Yadda namiji ya rika amfani da sunan mace yana damfarar maza a Facebook
Ya cuci ma’aikatarmu Naira 206,000 kudin tikitin jirgi zuwa Uganda domin aiki inji Bulama Bukarti
A makon nan ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gabatar da wani matashi mai suna Musa Lurwanu bisa zarginsa da amfani da sunan Zarah Mansur a kafar Facebook wajen damfara, inda ya damfari mutane da dama makudan kudade.
Musa L. Maje, da ke amfani da sunan Zarah Mansur, wata budurwa da ya taba nuna yana sonta, amma ba ta amince ba, daga nan ne ya bude shafin Facebook da sunanta, sannan ya ci gaba da amfani da hotunanta masu kyau da suka sha ‘filta’.
- Kotun Koli ta yi fatali da shari’ar Buhari kan Dokar Zabe
- Takarar Lawan da Akpabio ta tada kura a APC
Yakan shiga tattaunawa kan batun yau da kullum, sannan daga nan ya zabi wani ya shiga tattaunawa da shi, inda daga nan ne yake neman kudi kan za ‘ta’ zo ta same shi.
Ko kuma ya nemi bidiyon tsiraicin namijin, inda daga baya zai rika amfani da bidiyon wajen neman kudi, ko ya fallasa mutumin a duniya.
Yadda nake yaudarar mutane —Musa
Da yake bayani ga ’yan sanda, Musa, wanda ke amfani da sunan Zarah a Facebook, ya ce yana amfani da manhajar Magic Boice ne wajen mayar da muryarsa ta mata.
A game da Zarah ta asali, ya ce, “Da farko na fara sonta ne, amma daga baya muka daina maganar. Dama ina da hotunanta, sai nake amfani da su wajen neman kudi.
“Daga cikin wadanda suka turo min kudi, akwai wanda ya turo min Naira dubu 206,000 wanda dan Kano ne mazaunin kasar waje da wanda ya turo Naiar dubu 10, da wani dan Jihar Nasarawa da ya turo min Naira dubu 100 da wani abu.
A bi min hakkina —Zarah ta asali
Da take bayani kan lamarin, Zarah Mansur ta asali ta ce ta shiga damuwa ce lokacin da aka rika cewa ana ganinta a shafuka da yawa a Facebook tana magana.
Hakan ya sa ta fada wa mahaifiyarta da yayarta, sannan kawayenta suka ba ta shawara ta yi bidiyo ta ce ba ita ba ce.
Zahra ta ce akwai wata rana ma da wani ya tare ta a hanya, ya ce yaya za a yi suna magana sosai a Facebook, amma sun hadu tana share shi, wanda hakan ya sa har ya yi fushi.
A karshe ta ce, “Gaskiya a bi min hakkina. Dama farko cewa ya yi yana sona, ni kuma ban amince masa ba.”
Mu leka shafin Zarah Mansur
Aminiya ta leka shafin Facebook na Zarah Mansur na karya da Musa L. Maje ya bude, inda ta gano yadda ya tsara shafin da hotunan Zarah masu kyau.
A shafin, ya nuna cewa ya yi karatu ne a Jami’ar Kursk State Medical University da ke kasar Rasha, sannan yana aikin sanin makamar aiki ne a Asibitin Gundumar Maitama a Abuja, inda yake zaune, amma asalinta Kano ce.
Shafin na da mabiya 35,804 a lokacin da Aminiya ta leka.
Akwai tattaunawa da Aminiya ta ci karo da shi tsakanin Zarah Mansur ta karya da wani mai suna Malam Buhari, inda a ciki Zarah ta bukaci ya aiko da awara da yaji daga Sakkwato, za ta turo wani dan uwanta ya karba, shi kuma ya ce zai saya mata har da karin Naira dubu 100 ta sha ruwa tare da cewa, “Da girman kujerarki Hajiya.”
A wata tattaunawar kuma, Aminiya ta kalato yadda Zarah din ke bukatar bidiyon tsiraicin wani, inda ya ce zai shiga bandaki su yi magana ta bidiyo, sai Zarah din ta karya, ta ce ya dauka, ya turo mata kawai, wanda shi kuma ya amsa.
Yadda ya damfare mu —Bulama Bukarti
Da yake magana kan batun, Barista Bulama Bukarti ya ce Mansur ya yaudare su ta hanyar zamba cikin aminci ya karbi Naira 206,000, sannan ya ce ba duk wadanda ya yaudara din ba ne masu neman mata.
A cewarsa,“Ba dukkan wanda Zahra Mansur ya cuta ba ne maneman mata. Ni ma ya cuci ma’aikatarmu Naira 206,000 kudin tikitin jirgi zuwa Uganda domin aiki.
“Dalili kuwa shi ne ya yi mana karya cewa a can ya gama karatun likitanci kuma ya yi aikin duba marasa lafiya a cikin kauyukan Musulmin Uganda.
“Ni kuma ma’aikatarmu suna taimaka wa kauyuka ne a Uganda da Kwango amma kasancewar su Amurkawa, ba su da alaka mai karfi da al’ummar Musulmi, saboda haka mafi yawan masu amfana da tallafinsu ba Musulmi ba ne.
“Da na fara aiki da su wata biyu da suka wuce, daya daga cikin manyan ayyukan da suka so in mai da hankali a kai shi ne kulla alaka mai karfi da Musulmi.
“Ni kuwa na sanar da su cewa akwai wata ’yar Najeriya da ta yi karatu a can da za ta iya taimaka mana. Muka yi waya da ita Zahra Mansur, ofishinmu suka tura mata kudin jirgi Naira dubu 206.
“Ni kuma na yi magana da matar wani tsohon ambasada da ke zaune a Kampala cewa idan Zahra Mansur ta zo, za ta zauna a gidansu har mu gama aikin.
“Daga baya muka gane dan damfara ce. Na so in bibiyi maganar, har ma na yi dan wannan rubutun na kasa a Facebook a ranar 14 ga Mayu, 2022 (ya sa wani hoton rubutun da ya yi a lokacin cewa wadansu mutane a Facebook kamar mutanen arziki, amma mutanen banza ne), amma ma’aikatarmu ta ce in bar maganar.
“Asalin sanin Zahra Mansur kuwa ya faro lokacin da na je Uganda a Nuwambar 2021.
“Lokacin da ya ga hotunanmu da daliban can, sai ya tuntube ni cewa a can ya gama, kuma ya ce ya ji muna maganar cewa ana neman likitoci a Ingila a shirin Fashin Baki da muke da Barista Abba Hikima da Jagora Jaafar Jaafar.
“Ya ce yana son neman aikin likita a Ingila. Na ce zan hada shi da wani abokina da yake aikin likita a Ingila, amma ban samu damar hakan ba.
“Kuma daga nan ba mu sake magana ba sai da ofishin suka nemi in nemo hanyar kulla alaka da Musulmin Uganda da Kwango.
“Bayan mun gane cewa Zahra Mansur dan damfara ne, na nemi wasu hanyoyi na samu wadanda suka san Musulmin Uganda da Kwango.
“Cikin hanyoyin da na bi har da kiran ma’aikatan BBC irin su Abdu Halilou da Muhamman Babalala suka hada ni da ’yan Najeriya mazauna can. Kuma hakan ya yi nasara. Alhamdulillah.
“Da na je na samu ganawa da kuma kulla alaka mai karfi da Musulmin kasashen biyu. Allah Ya sani ban taba maganar banza ko ma ta soyyayya da wannan dan damfara ba ko wata a kafofin sadarwa, magana ce ta aiki, wanda daga baya muka gane damfara ce,” inji shi.
Ana ta ce-ce-ku-ce
Bayan maganar Mansur ta fito, sai mutane suke ta cewa neman mata ne ya sa mutane suke amincewa da macen da ba su taba gani ba, har su tura mata kudi.
Wannan caccakar, ba ta bar Barista Bulama ba, inda wadansu suke cewa shi ma an damfare shi ba tare da ya yi bincike ba.
Sai dai fitaccen lauya a Kano, Barista Abba Hikima ya fito ya kare Bulama, inda ya ce, “Duk wanda ya san rayuwar Malam Audu Bulama Bukarti ko da ta kwana daya ce, zai yi masa shaida da alheri da kyakkyawan zato.
“Kuma dama wannan shi ne shiriyarmu. Ni shaida ne a kan mutane da dama da Malam ya taimaka.
“Wadansu ma bayan ya sama musu aiki a Ingila, zai sauke su a gidansa da ke can. Duk don su taimaki kansu.
“Wadansu kuma ni yake aikawa da kudi domin in ba su hannu da hannu. Saboda ba wai wani kwazo wancan dan damfara ke gare shi ba.
“Duk mutumin da yake da zuciya mai kyau zai dauka kowa ma na kirki ne.”
Shafin zai taimaki Zarah
Rabi’u Biyora Shi kuma Shugaban Kamfanin Fafutika, Malam Rabi’u Biyora cewa ya yi a bar wa Zarah shafin domin ta ci gaba da amfani da shi, domin a cewarsa, za ta samu amfani sosai da shafin.
“A nawa bangaren kira zan yi ga Rundunar ’Yan sandan Kano, a kan su duba yiwuwar mallaka wa Zarha Mansur ta gaskiya shafin na Facebook wanda Musa ya bude da sunan Zahra, tunda dai da sunanta ya yi amfani har ya tara mabiya sama da dubu 35.
“A ba ta shafin sai a sanar a hukumance cewa yanzu ita ainihin Zarah za ta ci gaba da amfani da shi.
“A wannan lokaci da muke tunkarar zamanin fasahar METAVERSE (fasahar sadarwa) ina kyautata zaton mallaka wa Zarah shafin, hakan zai iya zama alheri gare ta zuwa gaba,” inji shi.