Yadda rayuwa ta kasance yanzu a Mubi

Bayan ‘yan bindiga sun kwace iko a garin Mubi da ke jihar Adamawa sai suka sauya wa garin suna zuwa ‘Madinatul Islam’ watau birnin musulunci, hakan ya sanya mutane da dama sun gudu daga garin, a yayin da wadansu kuma suka hakura suka zauna. Duk da cewa jami’an ‘yan sanda da sojoji sun yi alkawarin […]

Yadda rayuwa ta kasance yanzu a Mubi
Yadda rayuwa ta kasance yanzu a Mubi

Bayan ‘yan bindiga sun kwace iko a garin Mubi da ke jihar Adamawa sai suka sauya wa garin suna zuwa ‘Madinatul Islam’ watau birnin musulunci, hakan ya sanya mutane da dama sun gudu daga garin, a yayin da wadansu kuma suka hakura suka zauna.

Duk da cewa jami’an ‘yan sanda da sojoji sun yi alkawarin kwato garin daga hanun ‘yan bindiga, har yanzu ba a ga alamar haka ba.
Ruhotanni daga Mubi sun tabbatar da cewa ‘yan Boko Haram suna fasa gidaje da ma’ajiyar abinci su raba wa jama’ar garin abin da suka samu. Sukan kuma ce wa mutanen da ke garin sun ba su zabi, ko dai su tattara kayansu su bar garin ko kuma su tsaya a sabuwar garinsu ta Madinatul Islam, ko kuma su kona gidajensu.
Wadansu daga cikin mutanen garin Mubin sun ce sun yarda da kaddarar da ta fada musu, domin kuwa wannan wata jarabawa ce daga Allah. Kamar yadda wanin mai suna Malam Sani yake cewa, “ muna ji muna gani suke bari wuta ta ci mu, su ma tasu na jiransu, kuma wannan abu dai kaddara ce.”
Shi kuwa Thimoty Sam, wanda daya ne daga cikin wadanda suka gudu daga garin Mubi, bayyana wa manema labarai ya yi cewa, yanzu haka ‘yan Boko Haram da ke garin Mubi suna nan sanye da kayan sojoji a kan hanyar garin suna binciken masu wucewa, kuma sun ce kada a ji tsoronsu.
Wata budurwa ‘yar kimanin shekara 19 wanda ba ta son a fadi sunanta kuwa, cewa ta yi, “a lokacin da muke kokarin gudun hijira shi ne daya daga cikin ‘yan bindiga ya ce da ni in sauko daga motarmu, sai motar tamu ta tafi ta barni. Muna da yawa matan da suka kama, sai suka kai mu wani gida, suka ba mu abinci mai kyau, har da lemun kwalba. Daga nan sai daya daga cikinsu ya ce da mu za a aurar da mu. Ni dai na kasa cin komai don tsoro. Ana cikin hakan sai aka sako wani harsashi daga sama, ina ganin jirgin soja ne ya jeho shi. A wannan lokacin ne na saci jiki na gudo.”
Shi kuwa Malam Shehu cewa ya yi, yanzu dai komai lafiya a garin Mubi kuma ‘yan Boko Haram sun ce musu su ci gaba harkokin kasuwancinsu, sun ce za su kula da su, domin zama a birnin Musulunci ya fi kwanciyar hankali fiye da zama da sojoji a Nijeriya. Kuma mutanen garin na zaune lafiya.
Ya kara da cewa, ‘yan Boko Haram sun ce kada a kuskura a yi maganar wani abu mai suna zabe a garin, domin idan suka kama mutum za su san abin da za su yi da shi.
Wata majiya ta bayyana wa wakiliyarmu cewa, ‘yan Boko Haram din suna binciken duk wanda zai fita ko shiga garin Mubi, kuma motoci masu zaman kansu ne ake gani suna zirga-zirga, ba a cika ganin motocin haya ba.
A wani labarin kuma, wanijJirgin saman soja mai dauke da bindigogi da harsasai ya fado a kusa da sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) kusa da kauyen Damare, kilomita 8 daga Yola.
Jirgin ya fado ne da misalin karfe 9:30 na safiya a ranar litinin. A cikinsa akwai sojoji turawa guda 5 wadanda suka samu raunuka, amma ba su mutu ba.
Wata majiya da ta shafi tsaro ta bayyana cewa, jirgin na dauke ne da harsasai da bindigogi domin amfani das u wajen dakile hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa ajihar Adamawa.
Wani wanda ya ga yadda al’amarin ya faru mai suna Malam Baba Habu, ya bayyana cewa, “na fito daga gidana ina son zuwa unguwa sai na hangi jirgin daga sama yana tafiya kamar dai bai da koshin lafiya, kafin in ankara sai na ji wani babban kara. Na ki zuwa kusa da wajen sai da na ga daya daga cikin wadanda ke cikin jirgin ya fito neman taimako sanye da kakin soja, daga nan sai na kira wadansu mutane domin su agaza. Inda muka kwashe su muka kai si asibiti a cikin motata, amma mu tafi nag a wadansu sun zo sun kwashe harsasan da ke cikin jirgin day a fadi.’’
Aminiya ta so ta ji ta bakin manajan da ke kula da harkar jirage amma ya ki cewa komai.
An tsaurara matakan tsaro a wurin da jirgin nya fadi kuma an hana a kusanci wajen da kuma daukar hotor jirgin, sai dai da dabara, kuma an hana manema labarai zuwa asibitin da aka kai wadannan sojoji domin hira da su.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi