Yadda nake gudanar da aikina – Dogariya A’isha
Hajiya A’isha Usman ita ce Shugabar Dogaran Matan Sarkin Zazzau, dattijuwar mai kimanin shekara 70 ta kasance a fadar sarkin tun kafin nadin Mai Martaba Alhaji Shehu Idris. A wannan tattaunawar da Aminiya ta ce ta kwashe shekara 65 tana aiki a fadar, inda take shugabantar mata dogarai. Har ila yau, ta yi karin haske […]
Hajiya A’isha Usman ita ce Shugabar Dogaran Matan Sarkin Zazzau, dattijuwar mai kimanin shekara 70 ta kasance a fadar sarkin tun kafin nadin Mai Martaba Alhaji Shehu Idris. A wannan tattaunawar da Aminiya ta ce ta kwashe shekara 65 tana aiki a fadar, inda take shugabantar mata dogarai. Har ila yau, ta yi karin haske game da aikinta musamman ta fuskar kula da matan sarkin da dai sauransu.
Aminiya: Wane lokaci kika fara wannan aikin?
Hajiya A’isha: Ni dai ’yar asalin Zariya ce, sunan unguwarmu Unguwar Lalle. Har ila yau, kakanmu ya koma kauyen Zabi da ke Sabon Gari kuma wannan ya sa mu a can Zabi aka haife mu. Na fara aiki ne a gidan Iyan Zazzau, wato Hakimin Sabon Garin Zariya.
An dauke aiki ne lokacin da Hakimin zai aurar da diyarsa, a matsayin Dogariya. Bayan na yi aiki na dan wani lokaci a gidan, sai na koma fadar sarki. Aka karbe ni hannu biyu-biyu kuma aka ba ni cikakken matsayi na Dogariya. Aka ba ni katin shaidar aikin da kuma duk wasu abubuwan alfarma da maza Dogarai suke samu.
Aminiya: Kina da aure?
Hajiya A’isha: Eh, ina da aure. Kuma mijina ma yana rike da sarauta wato Madakin Kakakin Sarkin Zazzau kuma har yanzu muna tare da shi. Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya uku, kodayake guda ya rasu kwana guda gabanin ranar nadin sarautar Alhaji Shehu Idris wato fiye da shekara 40 da suka wuce ke nan. Hakazalika, ina da jikoki fiye da 50.
Aminiya: A matsayinki na Dogariya me ye aikin ki a fada?
Hajiya A’isha: Babban aikina shi ne kula da aikace-aikacen da ake gudanarwa a fada. Ina kula da matan sarki da ’ya’yansa mata. Har ila yau, ina taka muhimmiyar rawar a duk lokacin da sarki zai aurar da ’ya’yansa mata. Inda nakan tabbatar da cewa komai ya tafi daidai ba tare da an fuskanci wata babbar matsala ba.
Ina kai da kawo a duka sassan gidan musamman bangaren matan sarki da kuma na ’ya’yansa mata. Bugu da kari, aikina ya fi karfi a harkokin cikin fadar sarki sosai. Kodayake, nakan yi wasu ayyuka a waje idan matan sarki sun fita wasu al’amura a wajen fada.
Aminiya: Me ye ya bambanta aikin ki da na Jakadiya?
Hajiya A’isha: Ita Jakadiya tana aiki ne da sarki, ni kuma ina aiki ne da matansa da kuma ’ya’yansa mata. Wannan ya sa aikin ya sha bamban. Jakadiya tana isar da sako ne tsakanin sarki da matansa ko kuma wasu baki, amma ni kula nake da matan sarki da kuma ’ya’yansa mata. A matsayina na Dogariya ina da alhakin kula da matan sarki ne. Nakan bi sahunsu duk wurin da suka nufa. Aikina shi ne samar da kariya ga matan sarki da kuma ’ya’yansa mata.
Aminiya: Ke kadai ce Dogariya a fadar?
Hajiya A’isha: A’a, akwai wasu dogarai mata akalla guda 12. Kodayake, ni na fi su shekaru. Wannan shi ya sa aka sanni sosai. Har ila yau, saboda shekaruna ina taka rawar uwa a fadar. Akwai lokuta da dama da na sha ba da shawarwari . Kamar yadda kuka sani uwa tana son abu mai kyau ga ’ya’yanta.
Aminiya: Wadanne abubuwane ba za ki manta da su ba?
Hajiya A’isha: Godiya ta tabbata ga Allah. Na samu alherai sosai albarkacin wannan aikin. Matan sarki suna kulawa da ni. Na taba zuwa kasar Saudiyya, inda na sauke farali da dai sauransu. Duka wadannan abubuwa ne da ba zan manta da su ba. Na gode wa Allah bisa komai.
Aminiya: Yaya dangantakarki da sarki take musamman ganin yadda ke ce kike kula da harkokin gida?
Hajiya A’isha: Dangantakata da shi mai kyau ce. Mukan ziyarce shi tare da sauran iyalansa. Nakan je na taya shi murna, ko na jajanta masa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
A lokacin da na zo fadar nan, sarki yana aikin malamin makaranta ne. Mun yi makarantar firamare tare da mai dakinsa a makarantar firamare da ke nan fada. A kan idonmu aka daura masa aure da matarsa ta fari. Wannan ya sa duka ’ya’yansa a gabanmu aka haife su. Kuma hakan ya sa suke dauka ta a matsayin uwa.
Kodayake, batun gaskiya kusancina da sarkin bai kai wanda yake tsakanina da matansa da kuma ’ya’yansa mata ba. Na fi kusa da marigayi Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu, wanda matarsa ta fari ta kasance uwar goyo ta.
Aminiya: Dogarai maza sun fi taka muhimmiyar rawa lokacin Hawan Sallah. Su kuma mata fa?
Hajiya A’isha: Mu ma muna taka rawa a fada. Mu ne muke tabbatar da tsaro a kewayen fada gabanin sarki ya fito Hawan Sallah. Muna kula da ’yan kallo mata kuma muna yi wa matan sarki rakiya. Wannan ya sa mu ma muke rike bulala domin ladaftar da duk wani mai tada zaune tsaye. Kodayake da zarar mun ga abin zai fi karfinmu, mukan bukaci agaji daga dogarai maza. Ina matukar kaunar wannan aikin.