Yadda na zamanantar da harkar sayar da shayi – Shugaban masu shayi

Shugaban kungiyar masu shayi ta kasa Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana cewa ya bude wurin sayar da shayi irin na zamani ne, don dada inganta wannan sana’a. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen walimar bude wajen sayar da shayi irin na zamani da ya yi a garin Jos. Ya […]

Yadda na zamanantar da harkar sayar da shayi – Shugaban masu shayi

Shugaban kungiyar masu shayi ta kasa Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana cewa ya bude wurin sayar da shayi irin na zamani ne, don dada inganta wannan sana’a. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen walimar bude wajen sayar da shayi irin na zamani da ya yi a garin Jos.

Ya ce mun bude wannan wajen  sayar da shayi irin na zamani ne, domin wurin shayi wurin cin abinci ne da ya kamata a inganta shi fiye da kowanne irin wurin sana’a. Kuma wuri ne na kiwon lafiya. 

Ya ce mun kawata wannan waje mun sanya masa dukkan abin da ya kamata mu sanya, mun yi kamar yadda ake wuraren sayar da shayi a kasar Saudiya da sauran manyan kasashen duniya. 

Ya yi  kira ga masu shayi na Najeriya, su bude irin wadannan  wuraren sayar da shayi irin na zamani, domin inganta wannan sana’a tare  da  kwantar wa da abokan huldarsu hankali. 

Shi ma a nasa jawabin babban jami’in ‘yan sanda na shiyar Unguwar Rogo da ke garin Jos  Mansur Ahmed  ya nuna jin dadinsa da bude wannan waje. Ya ce  babu shakka an yi kokari wajen gyara wannan waje. Ya yi   fatan sauran masu sana’ar shayi za su yi koyi da wannan abu. 

Daga nan ya yi kira ga   masu wannan sana’a su bai wa jami’an ‘yan sanda  hadin kai da goyan baya,  ta hanyar ba su labaran masu aikata miyagun abubuwa. Ya ce Irin wadannan labarai za su taimaka masu wajen gudanar da ayyukansu.

 

Manyan mutane da sauran kungiyoyi da dama ne suka halarci wajen wannan walima ta bude wannan waje na sayar da shayi irin na zamani a garin na Jos.