Yadda rikicin Filato ya cutar da manoman dankalin Turawa
Abara manoman dankalin Turawa a Jihar Filato, sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon rikice-rikicen manoma da makiyaya da aka yi fama da su a Karamar Hukumar Bokkos da ke jihar, a watan Yulin shekarar. Yankin na Bokkos shi ne kan gaba wajen noman dankalin Turawa a Najeriya. Kuma dubban manoma daga kauyuka 10 na yankin […]
Abara manoman dankalin Turawa a Jihar Filato, sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon rikice-rikicen manoma da makiyaya da aka yi fama da su a Karamar Hukumar Bokkos da ke jihar, a watan Yulin shekarar.
Yankin na Bokkos shi ne kan gaba wajen noman dankalin Turawa a Najeriya. Kuma dubban manoma daga kauyuka 10 na yankin wadanda suka yi suna wajen noman dankalin ne suka yi gudun hijira suka bar kayan amfanin gonar da suka shuka, zuwa wasu sassa sakamakon rikice-rikicen.
Bayan haka manoman dankalin sun fuskanci matsalolin cututtukan dankali Turawa a jihar barar.Wadannan matsaloli da manoman dankali suka fuskanta, sun yi sanadin tashin farashin dankali, inda sai da buhun dankalin mai nauyin kilo 50, ya kai Naira dubu 17.
Mista Solomon Michael Arandong wani manomin a yankin Bokkos da yanzu ya dawo madatsar ruwa ta Lamingo da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa yana noma, ya ce ya rasa dukkan kayayyakin amfanin gonar da ya noma a yankin Bokkos, sakamakon rikice-rikicen.
Ya ce, akalla ya yi asarar Naira dubu 700 na dankalin Turawan da ya noma a yankin Bokkos. Ya ce, yanzu ba ya da karfin da zai yi noma mai yawa, sakamakon wannan babbar asara da ya yi, don haka ya dawo madatsar ruwa ta Lamingo ya samu karamar gona ya fara nomawa.
Misis Magdalene Habila wata mai noman dankalin Turawa a madatsar ruwan ta Lamingo, ta ce ta sayi buhunan irin dankalin Turawa 64, kan Naira dubu 16 a kowane buhu a bara don shukawa a bana.
Ta ce ta kashe Naira miliyan 2 da dubu 300 a gonar da take nomawa bisa fatar ta samu riba.
“Irin dankalin Turawa ya yi matukar tsada a bara, saboda rikice- rikicen da aka samu a kauyukan yankin Bokkos, yankin da ya yi fice a noman dankali. Don haka manoman yankin ba su samu damar hake dankalin da suka shuka ba.Wannan ya sa irin dankalin Turawan ya yi tsada a bana,” inji ta.
Ta ce a bara manoma da dama ba su samu damar girba ko hake kayayyakin amfanin gonar da suka shuka ba a kauyuka yankin Bokkos saboda rikice-rikicen manoma da Fulani makiyaya da aka yi fama da su. Kuma wadansu manoman sun rasa kayayyakin amfanin gonar da suka noma, sakamakon cututtukan da suka auka wa kayayyakin.
Ibrahim Umar wani mai sayen dankalin Turawa ne a yankin Bokkos da Mangu da Lamingo da Bassa da ke Jihar Filato tare da safararsa zuwa garuruwan Abuja da Legas da Fatakwal. Ya ce a yanzu ana sayar da buhun irin dankali da ake shigowa da shi daga waje, mai nauyin kilo 50 a kan Naira dubu 30.
“Tsadar da irin dankalin Turawa ya yi a bara, ba ita za ta sanya farashin dankalin ya tashi ba a bana. Bukatar dankalin ne za ta sanya farashinsa ya tashi. Amma idan bukatarsa ta yi kasa, farashinsa zai iya faduwa kasa a bana,” inji shi.
Ibrahim Umar ya ce dankalin Turawan da ya fi kowanne kyau a Najeriya shi ne dankalin da ake nomawa a yankin Bokkos da ke Jihar Filato. Don haka gidajen dafa abinci da dama a Najeriya suke sayen wannan dankali.
“Babu shakka a bara dankali ya yi karanci, don haka na rika bin kauyuka, ina bin manoma gonakinsu, don in samu dankalin da zan sayarwa da abokan cinikina’,’ inji shi.
Mista Geoffrey Mador cewa ya yi dama an saba dankalin Turawa ya fi tsada da rani, wato a watannin Afrilu da Mayu da Yuli. Domin mafiya yawan manoman dankalin sun fi yin noman ne a lokacin damina.
Ya ce, don haka manoman suke barin noma har sai lokacin ruwan damina ya zo.
Ganin irin yadda noman dankalin Turawan yake samar da ayyukan yi ga matasa, tare da samar da kudaden shiga ga Gwamnatin Jihar Filato, manoman dankalin sun bukaci gwamnati ta gina musu madatsun ruwa tare da samar musu da ingantaccen iri na zamani da ba su rancen kudade, domin su bunkasa wannan noma da suke yi.