Yadda nake sarrafa bawon rake zuwa abincin dabbobi – Malam Yakubu

Wani tsohon ma’aikacin gwamnati da ke zaune a Gombe mai suna Malam Yakubu Ahmad Shu’aibu ya ce shi ne mutum farko da ya fara sarrafa bawon rake ya mayar da shi abincin dabbobi a Jihar Gombe.Dattijon wanda  shi ne Hakimin Unguwar Orji Kwatas a garin Gombe, ya yi bayanin yadda yake sarrafa bawon raken ne […]

Yadda nake sarrafa bawon rake zuwa abincin dabbobi – Malam Yakubu
Yadda nake sarrafa bawon rake zuwa abincin dabbobi – Malam Yakubu

Wani tsohon ma’aikacin gwamnati da ke zaune a Gombe mai suna Malam Yakubu Ahmad Shu’aibu ya ce shi ne mutum farko da ya fara sarrafa bawon rake ya mayar da shi abincin dabbobi a Jihar Gombe.
Dattijon wanda  shi ne Hakimin Unguwar Orji Kwatas a garin Gombe, ya yi bayanin yadda yake sarrafa bawon raken ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce ya yi aikin gwamnati na tsawon shekara 35. Bayan ya kammala ne ya nema wa kansa abin yi don gudun zaman banza da biya wa kansa bukatunsa na yau da kullum.
Ya ce: “Wata rana ina zaune sai na samu labarin injin sarrafa abincin dabbobi  a wajen tsohon Sarkin Bodor Alhaji Saleh Tinka, domin shi yana sarrafa abincin dabboninsa ne kasancewarsa makiyayi. Daga nan ne na fara, amma na fara ne da sarrafa karan masara daga baya da na ga ba ya tafiya kamar yadda ya kamata, sai na yi tunanin fara sarrafa bawon rake,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Mutane sun fara gane wannan nau’i na abincin dabbobi har na fara samun oda ina sarrafa wa makiyaya. Kasancewar wannan inji yana iya sarrafa duk wata ciyawa ko danya ko busasshiya.”
Ya ce “galibin jama’a sun dauka bawon raken shara ne kawai saboda ba su san yadda za su yi da shi ba. Amma ka ga mu ke zuwa mu debo mu wanke sai mu zuba a inji ya nika shi, ya zama dusa, wadda ta fi dusar masara amfani a jikin dabba saboda akwai wasu sinadarai a rake wadanda babu su a jikin masara.”
Malam Yakubu ya ce yana sarrafa wannan  bawon rake ne a gidansa, amma yanzu yana shirin zai fadada shi zuwa kamfani nan gaba kadan zai yi masa rijista da hukuma da sunan dan Madami Feed Company.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki