Yadda ni da liman muka tsira daga harin bam – Sarkin Ladanan Kano
A sakamakon kazamin harin bama-bamai da harbe-harben bindigogi da ya hallaka mutane da dama tare da raunata mutane da yawa a babban masallacin birnin Kano ranar jumu’ar da ta gabata, Sarkin Ladanai na masallacin, Alhaji Habibu Sarkin Ladanai, ya bayyana yadda ya kubuta daga harin tare da Limamin masallacin, Farfesa Sani Zaharadden. Ya kuma ce […]

A sakamakon kazamin harin bama-bamai da harbe-harben bindigogi da ya hallaka mutane da dama tare da raunata mutane da yawa a babban masallacin birnin Kano ranar jumu’ar da ta gabata, Sarkin Ladanai na masallacin, Alhaji Habibu Sarkin Ladanai, ya bayyana yadda ya kubuta daga harin tare da Limamin masallacin, Farfesa Sani Zaharadden. Ya kuma ce tun fiye da shekara 100 da gina masallacin ba a taba kai masa hari ba, sai a wannan karon.
Alhaji Habibu, mai shekaru 76 a duniya, ya ce, “a takaice wannan masallacin ya fi shekara dari da ginawa, kuma tun yana ginin kasa na san shi, amma ko a lokacin rikicin Maitatsine ba a taba kawo masa hari ba, sai a wannan lokacin.”
Ya ce da shi da limamin masallacin, Farfesa Sani Zharadden da sauran wadanda suke sahun gaba, Allah ne kadai Ya sanya suka kubuta domin dukkaninsu kwanciya suka yi a kasa, har sai da aka gama harbe harben.
A lokacin da aka kai harin dai an yi sa’a Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu, ba ya nan, yana kasar Saudiyya don yin Umarah. Idan yana gari a wannan masallacin yake sallar Juma’a, a wadansu lokutan ma, shi yake yin limanci. Ga dai yadda cikakkiyar hirar ta kasance:

Aminiya: Ranka ya dade ya ya wannan harin ya faru?
Shi wannan abu ba tun yanzu ake yin shirinsa ba, an dade ana take-taken kawo hari wannan masalachin, kuma sun dade suna yin leken asirin yadda za su kawo harin, sai yanzu ne suka samu kawo harin.
Aminiya: Ta yaya suka shigo masallacin?
Ai kafin su shigo ma an gan su, kuma ba da sonsu bom din cikin mota ya tashi a bakin titi ba. Su nufinsu su shigo har tsakiyar jama’a kafin su tayar da shi. Da motar ta nufo cikin jama’a a lokacin ana shirin tayar da sallah, har sai da mutane suka yi ta magana ganin yadda motar ta kutso cikin taro kuma wadansu ma sun bi motar don su tsayar da ita, har sai da wani ya leka ciki, sai ya ga cewa abin da yake ciki ba na alheri ba ne. Ana haka ne sai kawai bom din ya fashe tare da kara mai karfi.
Mutane da dama sun mutu daga fashewar bom din, wadansu kuma sun ji raunuka, kuma harin ya shafi ‘yan kasuwa da suke kasa kaya a bakin titi. Duk na kusa da wajen sun hallaka, bayan nan kuma sai harbi ya biyo baya.
Aminiya: Da wane lokaci ne harin ya fara?

A lokacin da Liman ya tayar da kabbarar farko ne, kawai sai muka ji karar tashin bom. Daga nan mutane suka rude, sai Liman ya katse sallah, sai daga baya ne wadanda suka tsira kowa ya yi sallarsa daban.
Aminiya: Gaskiya ne cewa har a cikin masallaci bom ya tashi?
Eh, Bom biyu ne ya tashi a cikin masallaci. daya ya tashi ne a tsakiyar masallaci, daya kuma yana shirin tayar da shi a kofar ‘yan Hisbah, sai wani dan Hisbah ya kama shi da kokawa, ya doka shi da kasa. Daga nan sai ya kufce, ya nufi kofar kudu ta masallacin, inda ya tayar da bom din. Dukkaninsu ‘yan kunar bakin-wake ne, sun mutu tare da sauran mutanen da suka rasu.
Aminiya: Kana ganin dama suna nufin su tayar da bom din a tsakiyar masallaci ne?
Nufinsu su zo sahun gaba, amma da suka ga ba za su iya ba, shi ne suka tayar da shi a nan wajen. Mutane ne da suka hana su su iso zuwa gaban sahu, domin da ma shi Mai martaba Sarki a gaba yake, haka ma sauran manya da Liman da mu da sauran mutane da muke sahun gaba.
Aminiya: gaskiya ne cewa wani ne ya yi wa Liman rumfa, ya rufe shi da jikinsa?
A’a, babu wanda ya yi masa rumfa, sai kariyar Allah kawai. Ni ina nan a kwance kusa da bakin kofar da sarki yake shiga, ana ta tattake ni ana wucewa. Allah Ya ba ni nutsuwa, ban rude ba. Ina nan a kwance har zuwa lokacin da abin ya lafa, sai wani yarona Bello ne ya zo ya daga ni, ya zaunar da ni.
Amma hakika mun ga tashin hankali, don babu abin da bai faru ba, an samu raunuka da yawan gaske, kuma an mutu da yawa. Sai dai ni a cikin ikon Allah ban samu ko rauni ba.
Aminiya: To me ya faru bayan nan?


To bayan harin dai kowa ya zo masallacin nan zai ga yadda wajen ya yi kaca-kaca da jini da naman jikin mutane ko’ina, ga kuma wuraren da harsashi ya huhhuda. Wajen dai gaba daya kamar yaki aka yi. To daga baya ne bayan Mai martaba Sarki ya dawo, ya bayar da umarnin a wanke shi kuma a gyara. Yanzu an ci gaba da yin sallah, kamar yadda ka gani.
Aminiya: To ku ne manya da kuka san tarihin wannan masallacin. Ko an taba samun wani lokaci da aka kawo hari masallacin, banda wannan harin?
A tarihi wannnan ne lokaci na farko da na sani wanda aka kawo hari wannan masallacin, domin ko a lokacin rikicin Maitatsine ba a kawo hari masallacin nan ba. A takaice kuwa wannan masallacin ya fi shekara 100, tun a lokacin yana ginin kasa, har aka zo lokacin da Sarki Abdullahi Bayero ya sake masa gini, ya yi wanan ginin da ake gani yanzu, a shekarar 1954. Ko ni din nan na san shi a lokacin yana ginin kasa. Don yanzu na kai shekara 76 a duniya.
Aminiya: Wane kira za ka yi a game da abin da ya faru?
Mu dai mun saddakar wa Allah, mun san cewa babu yadda za mu yi, kaddara ce Ubangiji Ya kawo ta. Sai a yi ta yin addu’ a Allah Ya kare mu kuma kada Allah Ya sake nuna mana faruwar irin haka a nan gaba.