Yadda nake horar da kangararrun yara ba tare da duka ba – Malam Kawu
Malam Abdullahi Muhammad Tahir, wani malami ne mazaunin Titin Yakubu Wanka a cikin garin Bauchi da ake yi masa inkiya da Malam Kawu. Malamin ya sanu sosai wajen horar da matasa da yaran da suka kangare wa iyayensu saboda shiga harkar shaye-shaye suka zama kwarkwar. Wakilinmmu ya zanta da shi inda ya bayyana yadda yake […]
Malam Abdullahi Muhammad Tahir, wani malami ne mazaunin Titin Yakubu Wanka a cikin garin Bauchi da ake yi masa inkiya da Malam Kawu. Malamin ya sanu sosai wajen horar da matasa da yaran da suka kangare wa iyayensu saboda shiga harkar shaye-shaye suka zama kwarkwar. Wakilinmmu ya zanta da shi inda ya bayyana yadda yake wannan aiki na horar da kangararru su zama mutanen kirki:
Aminiya: Malam wadannan mutane mene ne alakarka da su?
Malam Kawu: Mutane ne wadanda suka kangare, za ka gansu manya da yara wadanda suka gagari iyayensu ba sa karatu, ba sa zuwa aiki, sun buge da sace-sace da shaye-shayen da suka taba musu kwakwalwa har kan kai wani ya ce zai kashe iyayensa. Su ne ake kawo su nan domin a gyara tarbiyyarsu su zama nagari. Bayan su kuma ina da almajirai wadanda aka kawo su domin karatu.
Aminiya: Ta wacce hanya kake horar da su ka gyara su su dawo mutane kamar kowa?
Malam Kawu: Alhamdullilahi Allah ne Ya ba ni wata baiwa ta musamman da nake amfani da ita wajen gyara tunaninsu kuma ina hadawa da addu’o’i wadanda da yardar Allah sai ka ga mutum idan ya kai wani lokaci ya gyaru ya dawo mutumin kirki.
Aminiya: Idan aka ce mutum kangararre ne kafin a kawo shi wajenka za ka ji an ce ya gagari kowa har duka yake yi saboda shaye-shaye, idan aka kawo shi daure shi kake fara yi ya natsu ko me kake yi?
Malam Kawu: Ana kawo mutum mari nake daura masa a kafa in yi masa addu’a nan take sai ka ga ya shiga hankalinsa, tun daga nan za ka ga ya daina fada shi ne abin da yake bai wa mutane mamaki. Daga nan ne nake fara bai wa mutum taimako har zuwa lokacin da zai zauna a gida kafin in sallame shi.
Aminiya: Shin gado ka yi ko yaya?
Malam Kawu: Baiwa ce daga Allah amma kuma ta wani wajen zan iya cewa akwai gadon, domin mahaifina kafin ya rasu yana ba da taimako na daure hannun masu ’yan sace-sace da masu shaye-shaye su daina. A wurinsa na fara gadar wani taimakon.
Aminiya: A garin Bauchi kawai kake zama don wannan aiki ko kana fita wasu jihohi?
Malam Kawu: A nan Bauchi nake zaune amma na taba zuwa Nijar ziyara ganin sun koka min da irin wannan matsala sai na taimake su kafin in dawo, kuma wanda na taimakawa din Allah Ya shirye shi. Maganar zuwa jihohi kuma, kawo min yaran ake yi daga kowace jiha domin yanzu haka a cikin manyan akwai na Gombe da Filato da Kaduna da Jigawa da nan cikin garin Bauchi har ma daga Abuja an kawo min yara.
Aminiya: Akwai wanda kake so ya gaje ke a wannan aiki da kake yi a cikin ’ya’yanka?
Malam Kawu: Eh zan so amma ’ya’yan nawa yanzu duk sun yi karatun boko suna da digiri ban san ko za su yarda su gaji wannan aiki da nake yi ba, domin su ’yan zamani ne duk da cewa sun yi karatun addini gwargwado. Ka san mutum ba zai so a ce abin da yake yi na alheri an daina yin sa ba idan ba ya raye.
Aminiya: Malam kamar shekara nawa ke nan yanzu kana yin wannan aiki?
Malam Kawu: Yanzu dai na kai sama da shekara goma domin a baya mutanen ba su da yawa domin ba su wuce biyar zuwa goma ba, amma tun lokacin da gidan rediyon Globe FM suka yi hira da ni aka ji labarina sai ne mutane suka yi yawa domin yanzu haka manya da yara da nake kula da su sun kai 70.
Aminiya: Ana biyanka wannan aiki da kake yi ko kyauta kake yi?
Malam Kawu: Maganar gaskiya ba a biyana, domin a da ni mai hali ne ina da motar hawa wacce nake zuwa da ita daji in nemo magunguna amma yanzu babu ita, ina da shaguna a kasuwar Santaral duk sun kare hakan ya sa nake karbar ’yan kudi kadan wadanda daidai suke da kyauta domin ba a iya biya duk da cewa akwai ’ya’yan manya da aka kawo su amma su din ma ba sa iya biyan komai.
Aminiya: Shin gwamnati ta san kana wannan aiki?
Malam Kawu: Eh gwamnati ta sani domin har sun taba kawo min tallafin katifun kwanciya, kuma matar Gwamnan Jihar Bauchi ta taba kawo mana gudumawar saniya aka yanka wa yaran a Sallar Layyar bara.
Aminiya: Bayan ka horar da yaran sun dawo hayyacinsu kana koya musu karatu ne?
Malam Kawu: kwarai kuwa yanzu ma ka gani da idonka ana koya musu karatun boko, da yamma kuma ana koya musu karatun addini duk da cewa wadansu da yawa sun wuce karatun amma shaye-shaye sun mayar da su baya, muna yi musu ne don su tuna abin da suka bari ya kubuce musu.
Aminiya: A shekarun da ka yi kana wannan aiki kamar mutane nawa ka gyara suka daina shaye shaye da sata?
Malam Kawu: Gaskiya ba na rubutawa saboda ka san aiki irin na almajirai tunda ba ina yi da tunanin za a zo a tambaye ni ba ne. amma dai sun kai mutum 100 domin akwai wadanda suke karatun likita yanzu haka a Sudan. Akwai wanda shi kuma yake Indiya ban san me yake karantawa domin bai fada min ba. Wadanda suke Makarantar Poly kuma ba za su kirgu ba, wadansu ma na manta da su sai dai wani lokaci ina zaune ka ga mutum ya zo ya gaishe ni, ya ce Malam ai mun zauna da kai a nan ya yi godiya ya yi min
alheri ban sa yawansu ba.