Yadda Najeriya ta samu kanta a bakin gaba
Dalilan da matsalolin tsaro suka yi wa Najeriya dabaibayi a tsawon shekaru.
Tun kafin hawan gwamnati mai ci karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Najeriya ta samu kanta cikin kalubalen tsaro mafi girma a tarihinta.
Tun daga lokacin aka fara fuskantar matsalar masu tada kayar baya a yankin Naija Delta, wadanda suka ce suna yaki ne da matsalar gurbacewar muhalli da kamfanonin da ke aikin hakar man fetur a yankin suke haifarwa, zuwa rikicin addini da kabilanci a Arewa ta Tsakiya, da kuma bayyanar ’yan ta’adda da ke alakanta kansu da addini, wato Boko Haram, masu da’awar jihadi da burin dabbaka shari’ar Musulunci a Arewacin Najeriya.
- Shekara 61 na mulkin kai: Me za a yi wa murna?
- Jami’an tsaron Ghana sun binciki dan Majalisar Najeriya kan zargin ta’addanci
Fantsamar rikicin kabilanci a jihohin Arewa ta tsakiyar irin su Filato, Nasarawa, Binuwai da Taraba shi ya hassala matsalar zaman doya da manja da aka dade ana samu a tsakanin manoma da makiyaya.
A dalilin haka an samu asarar dimbin rayuka da dukiyoyi da karuwar gaba da kyamar juna tsakanin Fulani da kabilun Arewa ta tsakiya, zuwa wani bangaren Kudanci da Gabashi.
Wannan dambarwa ce ta kawo ga kafuwar gungun ’yan bindiga masu fashi da satar mutane, wadanda sau da dama aka fi alakanta su da Fulani makiyaya.
Daga jihohin Arewa ta tsakiyar zuwa yankin Arewa ta Yamma irin wadannan gungun ’yan bindiga na nan suna hallaka jama’a da haifar da matsalar tsaro da lalata dukiyoyi da sanya rashin yarda a tsakanin ’yan kasa, gami da karuwar talauci da gurguncewar tattalin arziki da karuwar ’yan gudun hijira.
Daga jihohin Arewa maso Gabas, tarwatsewar kungiyar Boko Haram ta haifar da rabuwarta zuwa wasu kungiyoyi masu hadari irin su ISWAP da Ansaru wadanda duk kokari da sadaukarwa da hadin gwiwar rundunar sojin Najeriya ke ci gaba da yi na tarwatsa ayyukansu da kwace garuruwan da suka mayar karkashinsu, ba su daina barazana ga tsaron kasa ba.
Idan muka duba a bangaren Kudancin kasar nan, musamman a jihohin kabilar Igbo da ke Kudu maso Yamma, an samu farfadowar kungiyar masu fafutikar sake kafa kasar Biyafara ta IPOB da ke barazanar ga kasancewar Najeriya dunkulalliyar kasa.
Ana kuma samun karuwar wasu kananan kungiyoyin ’yan ta’adda masu dauke da makamai suna ikirarin ballewa daga kasar nan, don kafa kasar ’yan kabilar Igbo zalla.
Rahotanni na baya-bayan nan na nuni da cewa a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya akwai kungiyoyin ’yan a-ware masu dauke da makamai fiye da 10, wadanda ke ci gaba da haifar da tsoro da rashin zaman lafiya a zukatan ’yan Najeriya masu kaunar hadin kai da zaman lumana.
Wadannan rigingimu da rashin tsaro su ne suka sa Najeriya shiga cikin jerin kasashen duniya da ke yawan fama da kalubalen tsaro.
A wani rahoto na baya-bayan nan da aka fitar an bayyana cewa, Najeriya ita ce kasa ta biyu bayan kasar Afghanistan da ake samun yawaitar mace-macen mutane a dalilin rikice-rikice masu nasaba da ta’addaci; Ita ce kuma ta farko a nahiyar Afrika, yayin da Somaliya ke biye da ita a matsayin ta biyu.
Kungiyoyin ’yan ta’adda masu dauke da makamai na ci gaba da bayyana, da manufofi iri-iri wadanda wasu za a iya warware su a siyasance ko ta hanyar amfani da tsare-tsaren gwamnati.
A kowace rana ta Allah sai an rasa rayukan farar hula ko jami’in tsaro, lamarin da ake danganta faruwarsa ga rashin daukar matakan da suka dace cikin gaggawa daga gwamnati da jami’an tsaro.
Karancin jami’an tsaro da za su iya tunkarar ta’addacin da ya addabi Najeriya daga bangarori daban-daban.
A yayin da ake dada tunkarar babban zaben shekarar 2023, ’yan siyasa da kungiyoyin kare muradun bangaranci da addini, da kanwa uwar gami baragurbin masu sharhi a kafafen watsa labarai, da ’yan a fasa kowa ya rasa, na ci gaba da amfani da zaurukan sada zumunta wajen yada manufofin kiyayya da rabuwar kai a tsakanin ’yan kasa, da nufin cim ma mugun nufinsu da son zuciyarsu, don ganin kasar ba ta zauna lafiya ba, matukar ba a yi yadda suke so ba.
A daidai lokacin da ’yan Najeriya ke murna da ci gaban da ake samu a yakin da ake yi da Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabas, rahotannin baya-bayan nan da ke fitowa daga Jihar Neja na bayyana bullar wasu gungun ’yan ta’adda da ake zargin suna da nasaba da akidojin Boko Haram a yankin Shiroro da makwabtan kauyuka, inda aka ce har sun kafa tutar jihadi a wuraren da suke ikirarin kamawa, tare da kafa wasu dokoki da ke kishiyantar manufofin gwamnati; Duk kuwa da kasancewar rohoton ayyukan wannan kungiya ya dade yana fitowa ta kafafen watsa labarai.
Tun da Najeriya ta rungumi tsarin dimokradiyya take fuskantar irin wadannan matsaloli, saboda munanan manufofi na bangaranci da kabilanci da wasu ’yan siyasa da masu rike da madafun iko ke amfani da su, wanda suke ganin ta haka ne kadai za su iya samun karfin fada a ji ko a dama da su a duk wata gwamnati da ta zo.
Yawan tarin makaman da jami’an yaki da fasakwauri ke kamawa a bakin iyakokin kasar nan, ana shigowa da su a boye, ko wanda ake biyo da su ta barauniyar hanya, amma jami’an tsaro su samu nasarar gano su, zai daga hankalin duk wani dan Najeriya mai kishin kasar nan, musamman idan ya yi la’akari da yadda harkokin tsaro ke dada lalacewa.
Sai mutum ya fara tunanin ko dai wasu na shirin tada yaki a kasar ne!
Masu nazarin harkokin tsaro na ci gaba da jan hankalin hukumomi game da tsananin bukatar daukar matakin gaggawa kan lamuran tsaro a kasar nan.
Sanannen abu ne cewa matsalolin da ake ciki sun yi wa jami’an tsaron da muke da su yawa.
Sannan gwamnati ba ta iya cim ma yawan adadin sabbin jami’an tsaron da ta yi alkawarin dauka duk shekara ba.
Sai an hada da ’yan banga masu aikin sa kai da ba su da wata cikakkiyar kwarewa kuma ba a ba su wani tukwicin a zo a gani da zai karfafa musu gwiwa ko ya hana masu son zuciya a cikinsu hada baki da bata-gari.
Har kawo yanzu dai an kasa cim ma matsaya game da muhawarar da ake yi a Majalisar Kasa game da bukatar kafa rundunar ’yan sanda mallakin jihohi da za su rika taimakawa wajen kula da kananan matsalolin tsaro na cikin gida da suka shafi fashi da makami, sabani na kabilanci da rigingimun ’yan tsagera da sauran su; Domin rage nauyin da ya yi wa sauran rundunonin tsaro na Gwamnatin Tarayya yawa.
Lallai ne hukumomin gwamnati, rundunonin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, sadarwa da wayar da kan jama’a su dukufa sosai wajen ganin an samar da hanyoyi na inganta samar da bayanan sirri, wayar da kan ’yan kasa game da muhimmancin kishin kasa, da dakile yadda ake yada labaran karya da amfani da kafofin sadarwar zamani wajen rura wutar rikici da sabani a tsakanin ’yan Najeriya.
Sannan yana da muhimmanci a rika tabbatar wa ’yan kasa irin hukuncin da ake yi wa wadanda ake kamawa da hannu da laifukan cin amanar kasa, hadin baki da ’yan ta’adda da ma aikata ta’addacin kansa, domin ya zama izinina ga sauran ’yan kasa masu mummunan nufi irin nasu.
A yayin da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ke ganin muhimmancin boye bayanan sirri, ’yan kasa na ganin hakan a matsayin wata gazawa da rufa-rufa daga wajen gwamnati, kuma hakan na rage kima da darajar hukumomi da ake yi wa kallon masu fada babu cikawa.
A farkon zuwan wannan gwamnati ’yan Najeriya sun yi burin ganin gwamnati ta cika alkawarin da ta daukar musu na fallasa masu cin amanar kasa da sace dukiyar talakawa.
Amma daga bisani sai zance ya canza, aka rika kumbiya-kumbiya da batun, har dai maganar ta bi ruwa.
Ko da yake daga bisani wasu bayanan na fitowa jifa-jifa, amma ba yadda aka zata a farko gwamnati za ta fitar da jerin sunayen masu ci da gumin talakawa ba.
Yanzu ma da aka ji cewa gwamnati na shirin tona asirin wasu bata-gari da ke taimaka wa ’yan ta’adda ta hanyar ba su tallafin kudaden sayen makamai ko adana musu kudade da tura su wani asusun ajiya na banki da idanun jami’an tsaro bai cika hawa kansa ba, ’yan Najeriya sun sa ran ganin a wannan karon gwamnati ta yi abin da suke tunanin shi ne daidai, kuma hakan zai dakile yawaitar ayyukan ta’addaci a kasa.
Nan ma dai daga bisani mun ji yadda turancin ya canza.
Ya kamata masu magana da yawun gwamnati su rika tauna magana kafin su furta ta, domin wani lokaci suna sa gwamnati a halin tsaka mai wuya, kuma kimar shugabanni na dada zubewa, saboda zargin da za a rika yi musu na siyasantar da sha’anin tsaro ko rashin tsayar da magana daya.
Idan muka koma kan maganar mu ta bukatar kara yawan jami’an tsaro kuwa, ina ganin ya kamata gwamnati ta dubi shawarwarin da aka ce Sarkin Kano murabus, kuma masanin tattalin arziki, Muhammadu Sanusi II ya bayar a makonnin baya, inda ya bayyana bukatar rage yawan kudaɗden da ake ware wa ’yan majalisun kasa, domin gudanar da wasu ayyukan cigaba.
Ina ganin idan har an yi hakan za a iya juya akalar wadannan kudade a bangaren tsaro, domin daukar sabbin jami’an tsaro, samar da karin makamai na zamani da horar da jami’ai kan sabbin dabarun yaki da ta’addanci, da inganta albashi da alawus alawus din jami’ai da ke yaki a bakin daga.
Yadda Gwamnatin Tarayya ke kukan rashin kudaden tafiyar da gwamnati da muhimman ayyukan raya kasa, lallai ne a duba yadda kudaden da ake samu suke zirarewa ta hannun wasu ’yan tsiraru da ke gwamnati da mukarrabansu, ko ake almubazzarantar da su da sunan tafiyar da ayyuka, ko albashin masu rike da mukaman siyasa, don a rage wasu abubuwa da za su yi amfani wajen magance wasu daga cikin matsalolin da suka dabaibaye kasar nan.