Yadda nake jinyar kunar wuta ta hanyar tofi – Ali MaiTofin Wuta

Malam Ali Mai Tofin Wuta, ya jima yana jinyar wadanda suka gamu da matsalar kunar wuta a jikinsu inda yake yi musu tofi su warke ba tare da ba da wani magani ba. Aminiya ta ziyarci shagonsa da ke kusa da Babbar Kasuwar Suleja a Jihar Neja, inda ya yi bayani kan yadda ya faro […]

Yadda nake jinyar kunar wuta ta hanyar tofi – Ali MaiTofin Wuta

Malam Ali Mai Tofin Wuta, ya jima yana jinyar wadanda suka gamu da matsalar kunar wuta a jikinsu inda yake yi musu tofi su warke ba tare da ba da wani magani ba. Aminiya ta ziyarci shagonsa da ke kusa da Babbar Kasuwar Suleja a Jihar Neja, inda ya yi bayani kan yadda ya faro aikin da yadda yake gudanar da shi:

 

Mene ne sunanka kua daga ina kake?

Sunana Malam Ali Mai Tofin Wuta. Ni dan asalin karamar Hukumar Dawakin Kudu ne a Jihar Kano. Na yi sha’awar zuwa garin Suleja ne bayan na ji yekuwar neman jama’a su zo Abuja ta gidan rediyo a shekarun baya, inda wani mawaki mai suna Alhaji danlami Nasarawa ya yi a farkon kafa sabon Birnin Tarayya. To da na zo sai na zauna a nan Suleja, wannan ya faru ne kamar shekara 25 da su ka wuce. Amma idan ana maganar fara jinyar masu kunar wuta ne to na fara tun lokacin da nake gida kamar shekara 40 baya.

Wannan aiki da kake yi ka gaje shi ne ko daga baya ne ka koya?

A gaskiya ban gaji aikin ba, horewa ce ta Allah. Yadda abin ya faru shi ne, wani yaro ne ya kone sai ake ta tunanin ina za a kai shi, sai na ce bari in yi masa addu’a kamar yadda ka ga nake yi a nan, wato in yi karatu in hura don ko tofawa ban yi. Kuma cikin ikon Allah sai ya fara samun saukin zafin a lokacin sannan bayan wasu kwanaki ya warke. To ganin abin da ya faru da irin haka ta sake faruwa sai aka kawo mini wani, shi ma Allah Ya taimaka ya warke. To shi ke nan fa daga nan sai aka rika kawo mini masu matsalar ina duba su . Daga baya sai na koma cikin birni a Layin Shehu Azare da ke Fagge a birnin Kano. Sai dai koda na je wurin sana’ata ta soya kifi ita kadai nake yi kuma ba wanda ya san ni da wannan aiki. To ana cikin haka sai wani yaro ya fadi a cikin mai na suya, shi ma na duba shi bayan wani lokaci ya samu sauki, shi ke nan fa daga nan idan matsalar ta faru sai a kawo mutum wurina. Sai na yi sha’awar zuwa Abuja, jama’a sun nemi sanin ina zan koma amma sai na ce da su ku bar ni kawai ba na son a san inda zan koma. Ko da na zo nan Suleja sana’ar awo na shiga kasancewar ita na samu abokina Muhammadu Halidu yake yi a cikin babbar kasuwa. Daga baya ne na dawo nan inda ka same ni na fara sana’ar kayan tireda. Bayan dawowata nan inda ka same ni da sana’ar tireda, to da Allah Ya tashi bayyana abin ga jama’a sai wata mai tuya da ke makwabtaka da mu ta gamu da matsalar kuna za a kai ta asibiti sai na ce ku bar ta, na duba ta aka dace ta samu sauki bayan wasu kwanaki ta warke. Bayan nan sai wani makwabcinmu mai suna Malam Nuhu Tela ya kone a fuska da hannuwa, sai wannan wadda na duba ta farkon ta ce Malam Ali a taimaka masa mana, shi ma sai na duba shi. To bayan na yi masa ne sai abin ya bayyanna ga kowa aka fara kawo mini mutane daga ko’ina a nan Arewa da Kudu. Aiki kuma daga fitowata daga masallaci bayan Sallar Asubahi zan samu ana jirana da wasu a kofar masallaci tun daga can nake farawa sai na gama da su sannan na karasa gida. A can ma gidan kafin in fito wadansu sun taru haka zan yi musu, ina zuwa shago kuma nan ma zan samu wadansu na jirana, haka zan rika duba su daya bayan daya har zuwa lokacin da zan rufe shago in dawo gida.

Kamar daga wadanne wurare ne mutane ke zuwa?

Daga jihohin Arewa da Kudu, wadansu ana kawo su ne da sun kone, wadansu kuma sai an kai su asibiti sai ma’aikatan asibitin su turo su nan, wadansu kuma sai matsalar ta faskara a can tukuna ake kawo su, babu dai irin wanda babu.

Wane abu ne kake yi a wajen yi musu jinyar?

Wannan tofi da ka ji ake cewa ba ya wuce nan, shi ne zan yi karatu in busa a wajen da matsalar ta faru ba ma tofawa ba, sannan in yi wani a cikin ruwa a wuce da shi gida ana sha ana shafawa wanda zai taimaka wajen wanke zafin kunar ta ciki kamar yadda fitsarinsu ke bayyanawa, gobe ma a sake dawowa har mutum ya warke.

A cikin wadanda ka duba ko akwai wanda matsalarsa ta girgiza ka?

A gaskiya ya riga ya zame mini jiki, kuna duk muninta ba ta girgiza ni bare har na yi mafarkinta, haka zan fuskance ta. Mutum zai zo da zafin kuna yana kuka amma bayan farawa da wani lokaci sai zafin ya gushe, kuma komai yawan jama’a haka zan fuskance su daya bayan daya har mu gama. Kamar matsalar gobarar tanka da ta faru a Tafa a kwanakin baya an kawo mutum wajen 30 a lokaci guda, wadansu ma a sume aka kawo su nan, amma alhamdulillahi duk wadanda suka jure da jinyarmu kusan duk sun samu sauki. Daga cikin wadanda ’yan uwansu suka wuce da su zuwa wasu wurare ne muka samu labarin wadansu sun cika daga baya.  Nakan dai samu takaici idan na ji labarin yadda wadansu suka gamu da matsalar musamman mata inda za ka ji kishiyarta ce ta kona ta wata ma da ciki wata dan kishiyar ne za ta kona, ga su nan dai iri-iri, haka muke ta fama da su.

A duk abin da mutum ke yi bai rasa wata matsala, a naka gefen mece ce babbar matsalar? 

A gaskiya ni a nan ba ni da wata matsala kama daga masu zuwa wajen nan ko kuma masu wannan shago da nake haya a wajensu inda nake hadawa da sayar da kayan tireda. Kowa nawa ne ba Musulmi ba Kirista, ba mai gari ba talaka kuma duk wani babba da ka sani a garin nan malami ne ko dan kasuwa ko kuma jami’in gwamnatin, to ya san da zamana a nan, saboda ya kawo wani nasa nan ko ya kwatanta wajen ga wani nasa an yi masa aiki. Ban da wata matasala da wani duk wanda aka kawo shi nan za a yi masa aiki kuma da izinin Allah a samu nasara, idan dai ba ta karar kwana ba ce, wadda ita ba ta da magani, sai godiya ga Allah.

Ko kana da wani buri kamar na kafa waje na musamman don gudanar da wannan aiki? 

Ni dai babban burina shi ne Allah Ya ci gaba da ba ni karfin gwiwar yin wannan aiki sannan Ya samar da warakar.

A cikin ’ya’yanka ko akwai wanda ka fara dorawa a kan wannan hanya ta yadda koda bayanka ne aikin zai ci gaba?

Akwai dana Abdullahi da ka same ni da shi, tare muke gudanar da aikin a wasu lokutan ma ya yi shi kadai, saboda haka ko a yau na kasance ba na raye ina fatan zai iya tafiyar da aikin insha Allah.

Yaya batun hakki kamar nawa kake karba daga majinyaci? 

A baya ba na yanka wa mutum abin da zai bayar sai kawai abin da ya ga ya sauwaka gare shi. To daga baya ne da aikin ya yi yawa har na fara neman sauwaka wa kaina tare da tunanin yadda zan daina. Sai wadansu suka karfafa min gwiwa a kan in rike aikin sosai tare da yanka wa wanda ya zo abin da zai bayar. To a nan ne na fara yanka wa mutane kudi a tsawon jinyar da za su yi wanda ko kusa ba za a hada shi da wanda ake karba a asibiti ba, sai dai ko a nan din ma sai abin da jama’ar suka iya, ba na tsaurara musu a kan lallai sai sun ba da abin da na yanka musu.