Yadda Oshiomhole ya mika wuya ga NEC din Giadom
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Adams Oshiomhole ya mika wuya ga rushewar da Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Kasa (NEC) ya yi wa Kwamitin Ayyyuka na Kasa (NWC). Oshimole ya kuma ce zai janye dukkan kararrakin da ya shigar kotu kan rikicin shugabanci a jam’iyyar. Ya shaida wa ‘yan jarida a ranar Asabar 27 ga […]
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Adams Oshiomhole ya mika wuya ga rushewar da Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Kasa (NEC) ya yi wa Kwamitin Ayyyuka na Kasa (NWC).
Oshimole ya kuma ce zai janye dukkan kararrakin da ya shigar kotu kan rikicin shugabanci a jam’iyyar.
Ya shaida wa ‘yan jarida a ranar Asabar 27 ga watan Yuni, cewa ya umarci lauyoyinsa janye daukacin kararrakin da ya shigar kotu.
Oshiomhole ya jaddada gamsuwa da gudunmawarsa ga jam’iyyar, sannan ba ya nadamar abubuwan da ya yi.
Sanarwar na zuwa ne kwana biyu bayan NEC ta rushe NWC sakamakon rikicin shugabanci da ya kawo sabuwar baraka a jam’iyyar.
Rikicin ya tsananta ne bayan kotu ta dakatar da Oshiomhole daga kujerarsa, lamarin da ya haifar da rabuwar kai a NWC game da magajinsa.
Tsohon Mataimakin Sakataren Jam’iyyar, Victor Giadom, ya ayyana kansa yayin da kuma NWC ta nada Hilliard Eta, Mataimakin Shugaba (Kudu maso-Kudu).
A hannu guda kuma Oshiomhole na shirin daukaka kara domin kalubanatar dakatarwar da aka kotun daukaka kara ta yi masa.
Daga baya Giadom ya kira taron NEC mai cike da ka-ce-na-ce inda a nan aka rushe NWC wadda ta kunshi Oshiomhole da sauran mambobi.
Kazalika zaman ya nada Kwamitin Riko da zai gudanar da Babban Taron Jam’iyyar na Kasa, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.
A babban taron ne za zabi sabbin shugabannin da za su gudanar da jam’iyyar a matakin kasa.
Buni shi ne tsohon Sakataren Jam’iyyar na Kasa kafin ya sauka ya yi takarar gwamna.