Yadda ragon layya ya kusa raba magidanci da iyalinsa
Jama’a masu karanta jaridar Aminiya musamman masu bibiyar wannan shafi ina musu sallama irin ta addinin Musulunci, Assalamu Alaikum. Da fatan an yi salla lafiya, kuma Allah Ya maimaita mana na badin-badada. A duk lokacin da na yi rubutu a kan wani batu na kan samu sakonnin yabo masu tarin yawa da hakan ya nuna […]
Jama’a masu karanta jaridar Aminiya musamman masu bibiyar wannan shafi ina musu sallama irin ta addinin Musulunci, Assalamu Alaikum. Da fatan an yi salla lafiya, kuma Allah Ya maimaita mana na badin-badada.
A duk lokacin da na yi rubutu a kan wani batu na kan samu sakonnin yabo masu tarin yawa da hakan ya nuna ana gamsuwa da rubutun da nake yi. Hasalima makaranta da dama kan nuna cewa irin rubutun da nake yi tamkar wa’azi ne. Akwai wata da ta boye sunanta da lambarta amma ta tabbatar mini ita matar aure ce. Ta ce na ceto rayuwarta a rubutun da na yi a kan Illar Rashin Haihuwa ga Ma’aurata don abin ya shafe ta, har ta fara tunanin ta kauce hanya sai ta karanta rubutu kuma ta bi shawarwarin da na bayar. Hakan ya sa ta aiko mini da sakon godiya inda ta nuna rubutun da na yi ne ya kubutar da ita daga fadawa cikin halaka inda ta yi mini godiya da kuma addu’ar fatar alheri. Wannan sako da ma wasu makamantan haka da ake turo mini daga makaranta maza da mata, ya dada karfafa mini gwiwa wajen ci gaba da fadakarwa a duk al’amurran da na ga suna bukatar gyara a cikin al’umma.
To a yau na tabo wani batu ne da ya tayar mini da hankali, a kan wani labari da na samu na yadda ragon layya ya kusa raba wani magidanci da matansa 3 a wani gari da zan sakaya sunansa.
Wani magidanci ne yake da mata uku. Allah Ya yi masa arziki daidai gwargwado. A duk shekara idan sallar Layya ta zo yakan yankawa kowacce daga cikin matansa uku ragon layya, bayan nasa da na mahaifiyarsa.. A takaice a duk Sallar Layya yakan sayi raguna 5 zuwa sama ne inda yake yankawa tare da iyalinsa da mahaifiyarsa da kuma bayar da wasu kyauta ga abokansa da kuma ’yan uwansa.
Wannan attajiri rahoton ya nuna ya dade yana gudanar da haka, sai dai a Sallar bana (wacce aka yi a ranar Juma’ar da ta wuce), matsalar tattalin arziki ta shafe shi, Allah Ya jarabce shi da matsalar rashin kudi. Ya yi duk mai yiwuwa don ganin ya samu sukunin saya wa matansa uku ragunan layya amma abin ya faskara. Ganin haka sai ya yanke shawarar ya sayi rago daya, don ya yanka a madadinsa da iyalansa saboda a rufawa juna asiri. Ashe rago dayan da ya samu wani amininsa ne ya saya masa saboda ya fahimci halin da yake ciki.
Bayan an sauko daga sallar Idi ne, sai amininsa ya aika masa ragon gida, inda shi kuma ya shaida wa matansa halin da ake ciki. Abin takaici da kuma mamaki shi ne yadda matansa ukun suka hade masa kai suka ce atafau sai ya yanka wa kowace daga cikinsu rago kamar yadda ya saba. Sun nuna su ba za su iya yin tarayya a rago daya ba. Ba irin wa’azi da jan hankalin da bai yi wa matan ba a kan su hakura ya yanka wannan rago daya idan Allah Ya kai mu badi kuma abubuwa suka yi daidai zai ci gaba da yanka wa kowace rago kamar yadda ya saba. Nan dai suka kafe, suka ce atafau, ba gudu, kuma ba ja da baya. ko dai ya fita ya samo sauran raguna uku ko kuma ya fita da rago dayan daga gidan.
Nan fa hankalin maigidan ya tashi ya fahimci akwai rashin hankali da kuma shegantaka a wajen matansa, Bai zame ko’ina ba sai wurin mahaifiyarsa ya kuma shaida mata halin da yake ciki. Nan take ya umarci kaninsa ya je gidansa ya kamo wancan rago. kaninsa bai yi kasa a gwiwa ba ya tafi ya kamo ragon, inda aka yanka shi a gidan mahaifiyarsu.
Nan magida ya sa aka kada rago kuma ya yanka, aka fede ya rarraba naman ga ’yan uwa da abokan arziki kuma ya sanya mahaifiyarsa ta soya masa sauran inda ya rika ziyartarta yana cin abinsa ba tare da wani tashin hankali ba.
Sauran matansa uku da suka ji shiru sai kowacce ta yi yaji ta koma gidansu. Washegarin sallah surukansa suka neme shi daya bayan daya don jin dalilin da ya sa ’ya’yansu suka koma gida. Nan ya yi musu bayani dalla-dalla. Nan fa hankalin iyayen ya tashi inda suka nuna wa ’ya’yansu ai su ko kaza ba su samu sukunin yankawa a gidajensu ba, balle rago. Nan dai suka roki magidancin da ya yi hakuri su koma dakunansu, amma ya nuna hakan ba zai yiwu ba. Hasalima ya ce tun da abin haka ya kasance kuma tsiya suke ji to shi ya yanke shawarar yin sabon aure ne tun da dama bai taba haihuwa da kowace daga cikin matansa ukun ba.
Magidancin ya nuna ashe da ma ba zaman Allah da na Annabi yake yi da matansa ba, dukiyarsa kawai suke so, to tun da haka ne, a ganinsa bai dace ya ci gaba da zama da su ba, kamar yadda ya shaida wa surukansa.
Nan fa hankulan surukansa suka yi matukar tashi sai suka yanke shawarar nemo makusantan magidancin don su lallashe shi a madadinsu ya mayar da ’ya’yansu. Da kyar da jibin goshi ya amince kafin ya mayar da su amma ya gindaya musu sharadin idan hakan ta sake faruwa zai dauki mataki a kansu.
Daga nan ne matan suka gane kurensu, kuma suka nemi ya yafe musu.. Sai dai duk da sun koma gidansa, ko tsokar nama daya ba su gani ba, kuma ya yi musu haka ne don ya zama darasi a garesu.
Wannan labari yakamata ya zama ishara ga mata masu aikata ko niyyar aikata irin haka. Ya dace a rika sara ana duba bakin gatari musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki. Allah Ya kyauta.
Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883.