma a lokacin yaki ba a sanyin jiki, sai kazar-kazar, oda kawai ake bayar wa, sai mu na kasa mu ce “Yas Sa,” watau mun yarda, ba ka isa ka yi musu ko ka yi tambaya ba, kamar yadda ake yi a aikin ofis irin na farar hula ba. Sojan sama kuma suna da jiragen yaki samfurin F27 da F28. An dauke mu a jirgi zuwa Fatakwal, daga nan muka yi wa Owerri tsinke. Mu ne sojan da ‘Yan tawaye suka yi wa kofar-rago a Owerri, harbin bindiga babu kakkautawa ya sa muka waste, don ba mu samu karin kayan yakin ba, watau harsasai da sauransu. Mun sha wuya matuka. Mun yi amfani da dabarar yaki daga Owerri a kasa zuwa titin Elele zuwa Shokosho zuwa Oromo-Kuta, sai Oro-Mashi, sai Eleme, sannan muka hadu a dandalin Bori. Duk mai son yaki bai san shi ba ne, yana gani ne kawai a talabijin. Mun yi yakin ne domin Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya.
Aminiya: Yaya aka kare yakin basasan?
An yi shekara uku ana fafatawa kafin aka ci Ojukwu da yaki. Yaki ne na kai hari da matsawa gaba a kasa don babu mota. Mun yi tafiya a kasa a daji babu hutu ba zuwa ganin gida har na tsawon shekara uku.
Aminiya: Me ya sa Janar Murtala ya kara maka girma a fagen yaki?
Jin dadin ina kurtu mai ilimi, aka kai ni makarantar NDA aka ba ni anini, shi ya sa na sadaukar da kaina na yi yaki, haka ya sa Janar Murtala ya kara min girma zuwa mai anini uku, watau kaftin
Aminiya;Me ya sa soja suka ki barinka ka yi murabus da wuri?
Dokar soja ta hana hafsa ya yi mu’ammmala da kurata. Kuma ba hafsoshin da za su iya kokuwa da ni. Haka ya sa na rubata zan bar aiki tun lokacin da Janar Dabid Ejoor ya ke hafsan hafsosi, amma ba a sa hannu ba sai zamanin Janar Hassan Usman Katsina. Don ina matukar son yin kokuwa da burin zama zakara, shi ya sa na yi murabus. Ni mutum ne mai son kazar-kazar, shi ya sa na ga tun da an gama yaki an dawo ofis, sai na ce gara in shiga kokuwar zamani ko zan zama zakara.
Aminiya: Yaya aka yi ka zama zakaran kokuwar duniya?
Na fara kokuwa ne irin na zamani na turawa inda na yi kokuwa da yawa kafin na fara na kwararru. Na yi kokuwa da Tiger Epmos da Pedro Douglas na kasar of Turkiya, wanda na buge shi a filin wasan Ogbe da ke Benin. Na buge Napoliyon na kasar Iran a turmi na biyu lokacin Birgediya Abba Kyari yana Gwamnan Kaduna a filin wasa na Ahmadu Bello. Don masu kallo su more kudinsu, sai in yi ta yin taka-juye har kokuwar ta yi tsawo, domin na lura inda na buge mutum a turmi na farko ‘yan kallo ba sa so. Daga nan sai na koma kasar Amurka, inda na kara a Chicago da Jack Miller Norris, wanda yaya ne ga tauraron yin fim din nan mai suna Chuck Norris. Na ci wasan a turmi na bakwai, inda aka ba ni kambun zakaran kokuwar duniya. Na yi kokuwar ne don cika buri, ba don kudi ba. Domin lokacin Naira ta fi Dala daraja, don ana sayen Dala daya ne a kan Kobo Saba’in da biyar, ita kuma fam ta Ingila tana daidai da Naira daya da Kobo ashirin. Sannan kudin zuwa Makka shi ne Fam dari. Ban taba samun rauni ba, kuma lokacinmu ba a shan kwaya ko kafso.
Aminiya:Me ya sa ka ki kare kambunka bayan ka zama zakaran kokuwa na duniya?
Bukatata ita ce in zama zakaran kokuwar duniya, kuma Allah Ya cika min burina. Don na ki yarda kwadayi da burin duniya ya rude ni. Da na bar Amurka na dawo Najeriya, sai na kira taron ‘yan jarida na ce ba zan kara yin kokuwa ba. Wannan ya sa manajana a Amurka bai so ba, domin shi zai rika samun kudi da ni idan da na ci gaba da kokuwa, don zai ce ya yayata karon da nake yi da sauransu, ya kwace kudi ya ba ni dan la’adar da ya so, watau Kura da shan bugu, Gardi da kwashe kudi. Sai mutane suka rika tsokalata suna cewa tsoro ya sa na yi murabus daga kokuwa. Ni ba mai son burge kowa ba ne, don haka ban kula da su ba. Bayan na huta sai na koma Landan na yi karatu har zuwa matakin digiri na biyu, watau Masta, a jami’ar Manchester.
Aminiya:Yaya aka yi ka fara aiki da gwamnatin jihar Kaduna?
Na yi aiki da marigayi Alhaji Samaila, Dallatun Zazzau da Alhaji Umaru Idris, dan-Galadiman Zazzau da Mista Waje Yayock da Alhaji Abubakar Mustapha, wanda ya sauya ni daga bangaren wasanni zuwa na gudanarwa, bayan na ci jarrabawa iri-iri. Na yi aiki a gidan gwamnati a matsayin mataimakin daraktan tsaro a karkashin gwamnonin soja, Kanar dangiwa Umar da Sarki Muhktar da Lawal Jafar Isa da kuma ‘yan siyasa, Ahmed Makarfi, sannan na yi ritaya a zamanin Gwamna Namadi Sambo. Na gode Allah.
Aminiya: Yaya huldarku take da yaranka a soja da suka zama manyanka a matsayin gwamnonin soja?
Sun san ni soja ne kuma babbansu, amma ina ba su girmansu na gwamnoni kuma manyana, don ina aiki a karkashinsu a ofishin Gwamna, kuma ko dan cikina ya samu daukaka zan ba shi girmansa.
Aminiya: A matsayinka na wanda ya yi yakin basasa, wane kira za ka yi ga masu neman ta da zaune tsaye kamar ‘ya’yan kungiyoyin OPC da Boko Haram da MASSOB da MENDS da NDA da sauransu?
Lallai ne Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya cikin lumana, kuma gwamnati ta samar da sana’o’i ko aiki ga matasa, domin fatara tana sa a yi saurin sauya tunanin matasa daga masu bin doka zuwa ‘yan taratsi.
Aminiya:Me ya sa kungiyar kokuwa ta Najeriya ta mai da kai saniyar-ware?
Bayan da Kanar Abdulmumini Aminu ya sanya ni cikin kungiyar, sai Bolaji Oni da Grup Kaftin Jonah Jang da Mike Bamidele da Bernard Okoye (Lion Heart) suka yi watsi da ni don ina fadin gaskiya.
Aminiya:Me ya sa ba ka sa kaftin murabus a sunanka sai da Alhaji?
(Dariya) Idan mun je taron tsofaffin soja ana ba mutum wurin zama ne daidai da girman mukaminsa lokacin da ya yi murabus. Watau layin kujerun janar na gaba, sannan na kanar, sai na Manjo, sai da kaftin zuwa kasa. Tunda abokaina sun zama Janar, sai in je in zauna a cikinsu da sunan Alhaji, in bar yara da jikokina masu mukamin kaftin a baya (dariya). Na bar soja tun shekarar 1974. Na kuma yi murabus daga aikin gwmantin jihar Kaduna a matsayin babban sakataren hukumar rage radadin talauci a shekarar 2008, sannan na yi aiki na Naira biliyan daya da miliyan dari biyu, da aikin yau da kullum na Naira miliyan dari biyu da hamsin, na karbo bashin kudi daga masu taurin bashi na Naira miliyan 181 na kuma bar tsabar kudi Naira miliyan dari biyu da hamsin. Na dogara da albashi da alawus dina, don ina tsoron haduwata da Allah. Wannan ya sa aka rike ni a matsayin mai aikin kwangila bayan na yi murabus. Rashin yarda da cin hanci da rub-da-ciki ya sa ake kirana “Bin diddigi.” Har yanzu ina da hakorana cif-cif, idanuna suna gani tangaras kuma ba ni da ciwon hawan jini ko ciwon suga. Na gode Allah.
Aminiya: Yanzu me kake yi tunda ka yi murabus?
A da ina yin kwallon Tebur da iwo , amma yanzu na fi son yin tafiya a kasa don motsa jiki. Sannan ban matsa wa yarana da sai sun yi kokuwa ba.