Yadda na’urar ATM ta zazzago kudin bankin yara a Indiya

’Yan sandan birnin Kanpur da ke kasar Indiya sun fara bincike kan yadda wata na’urar zaro kudi ta ATM ta fitar da wasu jabun takardun kudi daga bankin yara na Indiya (children Bank of Indiya), dauke da hoton gwarzon Indiya, Mahtma Gandhi. Mutanen da suka yi kokarin zarokudinsu daga wannan na’urar ATM sun dugunzuma da […]

Yadda na’urar ATM ta zazzago kudin bankin yara a Indiya

’Yan sandan birnin Kanpur da ke kasar Indiya sun fara bincike kan yadda wata na’urar zaro kudi ta ATM ta fitar da wasu jabun takardun kudi daga bankin yara na Indiya (children Bank of Indiya), dauke da hoton gwarzon Indiya, Mahtma Gandhi. Mutanen da suka yi kokarin zarokudinsu daga wannan na’urar ATM sun dugunzuma da bacin rai da takaici.

Masu asusun ajiya a bankuna da suka citokudi daga wannan na’urar ATM a birnin Kanpur sun nuna rashin jin dadinsu kan ATM ta bankin Adis, wadda aka kafa a kasuwar Marble d ake Kanpur,kamar yadda kafar labarai ta DNA ta ruwaito daga Indiya. Biyu daga jerin takardun kudin Rs500 na nuni da cewa an buga su ne a Bankin Yaran Indiya.

Rahoton kafar labarai ta ANI ta bayyana cewa wani mutum ya gabatar wa ’yan sanda korafin cewa ya ciro kudi Rupees dubu 10 na Indiya, amma aka turpo mas ajabun daurin kudin 500.

“Na zo in ciro dubu 10 na Rupees ( kudin Indiya). daya daga cikin kudin na dauke da tambarin Bankin Yara na Indiya. Mun yi kokarfi ga mai gadin ATM din, wanda ya duki rajistar kudin. Sai  ya sanar da ni cewa za a dauki mataki, kuma za a sauya mana takardun kudin ranar Litinin,” inji Sachin, mutumin da ya zaro kudin.

Mun yi kokarfi ga mai gadijn na’urar ATM, wanda ya dauki rajistar kudi. Sai aka sanar da mu cewa za a dauki matakin da ya dace, sannan a sauya mana wasu kudin ranar Litinin a cewar sachin.

Kafafen yada labarai na ANI da DNA ne suka bayyana labarin bazuwar takardun kudin bankin Yara na Indiya, wadanda aka zazzago daga na’urar Bankin Adis a kasuwar Marble da ke birnin Kanpur.

 

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu