Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari

An taɓa kulle masallacin ne tun a lokacin anobbar Korona, bayan barkewar wani rikici.

Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari

A bayan nan ne mahukunta a Ƙaramar Hukumar Agege, a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙaramar Hukumar Agege, Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi suka kulle babban masallacin Hausawa na garin, biyo bayan wani rikici da ke da alaƙa da na limanci ya ɓarke a masallacin a ranar Juma’a makon jiya.

Rikicin na zuwa ne bayan rasuwar babban limamin garin Agege, Shaikh Sharif Habib Abdul-Majid, wanda ya rasu kwanaki biyu gabanin aukuwar lamarin.

A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na zamani, an ga masallata a cikin masallacin suna kai wa junansu duka, wadanda suka haɗar da ɓangarori uku.

Waɗanda suka bai wa hammatar iska sun haɗa da ɓangaren gidan limamin da ya rasu da magoya bayansu da kuma ɓangaren gidan Na’ibinsa tare da magoya bayansu, waɗanda ke fatan Na’ibin ya zama limamin gari sai kuma ɓangaren Masarautar Agege da magoya bayan masarautar.

Shaikh Mahmud Shafi’i, Baba Addini na ‘yan Arewa mazauna Legas wanda yake ɓangaren da ke fafutukar ganin Shaikh Mustapha Imam Mukhtar ya zama limamin garin Agege, domin a cewarsa shi ne Na’ibi ya shaida wa Aminiya cewa, a kan idonsa rikicin masallacin ya ɓarke a ranar Juma’a.

Ya ce bayan da Na’ibin masallacin ya shigo zai hau mumbari ne sai magoya bayan ɗan limamin masallacin da aka tanadar tare da wasu ‘yan agaji da suka hana shi hawa mumbari nan da nan kuma aka shigo da ɗan limamin da ya rasu shaikh Sharif Isma’il Habib, wanda ya ba da sallah a lokacin da ake tsaka da hayaniya.

Mustapha Imam Mukhtar ya ƙara da cewa, “an taɓa kulle masallacin ne tun a lokacin anobbar Korona, bayan barkewar wani rikici.

“Amma a wancan lokacin an cim ma yarjejeniya bayan wani zaman sulhu da sasanci da majalisar jihar ta yi da ɓangarorin da al’amarin ya shafa, inda aka cim ma daidaiton cewa, Marigayi Shaikh Sharif Habib shi ne limamin masallacin.

“Sai kuma Shaikh Mustapha Imam Mukhtar da aka tabbatar Na’ibi, kuma aka ce ba zai yiwu ɗansa ya zama Na’ibi ba, domin ba zai yiwu ba yana limanci ɗansa kuma Na’ibi ba, wanda a kan wannan yarjejeniya ake, don haka tunda liman ya rasu a ka’ida Na’ibinsa ne zai zama limamin gari, ya ci gaba da bada salla, sai dai abun takaici ne abun da ke faruwa a yanzu,” in ji shi.

Aminiya ta tuntuɓi magatakardar Masarautar Agege, Alhaji Abubakar Ali Na’ibi, wanda ya ce duk garin da ke samun ci gaba da bunƙasa ba a raba shi da irin wannan rigingimu.

Ya ce, Masarautar Agege ita ke da alhakin gudanar da al’amuran babban masallacin garin.

“Wannan al’ada haka take a ko’ina a kasar Hausa, babban masallacin gari yana ƙarƙashin kulawar masarauta ce, kuma haka abun yake a garin Agege tun fil azal, kuma Masarautar Agege ɗan marigayi limamin gari, Shaikh Sharif Isma’il Habib ta sani a matsayin Na’ibi, shi ne wanda ta naɗa Na’ibi tun da daɗewa, kuma shi ne ta sani ni a matsayin limamin gari,” in ji shi.

A wata sanarwa da Shugaban Karamar Hukumar Agege ya fitar a shafinsa na kafafen sada zumunta na zamani ya ce, matakin rufe masallacin ya zama tilas domin kare afkuwar rikici, inda ya shaida cewa, zai gayyato dukkanin ɓangarorin da ke rikici domin a zauna a teburin sulhu.

 

Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi

Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari

Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2

An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda