Yadda nada Sheriff ya nemi share PDP
A ranar Litinin din makon jiya ne wasu bangarori na masu fadi-a-ji na Jam’iyyar PDP ta kasa suka zaba tare da nada tsohon Gwaman Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar ta kasa. Nadin da ya nemi share PDP daga fagen siyasar kasar nan, sakamakon yadda ’ya’yan jam’iyyar suka yi mata […]


A ranar Litinin din makon jiya ne wasu bangarori na masu fadi-a-ji na Jam’iyyar PDP ta kasa suka zaba tare da nada tsohon Gwaman Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar ta kasa. Nadin da ya nemi share PDP daga fagen siyasar kasar nan, sakamakon yadda ’ya’yan jam’iyyar suka yi mata ca kan wannan nadi.
Kakakin Jam’iyyar ta kasa Olisa Metuh ne ya shaida wa duniya nadin a lokacin da yake bayani ga manema labarai a cibiyar ’yan jarida ta PDP jim kadan da nadin. Ya ce bayan cikakken nazari kan dukkan mutanen da suka nuna sha’awar hayewa kan kujerar shugabancin da kuma ayyuka mabambanta da manyan sassan jam’iyyar wato kungiyar gwamnoninta da Kwamitin Dattawa da Babban Kwamitin Gudanawa da manyan masu fada-a-ji na kasa, tsohon Gwamnan Jihar Borno aka zaba ya haye kan kujerar mai muhimmanci. Sai dai bai fadi matsayin Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar (NEC) ba.
Kakakin na PDP ya ce, bukatar da dan siyasar nan na Jihar Adamawa kuma tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu ya gabatar ta a a cire sunansa daga cikin masu neman mukamin, ta taimaka wajen yanke shawarar nada Sheriff.
Metuh ya ce Ribadu ya bukaci a cire sunansa bisa dalilai na kashin kansa.
Sauran wadanda suka halarci tantancewa don neman mukamin sun hada da Sanata Sa’idu Umar Kumo Garkuwan Gombe (Gombe) da tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa shiyyar Arewa maso Gabas Mista Wilberforce Juta (Adamawa) da Alhaji Lawal Grigiri (Yobe) da Alhaji Mohammed Wakili (Borno) da Alhaji Shehu Gabam (Bauchi), yayin da babu wanda ya nuna sha’awa daga Jihar Taraba.
Sai dai kuma ana bayyana nada Sanata Ali Modu Sheriff, sai barakar da ke cikin jam’iyyar ta fara ta’azzara, inda mambobin jam’iyyar da shugabannin siyasa suka rika barazanar za su fice daga cikinta.
Fayose da Wike ne kanwa uwar gami:
Ana zargin Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose da Gwamnan Jihar Ribas Nyosen Wike da shiga da fita don ganin an nada Sheriff a matsayin shugaban jam’iyyar, wanda masu adawa da nadin suka ce ba ya cikin mutanen da jihohin Arewa maso Gabas suka mika sunayensu don karasa wa’adin tsohon shugaban jam’iyyar Ahmadu Mu’azu wanda ya yi murabus jim kadan da faduwarta a zaben bara.
Alamun hannu Gwamna Fayose a wannan nadi sun bayyana a cikin wata sanarwar da kakakinsa Lere Olayinka ya fitar yana yaba zaben Sheriff a mukamin tare da kiran ’ya’yan jam’iyyar su goya masa baya.
Fayose ya ce zaben Mosu Sheriff an yi shi ne domin shi ne mafi a’ala ga jam’iyyar. “A koyaushe ina kare jam’iyya koda zan rasa mukamina da lafiyata da jin dadina. Koyaushe ina tsaye kan gaskiya kuma ba zan kasance cikin duk wata shawara da ba za ta amfani jam’iyya yadda ta kamata ba. Na goyi bayan hanyar da aka bi aka zabi Ali Modu Sheriff, saboda na yarda da shi, kuma wadanda suka fusata saboda wasu dalilai ina rokonsu su mayar da wukakensu don amfanin jam’iyyarmu,” inji shi.
Gwamna Fayose ya ce, “Jam’iyyar APC ta san wane ne Sanata Ali Modu Sheriff a fagen sanin siyasa, kasancewarsa sanata har sau uku sannan Gwamna sau biyu, za ta ji tsoron cewa samun irin wannan mutum a matsayin shugaban PDP, mulkinta ya yi kusan zuwa karshe.”
Kwamitin Dattawa bai yarda ba:
Wakilan Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP take suka ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan zuwa watan gobe ya ki amincewa da Sherifff a matsayin Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar ta kasa. Wakilan kwamitin da wasu sanatoci da suka fusata sun yi barazana ga tsohon Shugaban kasar cewa idan ya ki watsi da Sheriff to ya shirya wa ficewar jama’a kungiya-kungiya daga jam’iyyar.
Ministocin Jonathan sun botsare:
Sannan washegari Talata tsofaffin ministocin da suka yi aiki a karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan sun yi taro a Asokoro inda suka sha alwashin barin jam’iyyar matukar ba a cire Modu Sheriff daga sabon mukamin nasa ba.
A cewar tsofaffin ministocin, tsohon Gwamna na Jihar Borno ba zai iya jagorantar jam’iyyar ta kwato mulki daga APC ba. “A lokuta da dama an rika jingina shi da batun Boko Haram, duk da cewa har yanzu ba kotun da ta kama shi da laifi. Amma ana yawan zarginsa da hakan. Kuma ba za mu iya kare wannan zargi ba a yanzu, ba mu da wannan lokaci,” inji daya daga cikin tsofaffin ministocin na Jonathan.
Su ma sanatocin PDP da suka fito daga Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu sun yi fatali da zaben na Sheriff.
Kwatsam sai wata kungiya mai suna kungiyar Ceto PDP a karkashin su Wilberforce Juta ta kira taron manema labarai inda ta bukaci a yi watsi da zaben Modu Sheriff tare da kiran sabon shugaban ya yi murabus daga kan kujerar.
Sai dai kuma Modu Sheriff ya nace cewa ba zai sauka daga kujerar ba, kamarb yadda wasu ’ya’yan jam’iyyar ke nema, ya ce masu adawa da kasancewarsa shugaban jam’iyyar suna yi ne saboda tsoron yadda tauraruwarsa take haskakawa a fagen siyasa. Ali Modu Sheriff ya ce shi ne kashin bayan kafuwa da karbuwar Jam’iyyar APC, kuma zai yi amfani da wannan dama wajen sake farfado da Jam’iyyar PDP.
Fani Kayode ba zai sha ba – Sheriff
Sakamakon yadda tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama kuma jigo a Jam’iyyar PDP, Femi Fani-Kayode ya yi zargin cewa shi ya kafa kungiyar Boko Haram, Sanata Ali Modu Sheriff ya ce ba zai kyale tsohon ministan ba a wannan karo. Sheriff, ya yi wannan barazana ce a ranar Litinin da ta gabata bayan ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar.
Shugaban na PDP, ya kuma nace cewa ba ya da alaka da kungiyar, inda ya ce ’ya’yan kungiyar sun kashe danginsa. “Boko Haram sun kashe dan uwana. Sun kashe dangina. To ta yaya zan goyi bayan mutanen da suka kashe dan uwana da dangina? Ni ba mai tsaurin ra’ayi ba ne, ina son in more rayuwata… ’Yan Boko Haram masu barna ne da suke zaune a daji suke cin abinci sau daya a wuni. Ina da yakinin za a kama masu goya musu baya wata rana. Babu abin da ya hada ni da Boko Haram,” inji shi.
Game da jingina shi da kungiyar da Fani-Kayode da sauransu ke yi, ya ce: “A wannan karo mutane irin su Fani-Kayode ba za su sha ba.”
A shirye nake mu hadu da Sheriff a kotu – Fani Kayode
A martanin da Femi Fani-Kayode ya mayar ga barazanar Sanata Ali Modu Sheriff na ba zai sha ba kan jingina shi da Boko Haram, tsohon ministan ya ce abin takaici ne Sheriff da ya hau shugabancin jam’iyyar da sunan zai ciyar da ita gaba ya rika barazana ga ’ya’yan jam’iyyar.
“Ina jin ba zan lamunci wannan ba, babu wanda zai yi min barazana. Gaskiyar magana yana son kunno wutar rigima ce a Najeriya, yana son ya kunno wa PDP wuta, kuma wannan wutar za ta cinye shi, shi kadai,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Ni ba kamar mutanen da ya taba haduwa da su ba ne a baya. Zai hadu da jajircewar da bai zata ba.” Ya ce shi Fani-Kayode ya gama shiryawa su hadu da Ali Modu Sheriff a kotu.
Shugabannin PDP suna neman bakin zare:
Rikicin PDP ya ci gaba da ruruwa a ranar Talatar da ta gabata, a daidai lokacin da tsofaffin ministocin jam’iyyar da sanatoci da wakilan Kwamitin Dattawa da gwamnoni suka sake samun sabani kan wa’adin da sabon shugaban jam’iyyar Ali Modu Sheriff zai yi a kan kujerar.
Wannan ya faru ne a daidai lokacin da shugabannin jam’iyyar suka tashi-tsaye domin warware rikicin da zaben Sheriff ya jawo.
Wani zaman hadin gwiwa da suka gudanar a Masaukin Baki na Gwamnan Jihar Ondo da ke Abuja a ranar Talatar, ya amince cewa Sheriff ya shugabanci jam’iyyar na wata uku kacal inda jam’iyyar za ta kira babban taro ta zabi sabon shugaba a watan Mayu mai zuwa.
kungiyar Gwamnonin PDP ce ta kira taron wanda wasu wakilan Kwamitin Dattawa da Shugabannin Sanatocin PDP da na ’yan Majalisar Wakilai na jam’iyyar suka halarta.
Mukaddashin Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar Sanata Walid Jibrin da tsohon Shugaban Jam’iyyar ta kasa, Sanata Ahmadu Ali ne suka wakilci kwamitin a wurin taro. Yayin da Sheriff da Sakataren PDP na kasa Farfesa Wale Oladipo da Sakataren Tsare-Tsare, Abubakar Mustapha da Kakakinta, Olisah Metuh suka wakilici Babban Kwamitin Jam’iyyar (NWC). Dukkansu an ce sun yi jira na akalla awa daya kafin Sheriff ya iso wurin taron.
Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP kuma Gwamna Jihar Ondo, Dokta Olusegun Mimiko da Sanata Walid Jibrin ne suka yi magana da manema labarai bayan kammala taron.
Gwamna Mimiko, ya ce an kawo karshen takaddamar da nada Sheriff ta haifar. “Kamar yadda za ku gani, yanzu muka kammala taro. Kuna sane da takkadamar da nada sabon shugabanmu ta haifar. Kuma bisa wannan hali da aka shiga a jam’iyyarmu, ina shaida muku cewa dukkan bangarorin jam’iyya, wato Majalisar Gwamnoni da Shugabannin ’Yan majalisar dokoki da Kwamitin Dattawa sun amince mu goyi bayan shugabanmu na kasa don tabbatar da ciyar da jam’iyyamu gaba. Mun ajiye dukkan cece-ku-cen da suka faru a baya, kuma ina ba ku tabbacin mun dunkule a jam’iyya.”
Ya kara da cewa: “Mun umarci Babban Kwamitin Jam’iyya ya tsara hanyar da za ta tabbatar cikin wata uku an gudanar da babban taron jam’iyya.”
Mimiko, wanda wasu gwamnoni suka rufa masa baya, ya ce, an umarci kwamitin nan da mako biyu ya fito da jadawalin kiran tarurrukan jam’iyya da zai kai ga babban taronta na kasa.”
Shi ma da yake bayani, Sanata Walid Jibrin ya ce Kwamitin Dattawan ya amince da abin da Gwamna Mimiko ya fada. Ya ce an ba Sheriff mako biyu ya fitar da jadawlin kiran babban taron jam’iyyar da za a gudanar a watan Mayu mai zuwa. Sanata Walid Jibrin ya ce yana da tabbacin za a warware rikicin da jam’iyyar ke fuskanta nan da wata uku. “Mun gode wa Majalisar Gwamnonin kan kawo wannan dauki, kuma mu a Kwamitin Dattawa mun amince da wannan shawara,” inji shi
Sai dai ministocin Jam’iyyar PDP daga 1999 zuwa 2015 sun tsaya kai da fata cewa dole ne Sheriff ya sauka bayan da suka yi wani taro a Abuja a daidai lokacin da ake wancan taro.
Shugaban kungiyarsu, tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Alhaji Taminu Turaki (SAN) ne ya karanta wata takardar bayan taro da kimanin ministoci 40 suka halarta.
Turaki wanda shi ma wakili ne a Kwamitin Dattawan Jam’iyyar ya ce: “Wannan kungiya wadda ta kunshi tsofaffin ministocin da suka yi aiki daga 1999 zuwa 2015 ta yi zama tare da tabbatar da burinta kan tsayawa ga manufofin wadanda suka kafa PDP. “Kuma kungiyar ba ta amince da Sheriff a matsayin Shugaban PDP ba, saboda ya zama shugaba ne ta haramtacciyar hanya.” Don haka suna nan kan bakarsu ba su ji dadin ma amincewa da Kwamitin Dattawan Jam’iyyar ya yi na a bar Sanata Sheriff ya ci gaba da kasancewa shugaban jam’iyyar ba.
Tsofaffin ministocin sun nuna bacin ransu kan barazanar da Sheriff ya yi ga Fani-Kayode, inda suka ce barazana ga dayansu barazana ce ga dukkansu.
A cewarsa sun kadu kan kasancewar Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar Sanata Walid Jibrin a cikin wadanda suka amince da Sheriff, inda ministocin suka ce babu wani taro na kwamitin da aka kira domin daukar wancan mataki.
To amma sun hakura da matakin na kwamitin duk da suna da sabanin ra’ayi. Sun ce duk da cewa har yanzu akwai kafar tattaunawa da sauran bangarorin jam’iyyar, amma suna nan kan bakarsu. “Idan muka ga hujjar da za mu amince da matakin za mu amince, amma a kawo mana wasu hujjojin kan dalilin daukar matakin. Matsayinmu ya dogara ne kan hujja, wato tsarin mulkin jam’iyya da tsarin mulkin Najeriya,” inji Turaki.
Sai dai sanatocin PDP sun ki cewa komai ga manema labarai bayan taron, to amma daya daga cikinsu da ya nemi a sakaye sunansa ya ce, sun janye barazanar barin jam’iyya da suka yi daga farko.
Sanatan daga Kudu maso Gabas , ya ce sun ba Sheriff wata biyu ne kacal ya gama aikinsa ya yi gaba