Yadda rikicin Mile 12 ya hargitsa al’umma a Legas

A makon jiya ne rikicin da ake danganta shi da kabilanci ya kaure a unguwar Mile 12 Legas, tsakanin wasu ’yan Arewa masu sana’ar tukin babur, wadanda aka fi sani da ’yan acaba da wasu Yarabawa ’yan-zauna-gari-banza, wadanda ake kira da ‘Abero’ ko Eriya Boyis. ‘Alhaji Dauda Tarai, shugaba ne a bangaren kayan gwari a […]

Yadda rikicin Mile 12 ya hargitsa al’umma a Legas
Yadda rikicin Mile 12 ya hargitsa al’umma a Legas

A makon jiya ne rikicin da ake danganta shi da kabilanci ya kaure a unguwar Mile 12 Legas, tsakanin wasu ’yan Arewa masu sana’ar tukin babur, wadanda aka fi sani da ’yan acaba da wasu Yarabawa ’yan-zauna-gari-banza, wadanda ake kira da ‘Abero’ ko Eriya Boyis. ‘
Alhaji Dauda Tarai, shugaba ne a bangaren kayan gwari a kasuwar, ya shaida wa Aminiya cewa rikicin ba a kasuwar Mile 12 aka yi ba, kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka yi ta yayatawa. Domin a cewarsa: “Akwai bangaren cikin garin mile 12 kana akwai kasuwar a bangare guda kuma rikicin ya samo asali ne a can cikin garin, a gefen gadar Ajiliki, tsakanin ’yan acaba ’yan Arewa da wasu matasan Yarabawa ’yan-zauna-gari-banza, a lokacin da wani dan acaba dan asalin yankin Gwoza ta Jihar Borno ya biyo hannu guda na hanya, ya buge wata mata. Bayan da ya tsaya yana lallashinta, yana share mata kasar jikinta sai wani matashi Bayarabe ya fara kai masa duka, yana kururuwar cewa ya za a yi ya buge masa uwa ya biyo hannun da ba nasa ba?
Nan fa matasan Yarabawan suka yi ta jibgar dan acaban nan, inda su kuma abokan sana’arsa suka fara yin cincirindo a wajen, kamar yadda da ’yan acaba sukan yi in an taba nasu. Nan fa sa’insa ta kaure, suka fara ba-ta-kashi tun daga ranar Talatar makon jiya.
“Tun daga nan sai mutane suka fara yada jita-jita, ana cewa fadan ya zama na kabilanci, ana cewa ma ai an kashe wannan dan acaba, ana kuma buge duk wani Bahaushe, ana kashe shi. Nan fa sai su ma ’yan Arewa suka yi shirin daukar fansa da kare kansu bayan kwana uku da fara rikicin, wato ranar Alhamis ke nan da abin ya fara kazanta. Jami’an tsaro sun yi iya bakin kokarinsu na hana ko wane bangare ya kai ga abokin karawarsa, sai dai daga bisani bangarorin guda biyu sun bi ta bayan fagge suka abkawa junansu. To ta haka abin ya faru.” Inji shi.
Ya kara da cewa, da fari an yi ta baza jita-jita, ana cewa wai ana shiga makarantu ana yanka yaran Hausawa, wanda abin ba haka ba ne; domin shi ma yana da ’ya’ya 6 a makarantar kuma dukkaninsu an kawo su gida bayan da shugabar makarantar ta ba shi tabbacin yaran suna cikin koshin lafiya. Dangane da adadin rayukan da aka rasa kuwa, ya ce ya ga gawar mutum biyu ne a can unguwar da rikicin ya taso kuma a kididdigar da aka bayar a nan, cewa mutum 3 ne suka rasa rayukansu. An kuma tabka mumunnar asara a sakamakon rikicin, domin an yi kone-konen gidaje, an kuma fasa wa mutane rumfunansu, an yi musu sata kana an kone motocin J5 na  dakon kayan abinci guda bakwai; kana jami’an tsaro suka kame fiye da mutane 50 a lokacin rikicin.

Masarautar Agege ta yi taron gaugawa
Kwana biyu da ruruwar rikicin mile 12, Masarautar Agege ta yi taron zaman lafiya na gaugawa, domin kare yaduwar rikicin, inda ta gayyato masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro; wadanda suka hada da daukacin hakimai da masu anguwannin Agege da sarakunan Yarabawan yankin da manyan hafsoshin soji da jami’an kula da shiga da fice da jami’an tsaro na farin kaya, wadanda suka yi wa mahalarta taron bitar zaman lafiya.
Kakakin majalisar masarautar Agege, Alhaji Muhammadu Kabir Ali Dinar, Hakimin Arewa, ya shaida wa Aminiya cewa, taron da masarautar ta yi yana da dangantaka da tsaro saboda matsalar da ta taso a Mile 12. Don haka ne suka yi hobasar tunasar da jama’arsu mahinmancin zaman lafiya, domin kare yaduwar rikicin.
Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Musa Muhammadu Dogonkadai ya shaida wa Aminiya cewa al’ummar Legas al’umma ce guda: “Domin da Bayaraben da ya zo daga Ondo da wanda ya zo daga Saki da wanda ya zo daga Abekuta, dukkaninmu daya ne. Kana ba mu da wani gari da ya wuce nan kuma abin da muke bukata a junanmu shi ne zaman lafiya. Shi ko ba ya faruwa sai an yi hakuri, idan aka yi hakuri da juna za a fahimci juna, idan aka fahimci juna za a sami zaman lafiya, idan aka sami zaman lafiya za a sami ci gaba; idan aka sami ci gaba arziki zai zauna da gindinsa, ya zama abin da ake cewa turken kasa mai wuyar cirewa.”
Sarkin ya yaba wa Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode bisa kwararan matakan da ya dauka tun bayan barkewar rikicin. Ya kuma nuna jin dadinsa bisa bayanan da gwamnan ya yi, inda ya nuna cewa Jihar Legas gari ne na kowa kuma babu wata kabila da za ta bugi kirji ta ce nata ne ita kadai, domin kowa ka gani a Legas zuwa ya yi.
A nasu bangaren, Sarkin Hausawan Legas, Alhaji Aminu Yaro Dogara da Sarkin Fulanin jihar, Alhaji Muhammadu Bambado tare da tawagarsu, sun kai ziyarar jaje ga mutanen garin Mile 12, a inda suka yi wa jama’a jawaban kwantar da hankula suka kuma jadadda aniyarsu ta ganin an samu dawwamammen zaman lafiya. daruruwan matasan kasuwar Mile 12 ne suka kewaye Sarki Aminu, a lokacin da yake yi musu nasiha da gargardin a zauna lafiya; yana cewa da harshen Yarabanci ‘Eko ko ni baje’ matasan na maimaitawa cikin raha. Wato ma’ana, ‘Legas ba za ta tabe ba.’
 
Gwamnan Legas Ya Kai Ziyarar Gani Da Ido
Jim kadan da tafiyar tawagar sarkin Legas, Alhaji Aminu Dogara sai tawagar Gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode ta karaso; kodayake gwamnan bai ce uffan ba a lokacin wannan ziyarar, inda ya je can ciki unguwar da rikicin ya faru, ya kuma gane wa idanunsa irin barnar da aka yi.
Tun da farko dai shuwagabannin kasuwar Mile 12 din sun sanya ran zuwan gwamnan, domin ya ba da umarnin bude kasuwar bayan an yi kwanaki uku da rufe ta, matakin da ya janyo musu bakar asara. Sai dai ko da gwamnan ya zo bai ko tsaya a kasuwar ba, abin da ya sanya da yawa daga cikin ’yan kasuwar nuna rashin jin dadinsu.

An tabka asara a saboda rufe kasuwar Mile 12
Kadan daga cikin matakan da Gwamnan Jihar Legas ya dauka don kwantar da tarzomar shi ne, rufe katafariyar kasuwar Mile 12. Ya kuma yi wa jama’ar jihar jawabi mai ratsa jiki, a inda ya fayyace cewa Legas gari ne na kowa domin kowa ka gani zuwa ya yi, don haka babu wanda zai bugi kirji ya ce garinsa ne da nufin uzura wa abokin zamansa. Wannan jawabi ya faranta wa jama’a da dama musanmman ma ’yan Arewa rai, sai dai matakan da gwamnan ya dauka na rufe kasuwar ya kuntata wa jama’a, ya kuma janyo masu tabka mummunar asara. Shugaban Kasuwar ta Mile 12, Alhaji Haruna Muhammad ya jajanta wa jama’a a kan abubuwan da suka faru, ya kuma yi ta’aziyyar rashin da aka yi, kana ya koka ga asarar da suka yi a kasuwar, wadda ya ce ta miliyoyin Naira ce. A cewarsa, mafi akasarin kayayyakin kasuwar nasu kayan gwari ne, wadanda ba su da jimirin ajiya, hakan ne ya sa da aka rufe kasuwar suka tafka kazamar asara. Domin kayan da aka turo daga Arewa babu damar saukewa, na cikin kasuwar kuma babu damar a fidda su a sayar.
“Kan haka, duk kayan suka salwanta, suka tsiyaye fiye da mota 60, ba abun da za mu iya yi sai dai mu rungumi kaddara.  Rikicin ba a kasuwarmu aka yi ba amma duk abin da ya shafi ido hanci zai yi ruwa, hakan ya sanya aka rufe mana kasuwa. Mun tabka asara, mutane da dama sun rasa hanyar samun abin kai wa bakin salati. Fatanmu shi ne, gwamnati ta dubi Allah ta dubi Annabi a bude mana kasuwarmu, mu ci gaba da harkokinmu.” Inji shugaban kasuwar, wanda ya ce da an tunkari tarzomar a lokacin da ya kamata, da rikicin bai kai ga haka ba. Domin a cewarsa, tuni suka yi ta kai koke kafin lamarin ya kazanta amma sai gwamnati ta yi ta jan kafa wajen daukar matakan da suka dace. Ya ce sun dade suna ta ankarar da gwmnatin bisa sanya idanu a kan ayyukan bata-garin yankin da rikicin ya taso amma sai aka yi kunnen uwar shegu. A karshe ya yi kira ga daukacin jama’ar Mile 12 da su zauna lafiya.

Rikicin mile 12 ba na kabilanci ba ne
Uwar kasuwar Mile 12 da aka fi sani da ‘Iya Loja’ Alhaja Iyabo Hamid, ta shaida wa Aminiya cewa su a kasuwar lafiya lau suke zaune da juna kuma babu fada tsakanin Hausawa da Yarabawa, domin kuwa tare suke gudanar da kasuwancinsu cikin fahimtar juna da mutunta juna. “Ba Yarabawa da Hausawa suke fada ba, kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke ta yayatawa. Ai ga shi kun ganmu tare muke ta fadi tashi, fadan tsakanin wasu tsagerun matasan Yarabawa ne marasa ayyukan yi da masu sana’ar acaba, wadanda mafi yawancinsu ’yan Arewa ne. Mu ba ruwanmu da wannan rigimar, don haka fatanmu gwamnati ta bude mana kasuwarmu, mu ci gaba da harkokinmu.” Inji Iya Loja.

A hana sana’ar acaba don magance rikicin
Duba da yadda ake danganta wannan tarzoma da ’yan acaba da wasu matasan Yarabawa ’yan-zauna-gari-banza, wakilin Sarkin Nufawan Mile 12, Alhaji Abdu Jibrin Magaji, ya yi kira da a hana sana’ar acaba a unguwar Mile 12, domin a cewarsa hakan ne kawai zai magance wannan matsalar. “Sau tari za ka ga matasa daga Arewa suna zuwa suna kwasar shara suna sana’ar acaba a Legas, sun bar gida sun ki noma. Muddin aka hana acaba, matasan za su koma gida su yi noma, su taimaka wa gwamnati a kokarinta na bunkasa noma. Mafi yawancinsu ’yan shaye-shaye ne, to ta yaya ba za su dinga tada fitina ba?”  Inji shi.
A nata bangaren, Hajiya Halima, wacce daya ce daga cikin jagororin matan unguwar mile 12, ta soki kiraye-kirayen da wasu ke yi na a soke sana’ar acaba a yankin, domin a cewarta duk wani matashi dan Arewa da ka gani a yankin, yana da sana’a komai kankantarta; wanda hakan ba zai ba su damar tada zaune tsaye ba, domin sun san nema suka fito. Ta ce hanyar magance wannan matsalar ita ce sama wa wadannan matasan Yarabawa ’yan-zauna-gari-banza aikin yi. Ta kuma koka da yadda aka kame masu ’ya’yansu, wadanda ba su ji ba ba su gani ba a rikicin. Domin a cewarta, akwai mutumin da aka kame shi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa masallaci, kwanaki hudu da fara tarzomar. Ta koka da halin da suke ciki sakamakon rikicin. “A nan makwabcinmu ya kwanta rashin lafiya sai a baro muka kai shi asibiti saboda babu masu acaba, hakan ne ya sanya ya rasu saboda jinkirin da aka samu.  Ba ma a iya binne shi ba a wannan ranar saboda makabartar tamu na can cikin unguwar da rikicin ya taso sai da muka bari gari ya waye aka dauki gawar aka kai ta can Ikorodu, a can aka yi mata sutura.
“Wannan masifar da yawa take, daruruwan matasan ne suka yi hijira suka koma Arewa, duk a saboda rikicin, haka suka yi ta biyan 5000 ana daukarsu da baburansu ana kai su Arewa a manyan motoci. Wadanda ba su da kudi kuwa suka hau baburan suka tafi Arewa. Akan haka ne mutum hudu a cikinsu suka yi hadari a Birnin Gwari suka mutu nan take, hakazalika akwai mutum biyu da suka yi goyo a babur suka yi hijira, su ma a tsakanin garin Bode, Sa’adu a Neja suka ci karo da babbar mota suka mutu nan take. Dukkaninsu mun sansu, a nan muke tare da su. Wannan ita ce masifar da wannan rikici ya janyo, fatanmu shi ne Allah Ya kawo mana sauki.” Inji Hajiya Halima.