‘Yadda nake hadawa da sayar da kayan yara’

Amina Bala tsohuwa ce mai shekara 50 da ke hadawa tare da sayar da kayan wasan yara na gwangwani domin dogaro da kanta, inda ta ce  ba ta aminta da halayyar wadansu tsofaffin mata da suka rasa mazansu ba, inda za a gansu suna yawon bara  da maula a gidajen masu kudi da sunan  neman […]

‘Yadda nake hadawa da sayar da kayan yara’

Amina Bala tsohuwa ce mai shekara 50 da ke hadawa tare da sayar da kayan wasan yara na gwangwani domin dogaro da kanta, inda ta ce  ba ta aminta da halayyar wadansu tsofaffin mata da suka rasa mazansu ba, inda za a gansu suna yawon bara  da maula a gidajen masu kudi da sunan  neman taimako.

Malama Amina a zantawarta da Aminiya a makon jiya a inda take baje kolin kayan da ta hada, ta ce ta jima tana wannan harka kuma ta samu alheri a cikinta sosai. “A yini nakan samu fiye da Naira 500 a wannan harka, kai wani lokacin har Naira 1000 ina samu. Kuma daga cikin wannan kudi nake ci da sha da sutura har in a jiye in yi wasu bukatun rayuwa. Duk lokacin da wata hidima ta tashi duk wanda ya ga abin da nake yi sai ya rika mamaki don mutane ba su ganin ina wani kasuwanci babba, amma rufin asirin da na samu a wannan harkar Allah kadai Ya sani,”  inji ta.

Ta ce kayan da take yi na wasan yara mata, takan yi masu tire da kwanon abinci da tukunya ta tuwo da miya da murhu da sauran kayan amfanin gida, sannan ta ce tana amfani ne da gwangwanin madara wajen yin wadannan abubuwa.

“Bayan wadannan kayan cin abinci na yara ina yi musu zobe da tandun kwalli da munduwa da sarkar kunkuru da sauransu, in na tafi Hubbaren Shehu na baje kayan, nan da nan suke karewa ka ga ana nema har Naira 2000 ina samu a yini a can. Matsalar da nake fuskanta a yanzu masu shayi da ke sayen madarar gwangwani ta gari sun koma sayen ta leda, gwangwanin da nake sarrafawa yana yi mini wuyar samu ba kamar da ba, rashin samun gwangwani ne ke sanyawa a zo ana neman kayan domin sun kare kuma babu gwangwani ballanata na sarrafa shi.” inji Amina.

Ta ce ta shafe kusan shekara 30 tana wannan harka a Kasuwar Marina da ke cikin Sakkwato a cikin harlar ta yi aure wa danta. Ta ce kayan da take sayarwa sun hada da kayan suya na yara, Naira 20, sai hauren yara Naira 20, zobe, Naira 20 da Naira 30 da sauransu. Mafi tsada shi ne za a samu ya kai Naira 50 kamar tukunya.

“Na zabi dogara da kaina don shi ne mafi alheri ga kowane mutum musamman wanda ya san abin da yake yi, ya tabbatar Allah ne mai raba arziki kuma Yana son ka tsaya inda ya tsayar da kai,” inji Amina Bala.