Yadda rayuwar Hausawa ta kasance a kasar Chadi
Halin rayuwar da suka zabar wa kansu, Hausawa ba mutane ne da suka gaji zama a wuri guda ba. Mutane ne da suke yawan tafiye-tafiye. Hakan na da nasaba da yadda suke rugumar sana’o’i daban-daban ba tare da kyashi ba.Sakamakon wannan ya sa suka yi fice a fannin kasuwanci da dama. Lamarin da ya sa […]
Halin rayuwar da suka zabar wa kansu, Hausawa ba mutane ne da suka gaji zama a wuri guda ba. Mutane ne da suke yawan tafiye-tafiye. Hakan na da nasaba da yadda suke rugumar sana’o’i daban-daban ba tare da kyashi ba.Sakamakon wannan ya sa suka yi fice a fannin kasuwanci da dama. Lamarin da ya sa suka kasa zama a wuri guda.
A irin tafiyar da suke yi, al’ummar Hausawa suna jerawa ne tare da al’adunsu wadanda suka hada da harshe da dabi’u da sauransu. Domin su kasance tsintsiya madaurinki daya al’ummar ta Hausawa na kafa wasu kungiyoyi da za su ba su damar cudanya da juna, tattauna matsalolin da suke addabarsu kamar na neman ilimin yaransu da sauransu. A kasar Chadi akwai kungiyar da ake kira “ASUSU” wadda take kokarin hada kan Hausawan kasar baki daya a karkashinta. Sai dai daga cikin ayyukan da kungiyar take gudanarwa, babu fannin kare dabi’u ko kuma al’adun gargajiya da aka san Hausawa da su, irin na bikin aure da haihuwa da kuma sanya sutura masamman ma na ’ya’ya mata.
A babban birnin kasar Chadi, N’Djamena babu maroka Hausawa wadanda suke yin fadanci a duk wani biki. Hakannan babu makadan kalangu wadanda suke cin kasuwarsu a duk sanda wani lamari mai faranta zukatun jama’a ya faru.
Har ila yau, raguwar martabar sarakunan Hausawa a wajen a kasar Hausa ita ma wata matsala ce. Akasari babu fadar da ake zama, inda sarki zai zauna da zarar ya karbi sarauta. Abu da aka saba gani, ka ga sarkin da aka nada ya mayar da gidansa fada.
Kuma darajar sarkin ba ta wuce ta uku, wadda ita ce daraja ta karshe da sarki kan a wannan zamanin nan. Wannan ba ya rasa nasaba da irin cudanyar da Hausawa suka yi a kasar Chadi da larabawan shuwa.
A yau wata babbar matsala da take ciwa samari tuwo a kwarya ita ce ta hada irin kayayyakin da ake bukata idan yana neman aure wato kayan lefe. Abin da ake fara tambayar duk wani saurayi mai neman auren burdurwa a tsakanin al’umar Hausawan shi ne zinare. Daga nan sai a fara maganar wasu makudan kudi da zai bai wa iyayen budurwar. Kudin za su iya haura miliyan biyu zuwa biyar 5 na kudin CFA, sakamakon darajar budurwar da yake nema.
Kodayake, da kudin ne iyayen za su sayi kayan lefe da kuma kayan kawata dakin ango da amarya. A bikin auren kuma a maimakon a yi rawar ta Malam Bahaushen da aka sani, amma sai ka ga “rawar disko”. Saboda irin wadannan dabi’u, yana da wuya a kasar Chadi mutum ya bambanta mace Bahaushiya da kuma Balarabiya ta bangaren sutura da wasu dabi’u.