Yadda Obasanjo ya bamu cin hancin dubu 500 domin mu tsige Ghali Na’abba- Honorabul Jagaba

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ba wa duk wani dan majalisa Naira dubu 500 domin mu tsige shugaban majalisar na wancan lokacin Ghali Umar Na’abba. Dan Majalisar Wakilai Honorabul Jagaba Adams Jagaba ne ya sanar da hakan a lokacin da yake bayar da shaida a kan shara’ar Farouk Lawan wanda ake zargi da cin […]

Yadda Obasanjo ya bamu cin hancin dubu 500 domin mu tsige Ghali Na’abba- Honorabul Jagaba

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ba wa duk wani dan majalisa Naira dubu 500 domin mu tsige shugaban majalisar na wancan lokacin Ghali Umar Na’abba.

Dan Majalisar Wakilai Honorabul Jagaba Adams Jagaba ne ya sanar da hakan a lokacin da yake bayar da shaida a kan shara’ar Farouk Lawan wanda ake zargi da cin hanci da rashawa na harkallar kudin rarar man fetur a Babban Kotun Abuja da le Lugbe.

Da yake amsa tambayoyi a kotun, yaw a jami’an bangaren zantarwa ne suka kawo musu kudin a wancan lokacin domin su tsige Ghali.

“A lokacin na kawo kudaden majalisa inda na nuna cewa fa an kawo cin hanci. Na imamin cewa cin hanci ne domin nag a lokacin da aka kawo kudin,”