‘Yadda rikicin ‘yan Acaba da sojoji ya kai ni gadon asibiti’
Wani tashin hankali da ya auku a garin Karu da ke Yankin Birnin Tarayya, Abuja a ranar Lahadin da ta gabata, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu da jawo raunuka, ga mutane da dama baya ga asarar dukiya, kamar yadda shaidu suka tabbatar wa Aminiya. Wani da tashin hankalin ya faru a gabnsa mai suna […]

Wani tashin hankali da ya auku a garin Karu da ke Yankin Birnin Tarayya, Abuja a ranar Lahadin da ta gabata, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu da jawo raunuka, ga mutane da dama baya ga asarar dukiya, kamar yadda shaidu suka tabbatar wa Aminiya.
Wani da tashin hankalin ya faru a gabnsa mai suna Jabiru Salisu, ya shaida wa wakilinmu cewa, al’amarin ya faro ne sakamakon mutuwar wani dan acaba a kusa da wani coci mai suna Saint Mary Catholic Church da ke Karu.
Aminiya ta samu labarin cewa, dan acaban ya dauki wata mace ce zuwa cocin, kuma ya so ya saukar da ita nesa da sojojin da ke tsaron cocin duk ranar Lahadi, amma sai matar ta ce ita mamba ce a cocin, ba wata matsala. Majiyarmu ta ce sauke ta ke da wuya, sai wata soja ta sanya shi tsallen kwado da sauran gwale-gwale iri-iri, kuma da ta kula ya gaji tibis sai ta ce ya sha ruwan wani kwata, amma ya shaida mata cewa yana azumi. Sojar ta nace sai dai ya sha ruwan kwatan kuma yana sha ba a jima ba sai ya rasu nan take.
Majiyar ta ce ganin haka ne, sai wa su ’yan acaba da suke kallon abin da ke faruwa da shi, suka yi gangami suka kaddamar da zanga-zanga suna auka wa motocin da da ke bi ta wurin tare da killace hanyar.
Wakilinmu ya samu labarin cewa ’yan sanda da aka tura wurin da sojoji suke don shawo kan matsalar, sun tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar bude musu wuta, inda a dalilin haka suka kashe mutum na biyu, bayan da harsashinsu ya same shi. Haka nan kuma akwai wani matashi da harsashin ya yi wa rauni a kafafunsa biyu da ke kwance a Babban Asibitin kasa da ke Abuja.
Matashin mai suna Huzaifa Abdullahi wanda wakilinmu ya ishe a gadonsa na asibitin, ya ce bai jima da zuwa Abuja ba daga kauyensu Gwamlar da ke karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Ya ce ya gamu da wannan kaddara ce a lokacin da ya zo wani masallaci da bai da nisa da wurin.
Huzaifa mai shekara 22, ya ce bayan idar da Sallah a masallacin yana shirin fita don tafiya wurin harkokinsa, sai kawai ya ji harsashi a sawayensa, ya ce bayan tsawon lokaci, sojoji sun dauke shi zuwa Asibitocin Karu da na Asokoro da kuma wani Asibitin da bai rike sunansa ba, amma ba a karbe shi ba.
Ya ce bayan sun zo Asibitin kasa ne, sai sojojin suka a jiye shi a wuri suka kama gabansu.
A ganawarsa da wakilinmu, wani dan uwan majinyacin mai suna Tijjani Mubarak, ya ce sun gano yana asibitin ne bayan ya yi musu waya a safiyar Litinin. Kuma ya ce suna zuwa sai jami’an asibitin suka gabatar musu da takardar adadin kudin da aka kashe a kansa na Naira dubu 35.
Mubarak ya ce jami’an asibitin sun shaida musu cewa, sojojin da suka kawo shi ba su yi wa kowa magana ba suka ajiye shi suka tafi. Ya ce suna kokarin su ga ta yadda za su hada kudin da wasu kari don ci gaba da kulawa da shi.
A wata sabuwa kuma, mutanen da ke sana’o’i a kusa da inda zanga-zangar ta wakana, sun bayyana wa Aminiya yadda suka kubuta. Wani da ke sayyar da kayan marmari a kusa da masallacin da harsashi ya samu Huzaifa, mai suna Hamza Subsidi, ya ce, suna zaune a kusa da masallacin su kusan 20 lokacin da suka ji jiniyar ’yan sanda ta dumfari cocin. Ya ce a lokacin ne kowa ya tsere don gudun abin da ka iya biyowa baya. Subsidi ya ce daga nesa inda suka tsaya sun rika hango yadda ’yan sanda ke ta harba bindiga don tarwatsa masu zanga-zangar.
Wani mai kemis a kusa da wurin mai suna Adeyemi Elaija bayyana mamakinsa ya yi a kan yadda ya ishe shagonsu da hujin harsasai. Ya ce Allah Ya taimake su kasancewar a ranar Lahadi ba sa bude shago sai da maraice, inda ya ce watakila da harsashi ya daya daga cikinsu kasancewar daya daga cikin harsasan da ya shiga shagon bayan huda gilashin kofarsa, ya nufi ta bangaren da wata jami’ar karbar kudi ke zama ne. Haka kuma ya nuna inda harsasai suka huda kwandon sharar shagon da gininsa.
Wani jagoran al’umma a garin Karu, Alhaji Isma’ila Musa Madakin Sarkin Hausawan Karu, ya yi Allah wadai da zanga-zangar da ’yan acaban suka yi, kuma ya yi kira ga sojoji, wadanda a duk ranakun Lahadi ke aikin tsaro a majami’un Redeem Christian Church da Saint Mary Church da ke kan Titin Jikwoy su maida hankalinsu ga tsaron mujami’un, tare da barin abin da ya shafi hulda da jama’a ga ’yan sanda. Ya ce tilasta wa dan Adam shan ruwan kwatami musamman ga wanda yake azumi, al’amari ne da ya saba wa kowane irin tunani.
Tuni dai al’amura suka koma yadda suke a yankin, yayin da jami’an tsaro ke zaman dirshen a harabar cocin wanda ke daura da wurin Sallar idi na Karu.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, DSP Hyelira Altine Daniel, ta shaida wa Aminiya cewa rundunarsu ba ta da masaniya a kan mutuwa ko raunuka a yayin zanga-zangar. Ta ce tashin hankalin a tsakanin sojoji ne da ’yan acaba, kuma ’yan sanda sun shigo ciki ne domin dawo da zaman lafiya a yankin.
Da a ka tuntube shi a kan al’amarin, babban jami’in hulda da manema labarai na Rundunar Tsaron Fadar Shugaban kasa (Guard of Brigade), Kanar Aderati, cewa ya yi, sai ya sami izini daga na gabansa kafin ya yi magana a kai.