Yadda noman albasa ya kara habaka bana a Sakkwato

A bana noman albasa ya kara samun habaka da tagomashi abin da ya sanya manoman darawa a Jihar Sakkwato. Mafi yawan manoman da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu da wannan nasarar da suka samu: Shugaban Kungiyar Masu sayar da Albasa ta Jihar Sakkwato Alhaji Murtala Bawa Mai Albasa ya bayyana cewa “A […]

Yadda noman albasa ya kara habaka bana a Sakkwato

Wani dillalin albasa

A bana noman albasa ya kara samun habaka da tagomashi abin da ya sanya manoman darawa a Jihar Sakkwato. Mafi yawan manoman da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu da wannan nasarar da suka samu:

Shugaban Kungiyar Masu sayar da Albasa ta Jihar Sakkwato Alhaji Murtala Bawa Mai Albasa ya bayyana cewa “A bana manoman albasa sun samu amfani sosai, yanayin ya yi kyau, mafi yawan matasan da suka shiga harkar sun ci karensu ba babbaka, duk da yawan noma da amfanin albasar da aka samu  a bana  ba a samu cushewarta a kasuwa ba saboda bukatarta da mutane ke yi,  amfani da ake yi da ita ya karu ainun,.

Alhaji Murtala Bawa ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawarsa da Aminiya a Sakkwato.

Babban wurin da ake hada-hadar kasuwancin albasa da ke cikin Kasuwar Kara a birnin Sakkwato, ba wata rana a cikin mako da ba za a samu ana hada-hadar kasuwancin albasa ba,  kullum ba za a rasa tirela 20 da za su bar Sakkwato zuwa wasu wurare a sassan  Najeriya da kasashen waje ba dauke da albasa ba.

“Muna dakon dubban buhunnan albasa a kowa ne mako musamman yanzu da bikin Kirisimati yake kara kusantowa” inji Alhaji Murtala Bawa.

Shugaban ya bayyana suna daukar kayan albasa  zuwa Legas da Fatakwal da Aba da Oweri da kuma Ondo da sauran wurare a Najeriya da kasashe irin su Ghana da Kamaru da Kwadibuwa da Kwatano babban birnin Benin.

Wakilinmu ya samu labarin cewa a jihar manyan ’yan kasuwar albasa suna sayen buhunta a hannun manoma kai-tsaye kan Naira dubu 26 zuwa 28 su kuma su sayar da Naira dubu 30 zuwa dubu 32 ya danganta da kasuwar, saboda gwari ce ana iya cin riba kuma ana iya faduwa warwas.

Abdura’uf Muhammad manomin albasa ne mai shekara 50, wanda ya yi shekara 35 yana noman albasa wanda ya fito daga Karamar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato ya ce, “Akwai albasa sosai da ke jiran masaya a cikin kasa da wajenta, a bara na samu buhu 900 amma a bana na samu buhu 1500. Kasuwar ta bana ta kara sanya ni darawa, maimakon in shigo gidana da dubban Naira sai na shigo da miliyoyi, saboda kasuwar ba ta bayar da mu ba.”

Alhaji Abubakar Giyawa mai shekara 45 da ya kwashe shekara 20 yana noman albasa ya ce noman albasa a bana yana cike da nasara da farinciki.

“Bukatar albasa ta karu a nan cikin gida da kuma fitar da ita zuwa kasashen waje wannan albarka ce da manoman jihar nan suka samu.”

Ya kara da cewa, “Wannan ci gaba ya hana wa kasuwarmu cushewa duk da yawan kayanmu, masaya a cikin gida da waje suna ta kara-kaina wajen sayen albasar.”

Abubakar ya bayyana cewa a bara ya samu buhu 30 ya sayar da kowane buhu Naira dubu 20 amma a bana ya samu buhu 50 ya sayar da su tsakanin Naira dubu 26 zuwa 27 ga kowanensu.

“Na kashe kusan Naira dubu 200 a noman albasata yanzu ko na samu sama da Naira miliyan daya na gode Allah kan wannan baiwa,” inji shi.

Bede Akaulor mai shekara 42 haifaffen Jihar Imo wanda ya yi shekara 14 a cikin harkar kasuwancin albasa a Sakkwato ya  ce a bara farashin buhun albasa Naira dubu 25 ne zuwa dubu 27 amma yau ana sayarwa Naira dubu 31 zuwa dubu 32.

Ya ce, kowane buhu ana dakonsa daga Sakkwato zuwa Imo a kan Naira 2,500 ko 3000 ya dangata da mota.

“A kowane mako nakan yi dakon buhun albasa 20 zuwa 30, amma in Kirsimeti ta zo nakan kai fiye da buhu 120” inji shi.

’Yan kasuwar sun koka kan yadda jami’an tsaro ke takura musu a kan hanyarsu ta zuwa Imo daga Sakkwato da sauran wurare.

“Muna asarar kusan Naira dubu takwas a kowa ce mota daya da ta dauki albasa, haka yana barazana ga jarinmu, jami’an tsaro suna kara matsa mana musamman yanzu da Kirsimeti ta matso kusa,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Ina farautar albasa in kai ta Imo, bayan Sakkwato ina zuwa Aliero da Kebbi a Jihar Kebbi sai Kano da Zariya, a duk shekara ba tare da na huta ba sai na zagaye wadannan wurare.”

Shugaban ’Yan kasuwar albasa Alhaji Murtala Bawa Mai Albasa ya kara tabbatar da zargin da mambobinsa ke yi na yadda jami’an tsaro ke tare su a shingayen duba ababen hawa na sassan kasar nan suna karbar na goro.

“Naira dubu 10 ko 20 muke asara a kowane shinge kafin ka isa inda za ka je ka kashe Naira dubu 100, hakan  ba ya taimakon kasuwancinmu,” inji Shugaban wanda yake da mambobi fiye da 500.

“Shingaye a Kudu maso Kudu da wasu a bangarori na Kudu masu Gabas sun fi matsala fiye da na Kudu maso Yamma. Sakkwato zuwa Legas hadaddiyar kungiyar masu sayar da kayan abinci na girki ta kasa sun tsabtace hanyar, ba irin wadannan shingayen na wahala,” inji shi.

Haka kuma kungiyoyin manoma da na ’yan kasuwar albasar sun nemi gwamnati ta taimaka musu da kayan amfani na zamani da tallafin bashi mai sauki da takin zamani don su kara bunkasa harkar ta kai ga wani mataki da ya wuce wannan a yanzu.