Yadda Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki
Bangaren noma da na masana’antu su ne bangarori biyu da suka ceto tattalin arzikin Najeriya daga matsin da ya shiga a zagon shekarar da muke ciki. Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Najeriya wacce ake kira NBS ta fitar ya nuna tattalin arzikin kasar ya farfado. Bangaren noma ya bayar da gagarumar gudunmawa na fiye da […]
Bangaren noma da na masana’antu su ne bangarori biyu da suka ceto tattalin arzikin Najeriya daga matsin da ya shiga a zagon shekarar da muke ciki.
Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Najeriya wacce ake kira NBS ta fitar ya nuna tattalin arzikin kasar ya farfado.
Bangaren noma ya bayar da gagarumar gudunmawa na fiye da kashi uku a cikin shekarar.
Hukumar NBS ta bayyana cewa gagarumin girbin kayan abincin da aka yi ya taka gagarumar gudunmawa a bangaren noman.
Ci gaban da aka samu a bangaren noman da masana’antu ya cike gibin da ke tsakanin albarkatun mai da wanda ba na mai ba.