Kofin Duniya: Da sauran rina a kaba duk da Najeriya ta ci Jamhuriyar Benin 4-0
Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta casa kasar Jamhuriyar Benin da ci 4-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta casa kasar Jamhuriyar Benin da ci 4-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta.
Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa. A gaba kuma, an hada Victor Osimhen da Akor Adams domin tayar da kura.
Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika masa. Cheetahs sun yi kokarin farkeaw a minti na 12, amma Calvin Bassey ya dakile harin.
- Na yafe wa Maryam Sanda —Mahaifin Bilyaminu
- Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya Abdullahi
A minti na 22, Osimhen ya kusa kara ci, amma dan wasan baya na Benin ya hana shi. Sai dai a minti na 38, Chukwueze ya sake aika masa da wata kwallo, kuma Osimhen bai yi wata-wata ba — ya zura ta biyu! Najeriya 2, Benin 0.
Bayan hutun rabin lokaci, Benin sun fara da matsa lamba, amma Osimhen ya sake daukar hankalin duniya — inda a minti na 51, ya cika hat-trick dinsa! Kwallo ta uku ke nan a hannunsa.
Super Eagles sun ci gaba da matsa lamba, inda suka nemi ci na hudu a minti na 68, amma Ndidi ya kasa cin kwallon da aka buga masa.
A minti na 90 Onyeka ya zura wa Super Eagles kwallon Najeriya na hudu a ragar Jamhuriyar Benin.
Wannan wasan ya nuna cewa Osimhen ba dan wasa bane kawai — jarumi ne, gwarzo ne, kuma jagora ne a fagen kwallon kafa.
Najeriya na kan gaba a wannan fafatawa, kuma alamu na nuna cewa Super Eagles na kan hanya madaidaiciya zuwa Kofin Duniya ta 2026.
Sai dai duk da haka, Najeriya na da kalubalen fafata wasan neman gurbin karshe, inda za ta sake karawa da wasu kasashe hudu uku da ke neman gurbin. Duk wanda ya samu nasara a cikinsu, shi ne zai samu gurbin karshe da ya rage a jerin kasashen Afirka da za su shiga gasar mai muhimmanci a duniya.