Yadda Oyegun da wasu suka sami amincewar sake tsayawa takara

  Shugaban jam’iyyar APC da sauran shugabannin jam’iyyar sun sami amincewar sake neman tsayawa takara karo na biyu.   Da yakje jawabi a taron shugabannin jam’iyyar, Shugaba Buhari ya godewa membobin kwamitin dangane da ayyukan da suka yi cikin lokaci inda suka yi maganin matsalolin da suka dabaibaye tazarcen shugabannin jam’iyyar.   Ya ce “Hakan […]

Yadda Oyegun da wasu suka sami amincewar sake tsayawa takara

 
Shugaban jam’iyyar APC da sauran shugabannin jam’iyyar sun sami amincewar sake neman tsayawa takara karo na biyu.
 
Da yakje jawabi a taron shugabannin jam’iyyar, Shugaba Buhari ya godewa membobin kwamitin dangane da ayyukan da suka yi cikin lokaci inda suka yi maganin matsalolin da suka dabaibaye tazarcen shugabannin jam’iyyar.
 
Ya ce “Hakan ya nuna irin yadda kuka mayar da hankali kan tabbatar da ganin ci gaban jam’iyyarmu ta yadda za ta ci gaba da gudanar da mulki na gari don ci gaban Najeriya”.
 
“Idan muka yi la’akari da cewa siyasa al’amari ne na yawan lamba saboda haka bai kamata mu raba kanmu ba kamata ya yi mu ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya duk da bambance-bambancenmu kamar yadda doka ta tanada”. Inji shi