Yadda nake sana’ar nika in gyara inji – ’Yar firamare

Wata yarinya ’yar shekara 10 mai suna Rukayya Ahmed da take gudanar da sana’ar nikar garin masara da dawa a garin Saminaka a Jihar Kaduna, ta ce wannan sana’a ta nika gari, ta yi mata daidai. Rukayya Ahmed ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da jaridar Aminiya, inda ta ce babanta ne […]

Yadda nake sana’ar nika in gyara inji – ’Yar firamare

Wata yarinya ’yar shekara 10 mai suna Rukayya Ahmed da take gudanar da sana’ar nikar garin masara da dawa a garin Saminaka a Jihar Kaduna, ta ce wannan sana’a ta nika gari, ta yi mata daidai. Rukayya Ahmed ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da jaridar Aminiya, inda ta ce babanta ne ya koya mata wannan sana’a tun tana karama.

Ta ce a yanzu tana yin wannan sana’a ita kadai da kanta, ta tayar da injin ta yi aikin nikar, kuma idan injin ya lalace ta kwace shi ta gyara, sannan ta tayar ta ci gaba da aiki.

“Babana yakan yi tafiya ya bar ni da injin, ya yi kwana da kwanaki ya dawo ya samu, babu wata matsala. A duk rana nakan yi  aikin Naira 1,500 wata rana Naira 2,000 wata rana  har Naira 3,000 nake yi,” inji shi.

Rukayya Ahmed ta yi bayanin cewa  duk da wannan sana’a da take yi, tana zuwa makarantar firamare domin a yanzu tana aji hudu na makarantar firamare. Kuma idan lokacin tafiya makaranta ya yi, takan rufe ta tafi idan an ta so ta zo ta sake bude injin ta ci gaba da aiki.