Yadda rayuwar mutanen Najeriya ta bambanta da ta Kamaru
A ka®ro da dama na samun sabanin gudanawar wasu al’amurra a tsakanin al’umar kasa daya wani lokacin ma a cikin gari daya. A wani mataki mafi girma kuma shi ne yadda jama’a suke dinga tafiyar da rayuwarsu daga wannan kasa zuwa wancan a fannonin rayuwa daban-daban. Misali a cikin birane ba a yin “obalodi” wato […]
A ka®ro da dama na samun sabanin gudanawar wasu al’amurra a tsakanin al’umar kasa daya wani lokacin ma a cikin gari daya.
A wani mataki mafi girma kuma shi ne yadda jama’a suke dinga tafiyar da rayuwarsu daga wannan kasa zuwa wancan a fannonin rayuwa daban-daban. Misali a cikin birane ba a yin “obalodi” wato daukar fasinjoji fiye da kima a birnin Abuja, alhalin kuma sabanin haka ne yake a Kamaru.
Fasinjoji uku ne suke zama a kujerun baya na tasi-tasi, sa’annan kuma biyu ta gaba. Hakan ya sa akasarin mutane a Kamaru basa yar da su zauna a kujerar gaba domin sun san cewa gabannin su isa masauki za a iya kara wani fasinja a gaban mota wanda idan kuskura ne zai iya takura musu.
Sai dai kuma a inda aka samu dace wa wurin yin lodin fasinjojii a cikin mota a Kamaru da Najeriya shi ne idan motocin unguwannin bayan gari za su shiga a wannan lokacin ne ake yin obalodin fasinjoji a gaba da kuma bayan mota. Sa’annan kuma motar ba taa motsa wa sai har sai fasinjoji sun cika.
Wani bambancin da kuma ake gani a gidajen cin abinci shi ne a duk sanda mutum ya bayyana bukatar irin abinci da yake so ya ci kamar tuwon shinkafa da miyar kubewa wani lokacin kuma sai kuma a tambayeshi da yankan nama nawa? Irin wannan lamarin ba a dinga samunshi a gidajen cin abinci na Kamaru. A duk sanda aka ba wa mutum tuwo da ko wani irin miya tabbas akwai tsokan nama a ciki. Wato ba a yi wa tuwo da miya farashi daban, sa’annan kuma a yi wa nama farashi daban. Sai dai kuma yankar nama a Najeriya yana da girma fiye da na Kamaru. Duk da cewa kuma kudi da ake amfani da su a Kamaru da Najeriya sun bambanta, hakannan ma yadda aka lissafa kudi suka bambanta.
A yayin da Najeriya take amfani da kudin naira wadda ta karan kanta ne kawai ita kuma Kamaru tana amfani da kudin CFA tare da wasu makwabtarta da kuma wasu kasashen Yammacin Afirka. A Najeriya ana lissafa naira daga daya zuwa daya ma’ana ana cewa Naira daya, biyu , uku har sama.
A Kamaru kuma da sauran kasashen da suke amfani da CFA, ana lissafa kudin ne daga biyar zuwa biyar misali CFA 5, CFA 10, CFA 15 har zuwa sama amma kuma idan za a furta CFA 5 ana kiranshi dala daya (1), CFA 10 dala biyu (2), CFA 15 dala uku (3) wannan a hausance kenan da kuma a sauran yarurrukan Kamaru. CFA 500 ana cewa da ita dala dari (100). Amma kuma idan lissafi ya kai dubu daya (1,000) ana cewa da hausa jaka daya (1). Saboda haka 10,000 jaka goma ke nan.
A kasar Chadi kuma inda suma kudin CFA suke amfani da shi, a can ma yadda ake lissafin kudin da sauran kasashen ya bambanta. A yayin da a Kamaru CFA 5,000 ana furtashi jaka biyar su kuma a Chadi suna cewa dubu daya (1,000) wato anan sun danganta lissafin kudin da na Riyal wato kasar Sa’udiyya wadda itama kamar Naira ana lisaafata daga daya zuwa daya ne. Kenan a yarensu na Hausa babu batun jaka a ciki face dubu kawai.
Saboda haka CFA 12,000 da za a furtashi akan jaka goma sha biyu. A chadi kuma za a ce dubu biyu da dari hudu (2,400). kasashen da suke furta lissafin kudi kamar Kamaru sun hada da Gabon, Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Ekuatorial Guinea da kuma Congo a hausance ke nan. Kodayake, yadda ake gane matar Bahaushiyar Kamaru ta fanni sanya sutura shi ne za a ga cewa dan kwallin kanta da kuma atamfar da ta daura da wanda ta rufa a kanta dukkansu samfuri daya ne wato idan ta sayi atamfa guda mai yadi shida tana rabashi gida uku yadi biyu ta sanyashi akanta , yadi biyu ta daura shi sauran yaduka biyun.
Kuma ta dinka riga da shi ta kuma fidda dan kwali a ciki. Sai dai kuma ana dinga samun matsala matukar har idan matar ba ta da rama. A wannan lokacin yana kasancewa kawai tana yin amfani ne da yaduka biyu wurin dinka rigar da za ta sa abin da ya rage kuma ta yi adiko da shi. Sa’annan kuma ta nemi wani mayafi ko gyale ta rufa shi akanta. Irin yadda ake gane mata a Najeriya ke nan, wato wadanda suke dinga bambanta atamfofin da suke sanya wa a lokaci guda.