Yadda rasuwar fitaccen mawaƙi El-Mu’az ta girgiza Kannywood
A jiya Laraba ce Allah Ya yi wa fitaccen mawaƙi a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, El-Mu’az Muhammad Birniwa, rasuwa. Rahotanni sun bayyana cewa El-Mu’az ya rasu ne bayan ɗan ƙaramin aikin motsa jiki da ya saba a farkon daren ranar Laraba. Boko Haram: Fararen hula 10,000 sun mutu a hannun sojojin Najeriya — […]
A jiya Laraba ce Allah Ya yi wa fitaccen mawaƙi a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, El-Mu’az Muhammad Birniwa, rasuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa El-Mu’az ya rasu ne bayan ɗan ƙaramin aikin motsa jiki da ya saba a farkon daren ranar Laraba.
- Boko Haram: Fararen hula 10,000 sun mutu a hannun sojojin Najeriya — Amnesty
- ’Yan Majalisar Wakilai 6 sun sauya sheƙa zuwa APC
Jama’a da dama sun kaɗu da rasuwar mawaƙin musamman abokan hulɗarsa ganin cewa ana tare da shi har tsawon yinin ranar da zai rasu.
Bugu da ƙari, ‘yan awanni kaɗan gabanin rasuwarsa, El-Mu’az ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook, wanda hakan ya sa mutane da dama da suka bayyana alhini suka girgiza da mutuwar tasa.
Jaruman Kannywood da dama da sun bayyana alhininsu game da rasuwar mawaƙin da suka haɗa da Maryam Booth, da Bello Muhammad Bello wanda aka fi sani da General BMB inda suka bayyana saƙon ta’aziyyarsu a shafukansu na Facebook.
Sadiq Mafiya shi ma cewa ya yi: “Kullu nafsin za’iƙatul maut.
“Na daɗe ina gani kuma ina jin mutuwa kuma na san kowa da lokacinsa, amma ban taɓa jin mutuwa irin na ɗan uwa, abokin shawara, abokin arziƙi irin naka El Mu’az Birniwa.
“Fatana kawai Allah Ya jiƙanka da rahama Allah Ya gafarta maka, kai masoyin Annabi Muhammad SAW ne kowa ya shaida, kai mai taimakon na ƙasa da kai ne kowa ya shaida, ba ka da hassada…”
Har wa yau, daga cikin mutanen da suka kaɗu da rasuwar mawaƙin akwai Abba Faransa wanda a shafinsa na Facebook ya wallafa cewa,
“Innalillahi Innalillahi, wallahi ban san ka ba, amma na kaɗu da jin mutuwarka, awa bakwai da suka wuce 7 kana lafiya ba kasan ma ranar ce ranar ka ba. Lallai Allah ba ya sabon aiki.”
Kafin rasuwar haziƙin mawaƙin ya yi waƙoƙi da dama.
Marigayi El-Mu’az ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Birniwa ne ta Jihar Jigawa, wanda aka haife shi a Jihar Kaduna inda a nan ya taso kuma yake gudanar da harkokin rayuwarsa.