Yadda noman lalle ke samun tagomashi a Sakkwato

Noman lalle yana kara bunkasa tare da samun tagomashi a Jihar Sakkwato, sakamakon yadda ’yan mata ke shiga cikin harkar sana’ar lalle don samun kudin shiga da inganta tattalin arzikinsu a yunkurinsu na kauce wa zaman  kashe zane. Garuruwan da suka ciri tuta a harkar noman lallen a Jihar Sakkwato sun hada da Gandi a […]

Yadda noman lalle ke samun tagomashi a Sakkwato
Yadda noman lalle ke samun tagomashi a Sakkwato

Noman lalle yana kara bunkasa tare da samun tagomashi a Jihar Sakkwato, sakamakon yadda ’yan mata ke shiga cikin harkar sana’ar lalle don samun kudin shiga da inganta tattalin arzikinsu a yunkurinsu na kauce wa zaman  kashe zane.

Garuruwan da suka ciri tuta a harkar noman lallen a Jihar Sakkwato sun hada da Gandi a karamar Hukumar Rabah da Goronyo da Dundaye a karamar Hukumar Wamakko da Milgoma a karamar Hukumar Bodinga da sassan kananan hukumomin  Yabo da Wurno da kuma Kware.

Sai dai lallen da ake nomawa a Gandi ne ya fi fice ta fuskar kasuwa da farin jini da yawan masu saye da ke zuwa daga wurare daban-daban a Afirka. Haka kuma sun fi yawan matan da ke sana’ar lallen, koda yake dadaddiyar al’ada ce a kasar Hausa da mata ke yi don kwalliya, inda yawancin mata ba su iya zama ba lalle bisa gamsuwarsu cewa abu ne da ke kan gaba cikin kayan kwalliya.

Kazalika masana’antun lalle na kara bunkasa har a kasashen Asiya ana kasuwanci da sarrafa shi, manoman suna samun albarkarsa a lokacin yabanya da cira, inda babban manomi a Gandi yakan iya samun buhu 500 zuwa 1000 a kullum lokacin taba har zuwa cire amfanin gaba daya. Kamar yadda wadansu manoma, Shehu Umar da Kabiru Lawal suka bayyana wa wakilinmu  a garin Gandi.

Kuma sun ce manoman da kansu ne suke daukar lalle zuwa kasuwannin irin su Ilela  da Sakkwato har da Kwanni a Jamhuriyyar Nijar don samun riba. A wuraren ne wadansu ke dauka zuwa kasashen Indiya da China, inda ake sarrafawa a masana’antun zamani.

Noman lalle da ake yi musamman a Gandi ya kara sanya ’yan mata shiga harkar lalle gadan-gadan, aikin  tabarsa da cire masa haki da sanya shi ya bushe har zuwa zuba shi a buhu.

Malam Ali babban dan kasuwar lalle ne, wanda ya ce sukan saye dukan gonar lalle ne a tabar musu a busar musu shi kawai su dauka zuwa kasuwa, kuma suna biyan ’yan matan da ke yi masu aikin daga Naira 300 har zuwa 1000, kuma mafiya yawansu suna amfani da kudin da ake biyansu ne wajen sayen kayan dakin aurensu. Wannan ya sanya a gefen hanyar Gandi za ka samu mata a jere sun shanya lalle suna gyaransa ba tare da suna kula masu tafiya ba, wannan neman kudin suna iya kwashe awowi 12 suna yin sa a yini daya.

“A yini daya ina iya samun Naira 600, ko yanzu da nake maganar nan na sayar da mudu uku na lalle kowane mudu a kan Naira 200, mukan fito tunda safe mu tashi kusan Azahar ko wuce haka, nakan ajiye kudina na sayi kayan daki da na biki,” inji Suwaiba Tsamiya, daya daga cikin masu gyaran lallen.

Malam Ibrahim Isah ya shafe fiye da shekara 11 yana kasuwancin lalle, ya bayyana nau’ukan lallen da  cewa, “Lallen da kake gani yana da nau’uka uku, sagagi da baranda da ubandawakin sagagi. Ana noman su a Gandi da Wurno da Goronyo da Mafara. Kuma a duk shekara ana nomansa ne sau biyu, shi ne ya sanya ba sa katsewa sai dai canja launi. A duk damina lalle yakan canja launi daga danyen haki shar zuwa fatsi-fatsi, ba don ruwa ko wani abu ya taba shi ba. Kafin damina lalle ya fi tsada, buhunsa na kaiwa har dubu Naira 5500 zuwa 6000 sabanin yanzu da bai wuce Naira3000 ba.

“Mutanenmu suna daukarsa zuwa Dubai da sauran kasashe a Afirka. Asarar lalle daya ce, ka bar shi tare da ’ya’yansa wuri daya baka cire su ba, to asara ce za ka yi mai yawa sosai, domin ba ya zama da kwarorinsa a hade yanzu zai rube ya lalace,” inji Malam Ibrahim.

Haka shi ma Muhammadu Saminu, mai kimanin shekara 70 da ke noman lalle a garin Gandi, ya ce kasarsu tana da kyau a noman lalle fiye da sauran garuruwan da ke noma shi, “Muna da irinsa kusan ko’ina a gonarmu, hakan ya sanya wadansu ke sanya shi iyakar gona,” inji shi.

A wurin da aka fi sayar da lalle a babbar kasuwar Sakkwato, wani babban dan kasuwar lalle mai suna Murtala Tukur, mai shekara 38 ya ce “A matsayina na dillalin lalle a wannan kasuwa, ina da abokan ciniki da ke sayen lalle suna tafiya da shi kasashen waje irin su Dubai da Indiya da Nijar da wasu kasashen Afirka da na Larabawa irin Sudan da sauransu.”

Zinatu Aliyu Mande ’yar shekara 15 da ta share shekara shida tana sana’ar yi wa mata lalle, ta shaida wa Aminiya cewa “Ban koyi wannan sana’a wurin kowa ba, a yi wa kannena ne na iya lallen iri biyu, akwai baki da ja, a wurin hada launin ja akan sanya sajen da muhaladiya da farin magi da sabo da tsamiya. Baki kuwa ana hada shi da janko kawai. Muna sayen kayanmu a kasuwar Marina da babbar kasuwa.”

“Amma mutane sun fi son bakin lalle, a yini nakan yi wa mutum 20 zuwa 25 idan akwai su a kasa, ya danganta da lokaci. A duk minti 20 ina kammala wa mace daya. Lallen da ba zan taba mantawa da shi ba, shi ne na kawata da ke cewa duk lallen da nake yi, na ta ya fi kyau. A cikin lalle ja ya fi saukin yi, ina yi wa amare da wuraren suna. Na dauki lalle sana’ar dogaro da kai, kan haka har Abuja da Kebbi da Zamfara da Kaduna ina tafiya wurin yin lalle ga amare. Mata na son lalle don yana cikin kawa, da wuya su daina yin lalle, mazansu na sonsa. Lalle yana gogewa a jikin mace mako daya zuwa kwana 10 kafin nan ana iya sanya rilakza ko kanwa don goge shi a yi sabo,” inji Zinatu. 

Ita ma Maryam Muhammad ’yar shekara 17 ta ce tunda ta tashi take harkar lalle, iri uku, ta iya ja da baki da maroon kuma ya bambanta da sauran don shi ana sanya lemon tsami da ruwan lipton. “In kina son lalle ya yi ja sosai kuma garin lallen ana sanya masa fetur da zobo da magi fari ko farasitimol ko sukari, idan aka yi yana iya daukar mako biyu bai goge ba. Yin lallen Hausa ya fi wahala fiye da sa fulawa, ta rani ba da salatif  ba. Ina yi wa mace 10 a yini nakan amshi Naira 300 zuwa sama, duk yadda mutum ya ba ni bana tambaya,”  inji Maryam.