Yadda rashin wutar lantarki ya zame min alheri — Mai cajin waya

“Rayuwa ta kasance idan wani mutum yana kuka, wani kuma yana dariya ne”

Yadda rashin wutar lantarki ya zame min alheri — Mai cajin waya

Wani mai cajin wayar salula a Unguwar Rogo da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, ya ce rashin wutar lantarki da ake fama da shi a yankin arewacin ƙasar nan na ƙara haɓaka kasuwancinsa.

A halin yanzu dai yawancin Jihohin Arewacin Nijeriya suna fama da matsalar rashin wutar lantarki bayan katsewar manyan layukan samar da wutar lantarki suka yi da ke jihohin Benuwe da Enugu.

Auwal Bayya, wani mai sana’ar cajin waya a yankin, ya ce, “Rayuwa ta kasance idan wani mutum yana kuka, wani kuma yana dariya ne”, inda ya yarda cewa matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a halin yanzu tana bunƙasa sana’arsa.

Ya ce, “Rayuwa tana da ɗaci; hawayen wani abin dariya ne gari wani. Sai dai gaskiyar ɗaya ce, waɗanda ke shan wahala suna da yawa.

“Yanzu ina samun isassun kuɗi da nake ciyar da iyalina, ba kamar a da ba lokacin da mutane ba sa son su ba ni tallafi kan sana’ar da nake yi.

“Amma tunda aka fara rashin wutar lantarki, mutane na tururuwa a nan don yin cajin wayoyinsu.

“Ƙarin abokan ciniki yana nufin ƙarin shigowar kuɗi. Ina cajin wayoyi sama da ɗari kullum, da kwamfutocin tafi-da-gidanka, fitilu, da sauran kayan laturoni.

“Wani lokacin a dole nake ƙin karɓar cajin mutane saboda rashin sarari. Kamar yadda kuke gani, ko’ina cike yake da wayoyi.

“Ina ɗaya daga cikin waɗanda ke cin moriyar lamarin, amma ina tausaya wa ‘yan Nijeriya da ke kokawa game da lamarin rashin wutar.

“Babu abin da zan iya yi. Yanayin ne ya ba ni damar samun ƙarin kuɗi.

“Kar ku manta, ni ma ina siyan mai a farashi mai tsada. Duk abin da na samu, ina rabawa ne tare da gidajen mai,” in ji shi.

Sai dai Bayya ya buƙaci gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su gyara wutar lantarkin a yankunan da abin ya shafa, duk da ya zame min alheri.

Ya ce, “Ba za mu iya ci gaba da jin daɗi yayin da miliyoyin ke shan wahala ba.”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos