Yadda NNPCL ya gwara kan ’yan Najeriya kafin ya gaskata cewa yana biyan tallafin mai

Bayan kauce-kauce, a ƙarshe NNPCL ya tabbatar cewa yana biyan tallafin mai kuma yawan bashin tallafin na barazana ga ayyukansa

Yadda NNPCL ya gwara kan ’yan Najeriya kafin ya gaskata cewa yana biyan tallafin mai

Malam-Mele-Kyari

A ƙarshe kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) ya gaskata cewa ya ci gaba da biyan tallafin mai kuma ana bin sa bashi, bayan kamfanin ya dade yana musanta batun biyan tallafin.

NNPCL ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar ba zai iya wadatar da Najeriya da man fetur ba, sakamakon yawan bashin da ’yan kasuwa ke bin sa.

Kakakin na NNPCL, Olufemi Soneye, ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambaya kan bashin Dala biliyan shida na tallafin mai da ake zargin ’yan kasuwa na bin kamfanin.

Jami’in ya ce yawan bashin da ya yi wa kamfanin NNPCL katutu na barazana ga ƙarfinsa na samar da isasshen mai a Najeriya.

Kodayake  bai faɗi haƙiƙanin yawan bashin da ake bin kamfanin ba, amma dai ya yi wannan bayani ne bayan NNPCL ya jima yana jaddada cewa ya daina biyan tallafin mai, tunda Gwamnatin Tarayya ta soke shi.

Haka kuma a baya kamfanin ya yi ta kauce-kauce da musanta cewa  ’yan kasuwa da ke shigo da tataccen mai Najeriya suna bin shi bashin kuɗaɗen tallafi.

Amma dai, wani rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya bayyana cewa yawan bashin da dillalan ke bin NNPCL ya kai Dala biliyan shida.

Rahoton ya nuna cewa kuɗin tallafin da NNPCL ke biya ya ninku ne tun a watan Afrilun 2024 sakamakon tashin Dala, wanda ya kawo ƙaruwar farashin man a kasuwar duniya.

Tashin Dala ya kuma haddasa ne ƙaruwar farashin litar mai a Najeriya, wanda a sakamakonsa aka samu ƙaruwar kudin tallafin da ake biya a kan kowace lita.

Rahoton ya ce tun a watan Maris na 2024 da yawan kuɗin tallafin fetur ya haura Dala biliyan uku, NNPCL ya fara tangal-tangal dangane da biyan kuɗaɗen tallafin.

Sai dai kamfanin ya musanta cewa tun watan Janairun 2024 bai sanya ko sisi ba a Asusun Gwamnatin Tarayya.

Ya kuma ƙaryata labarin cewa dillalan mai na bin sa bashin Dala biliyan 6.8.

Amma kuma, ya ce, ba sabon abu ba ne yin ciniki a kan bashi a ɓangaren harkar mai; abu ne da aka saba, don haka, idan ma har NNPC ya ci bashi, ba laifi ba ne.

Sannan NNPCL ta hannun reshensa na kasuwanci, wato NNPC Trading, yana da tsarin biyan basuka, gwargwadon yadda aka karɓe su.

A cewar kamfanin na NNPCL, baya ga kuɗaɗen da ya sanya a asusun tarayya, dukkan rassansa suna biyan harajin da ya dace ga hukumomin gwamanti, da kuma duk sauran masu haƙƙokin da suka dace.

Hasali ma, NNPCL ne ja-gaba wajen samar da kuɗaɗen shiga da ake rabawa a kowane wata na Kwamitin Asusun Tarayya.

A cewarsa, babu abin da ya shafi NNPCL da batun farashin shiga ko fitar da mai Najeriya, domin wannan alhaki ne da ya rataya a wuyan hukumar MNDPRA, kuma ba a ƙarƙashin NNPCL take ba.

Anan dai abin lura shi ne, bayan duk wadannan bayanai dai, a karshe kakakin na NNPCL ya amsa cewa yawan bashin da ’yan kasuwa ke bi na tallafin mai, yana barazana g samuwa isasshen mai a Najeriya.

Duk da cewa  bai faɗi ainihin yawan bashin ba, amma wannan bayanin nasa ya tabbatar cewa Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da biyan kuɗin tallafin mai.

Sannan wannan bayani ya zo ne bayan NNPCL ya jima yana cewa ya daina biyan tallafin.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda