Yadda nake gane duk maganar da mutane suka yi – Sarkin Kuramen Jos

Malam Abubakar Sa’idu Abdullahi shi ne Sarkin Kuramen Jos a Jihar Filato, a tattaunawa da wakilinmu ya bayyana cewa yana iya gane duk maganar da mutane suka yi da yadda mutane suke jin maganar da ya yi, kamar shi ba kurma ba ne. Kuma ya bayyana irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ilimantar ’ya’yan kurame […]

Yadda nake gane duk maganar da mutane suka yi – Sarkin Kuramen Jos
Yadda nake gane duk maganar da mutane suka yi – Sarkin Kuramen Jos

Malam Abubakar Sa’idu Abdullahi shi ne Sarkin Kuramen Jos a Jihar Filato, a tattaunawa da wakilinmu ya bayyana cewa yana iya gane duk maganar da mutane suka yi da yadda mutane suke jin maganar da ya yi, kamar shi ba kurma ba ne. Kuma ya bayyana irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ilimantar ’ya’yan kurame a aikin koyarwar da yake yi da yadda larurar shanyewar bangaren jiki ta same shi, a lokacin da yake kokarin sasanta wasu kurame miji da mata:

Aminiya: Da farko za mu so mu ji  takaitatcen tarihinka?
Sarkin Kuramen Jos: To, an haife ni ne a 1964 a garin Kaduna, saboda a lokacin mahaifina ma’aikacin gwamnati ne. Daga nan muka dawo nan Jos, muka zauna a Layin Tsoho Salihu. Daga nan aka sanya ni a makarantar firamare ta Islamiyya, da ke Bauchi Road a nan Jos. Daga baya aka dauke ni aka kai ni kauye aka sanya ni a makarantar allo. Bayan haka sai mahaifiyata ta dauko ni ta dawo da ni wajenta aka sake sanya ni a firamaren St. Paul da ke nan Jos. Bayan na kammala firamaren, sai yayana mai suna Alhaji Kasimu ya zo ya ce ga wata sabuwar makarantar kurame an bude. Sai babana ya kai ni makarantar. Na shiga aji uku na kamala ta. Daga nan na zauna ban ci gaba da karatu ba. Sai aka sanya ni a koyon sana’ar kafinta da gini. Bayan na koyi wadannan sana’o’i sai na tara kudi na ce zan koma makaranta. Sai na shiga makarantar koyon sana’a ta tarayya wato Federal Technical College da ke Yaba a Jihar Legas, na yi diploma kan sana’ar gini a bangaren kurame na makarantar. Daga nan na dawo gida Jos, na koma harkokin wasanni a bangaren kurame. Muna tafiya da kurame gari-gari muna guanar da gasar wasannin motsa jiki na kurame. A wannan harka ta wasannin matso jiki ne na tafi har kasashen Kenya da Aljeriya.
Sai babana ya ce na yi aure, bayan na yi aure muka ci gaba da zama da mahaifina, a yanzu ina da mata biyu da ’ya’ya 15.
Aminiya: A wane lokaci larurar kurumta ta same ka?
Sarkin Kuramen Jos:  An haife ne da larurar ciwon kunne, na tashi tun ina karami na ga kunnena yana zubar da ruwa ana tushe min da soso.
Aminiya: To, yaya aka yi duk da kai kurma ne ba ka jin magana, amma kana yin magana kamar ba kurma ba, kuma kana gane maganar da mutane ke yi?
Sarkin Kuramen Jos: A gaskiya mahaifina ya sha wahala da ni kan wannan larura ta kurumta da Allah Ya dora min. Domin duk kokarin da ya kamata iyaye su yi, wajen bai wa ’ya’yansu ilimi, mahaifina ya yi min iya gwargwado. Ya kai ni Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) a kan wannan lalura ta ciwon kunne. A asibitin ne wani likiti ya ce zai yi wa mahaifina hanya a fitar da ni waje a yi min aiki a kunnen. Daga nan mahaifina ya sayar da kadarorinsa ya bayar da kudi muka tafi Legas muka yi wata biyu, ana horar da ni don na samu na rika yin magana. Daga nan muka tafi kasar Holland, a wannan kasa Turawa suka sanya mu a wani daki ana rawa a dakin, mu ma aka ce mu yi rawar haka muka rika kada kai. Daga nan suka kai mu wani asibiti. A wannan asibiti aka sanya mana wani inji  kamar hular kwano, wannan inji ya yi ta yi mana aiki. Daga nan sai muka fita daga wannan asibiti. Sai kuma aka hada mu da karnunaka suka rika horar da mu. Bayan haka, sai Turawan suka zo suka rika koya mana yadda za mu yi magana ta hanyar kallon bakin mutum idan yana magana ko kuma yadda za ka gane idan mutane suna magana da ka ko hannu. A haka muka yi wata shida ana yi mana horo a wannan kasa ta Holland. Saboda wannan horo da na samu a makarantar, ya sanya idan na kalli mutum a lokacin da yake magana nake gane abin da yake nufi.
Aminiya: Idan muka dawo ga sarautar Sarkin Kuramen Jos yaya aka yi aka nada ka a kanta?
Sarkin Kuramen Jos: To, ita wannan sarauta ta Sarkin Kuramen Jos, Allah ne Ya ba ni. Amma a gaskiya a lokacin da aka ba ni sarautar ba na so, saboda Sarki na farko aminina ne.  Kuma an kashe shi ne a lokacin da aka yi rikicin Jos a garin bukur. Aka zo aka nada Sarki na biyu Malam Yahaya bayan rasuwar Sarki na farko. To, shi ma wannan Sarki mun saba da shi sosai, sai ya ce min wata rana in Allah Ya yarda zan zama Sarkin Kurame. Sai na ce masa ba na so. Daga nan wata rana sai rashin lafiya ya kama shi, aka kai shi asibiti ya rasu. To, a she kafin ya rasu ya rubuta takarda ya bar wa matarsa cewa idan ya rasu, ni ne zan zama Sarkin Kuramen Jos. Da muka gama zaman makokin rasuwar Sarki sai aka ce za a nada ni Sarki, sai na ce musu ba na so saboda na san halinsu, mutane ne masu damuwa, amma aka matsa min na karbi wannan sarauta. Aka nada ni aka yi biki shekara biyar da suka gabata.
Aminiya: Wace gudunmawa ce kake ganin ka ba kurame da sauran nakasassu a Jos kake ganin ta sa aka nada ka a sarautar?
Sarkin Kuramen Jos: Na ba da gudunmawa da dama ga kurame da sauran nakasassu a nan garin Jos, musamman ta wajen karantar da yara kurame a makarantar da nake koyarwa ta Sunnah Pribate. Domin a lokacin da aka dauke ni aikin koyar da kurame a makarantar da kurame biyu na fara. Daga nan sai na fara yawo ina neman kurame unguwa-unguwa a nan garin Jos don su zo su shiga wannan makaranta. Da haka har Allah Ya sa muka tara kurame masu yawa a makarantar muka ci gaba da karantar da su. A yanzu daliban da na koyar a wannan makaranta, wasu har sun shiga jami’a wasu sun kama sana’o’i. A bangaren wasannin motsa jiki kuma akwai wadanda na horar da suna nan suna cin abinci a wannan harka.
Aminiya: Yaya aka yi wannan larura ta shanyewar bangaren jiki ta same ka?
Sarkin Kuramen Jos: To, wannan larura ta shanyewar jiki Allah ne Ya dora min. A lokacin da na hadu da larurar na bar gida lafiya-lafiya, na tafi wani gida don sasanta wasu kurame maji da mata da suke fada. Da ma ni ne nake sasanta duk wani rikici idan ya taso a tsakanin miji da mata kurame a nan Jos, saboda ba kowa ke gane maganar kurame ba sai ni. To, a lokacin da na je wajen sasanta wannan matsala, bayan na sasanta su, na yi musu fada, sun hakura. Sai na ji jikina kamar an jijjiga ni, na ji baki daya bangaren jikina na dama da hagu sun yi sanyi ba sa aiki. Nan take aka kai ni asibiti. Amma a yanzu na samu sauki har na fara dogarawa da sanda ina fitowa ina tafiya. A gaskiya jinyar wannan larura da nake yi mutane da dama sun taimaka mini musamman a lokacin watan azumin Ramadan da ya gabata. An taimaka min da addu’o’i da abinci da kudin magani. Amma duk da haka ina rokon jama’a su kara taimaka min da addu’o’i da daukar nauyin kudin asibiti da abinci kan wannan jinya da nake yi, musamman ganin yadda ba ni da karfin daukar nauyin wannan jinya kuma ga shi har yanzu ban gama warkewa ba.