‘Yadda rikicin Kafanchan ya mayar da ni nakasasshe’
Wani matashi da kimanin shekara 27 mai suna Mohammed Isma’ila da ya tsallake rijiya da baya a rikicin da aka yi a Kafanchan da ke Jihar Kaduna a shekarar 2011, ya ce rikicin ne ya mayar da shi nakasasshe. Mohammed Isma’il ya bayyana wa Aminya cewa: “Lokacin da ake rikicin cikin dare sai abokan gaba […]

Wani matashi da kimanin shekara 27 mai suna Mohammed Isma’ila da ya tsallake rijiya da baya a rikicin da aka yi a Kafanchan da ke Jihar Kaduna a shekarar 2011, ya ce rikicin ne ya mayar da shi nakasasshe.
Mohammed Isma’il ya bayyana wa Aminya cewa: “Lokacin da ake rikicin cikin dare sai abokan gaba suka zo da kayan fada, duk cikinmu babu mai wuka balle bindiga, hakan ya sa suka fara karkashe mu kamar kiyashi. Ni da mahaifina da sauran ’yan uwana muna cikin gida, sai suka shigo suka rika kashe duk wanda suka gani, sannan suka banka wa gidan wuta. Ina labe ina kallo Babana yana konewa, kuma haka na daure kafafuna na yi cikin wuta ina kokarin janye su daga wutar amma na kasa,” inji shi. Ya ce, bayan da kura ta lafa ne masu taimako tare da jami’an tsaro suka dauke shi da sauran masu rauni zuwa asibiti.
“In takaita maka sanadiyar rikicin Kafanchan na rasa kowa a dangina, yanzu haka babu wani jinina da na sani. Da na samu sauki ne na tafi wurin wani abokina a Kucigoro da ke Abuja. Kuma saboda abokina ba mai karfi ba ne da kyar nake samun kyalle ko audugar da zan wanke mikin kafafun, sai bana bayan shekara biyar kafar ta fara warkewa amma wani sashi na azabtar da ni har wani lokaci sai in gwammace dama na mutu ne in huta,” inji shi.