Yadda rufe Dam ɗin Balanga ya talauta manoman rani

Na yi aikin noman ban ruwa sama da shekara 30 a Balanga.

Yadda rufe Dam ɗin Balanga ya talauta manoman rani

An kafa madatsar ruwa ta Balanga ce tun a shekarun 1980s don samar da hanyoyin rayuwa da samar da tsaro ga ayyukan yi.

Sai dai kuma rufe madatsar ruwan da Gwamnatin Jihar Gombe ta yi shekara biyar da suka gabata ya jefa al’ummar yankin cikin mawuyacin hali, kamar yadda wakilinmu ya ruwaito mana.

Dam din Balanga da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, Gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ce ta gina shi domin samar da ababen more rayuwa ta hanyar noman shinkafa da kamun kifi ga dubban mazauna yankin da sauransu.

Baya ga ayyukan ban ruwa da kamun kifi, Dam din na da ƙarfin samar da wutar lantarki.

Tsawon shekaru, Dam din ya kasance tushen samar da ayyukan yi ga dubban mutane a fadin jihar, har da ma wasu jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Dubban matasa ne suka tsunduma ko dai a matsayin leburori ko kuma manoma don yin noma a lokacin damina, inda suka samar da tan mai yawa na shinkafa, wanda hakan ya taimaka wajen samar da abinci a ƙasar.

A lokacin da madatsar ruwan ke aiki, tsakanin shekarar 1984 zuwa 2019, dubban mutane ne suka zuwa Balanga domin noman rani, wanda hakan ya inganta tattalin arzikinsu da na al’umma.

Sai dai tun a shekarar 2019, da gwamnati ta rufe madatsar ruwan ta jefa al’ummar yankin cikin mawuyacin hali.

Manoman da wakilinmu ya zanta da su a yayin ziyarar da ya kai a filin ban ruwa na Dam din na Balanga, sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta ba su damar ci gaba da noman su bayan shekara hudu ba su yi aiki ba.

A cewarsu, sama da mutum 900,000 ne abin ya shafa, yayin da wasu matasa da ma’aikatan gona suka shiga aikata laifuka saboda zaman banza.

Sun buƙaci gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace don dawo da hanyoyin rayuwarsu da kuma yaƙi da rashin aikin yi a cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Sakamakon ci gaban da aka samu, al’ummomin suna fuskantar munanan dabi’u yayin da ma’aikata da matasa wadanda a da suka tsunduma a cikin gonaki, sun dawo suna aikata laifi.

Wani manomin rani mai suna Yahaya Ali ya bayyana cewa madatsar ruwa ta Balanga ta zama hanyar rayuwa ga dubban jama’a musamman a garuruwan Balanga da Gelengu da Swa da Tula da Dong da Reme duka a yankin na Ƙaramar Hukumar Balanga a jihar ta Gombe da ma jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Sai dai ya ce shekara hudu da suka yi ba su yi aiki ba ya hana su shiga gonakinsu kamar yadda gwamnatin jihar ta ba da umarnin a rufe madatsar ruwa tare da zuba ruwa a magudanan ruwa don noman ban ruwa.

A cewarsa, wannan ci gaban da bai dace ba ya sanya manoman cikin wahala, domin a yanzu yawancinsu ba sa iya biyan buƙatun iyalansu.

Yahaya Ali mai shekara 58 ya ce rayuwarsa ba ta taɓa shiga irin wannan wahala da yake ciki a yanzu ba.

“Na shafe kusan shekara 30 ina aikin ban ruwa, kuma na dogara da shi ne kawai domin in ciyar da iyalina.

“Ayyukan ƙarshe a gonakinmu sun faru ne a shekarar 2019. Yanzu da muka shafe shekara hudu ba tare da noman ban ruwa a nan ba, abin da ke damunmu shi ne yadda za mu ciyar da kanmu.

“Rayuwa ta zame mana baƙin ciki saboda an mayar da mu marasa aikin yi.

Wani manomi mai suna Mista Abel Usman, ya shaida wa wakilin namu cewa shekara 30 da suka gabata, noman ban ruwa shi ne kadai abin da zai iya rayuwa.

Ya ce, “Na yi aikin noman ban ruwa sama da shekara 30. Kuma a kowace shekara muna sa wa kanmu haraji don share tarkace da ciyayi a magudanar ruwa kafin lokacin noman ban ruwa, kuma ana yin hakan ne ta hanyar hadin kai tare da taimakon gwamnati.

“Amma, a cikin shekara hudu da suka gabata, ba mu iya noman gonakinmu ba saboda gwamnati ba ta yi babban aikin share magudanar ruwa ba.

“Har ma mun yarda mu yi aikin gaba daya, amma gwamnati ba ta amince da tayinmu ba.

A gaskiya mun yi duk ƙoƙarinmu, har mun gaji a halin yanzu, amma har yanzu ba a sanar da mu a hukumance dalilin rufe dam din ba.”

A nasa ɓangaren, Malam Yusuf Musa, ya ce rufe madatsar ruwan ya yi illa ga rayuwarsu da kuma sanya daruruwan matasan da suke yin aiki a gonakin suka zama marasa aikin yi.

“Wannan abin baƙin ciki ne matuƙa saboda ya yi illa ga rayuwarmu.

“A yanzu matasanmu su koma zuwa wasanni a ƙarƙashin bishiya ne maimakon zuwa gonaki, yayin da wasu kuma a halin yanzu suna aikata abubuwan da ba su dace ba, wanda hakan ba shi da kyau ga makomarmu.

Kwamishinan Ruwa, Muhalli da kula da gandun Daji, Mohammed Sa’idu Fawu, ya ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin ganin an dawo da zaman lafiya a madatsar ruwa ta Balanga.

A cewarsa, shekara hudu da suka gabata ba a yi aikin noman rani a dam din ba, sakamakon wasu ƙalubale da ake fuskanta daga ciki har da batun tsaro.

Ya ce ruwan ba ya isa inda ake gudanar da manyan ayyukan ban ruwa, sauran manoman da ke kusa da madatsar ruwa ne ke dibarsa, wanda hakan ya haifar da matsalar tsaro tsawon shekaru.

Mohammed Fawu ya ƙara da cewa, saboda rahotannin tsaro da dama, a shekarar 2019, sai da gwamnatin jihar ta rufe dam din domin kaucewa taɓarɓarewar tsaro da rikicin ƙabilanci a tsakanin al’ummar yankin.

“Muna kan shirin dawo da ayyuka a wajen. Har ila yau, Gwamnatin Tarayya da Bankin Funiya sun fito da shirin samar da wutar lantarki na shirin SPIN kuma ina mai farin cikin sanar da ku cewa muna jiran fara aikin ne a watan Janairun 2025, kamar yadda suka yi alƙawari.”

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kuma tuntuɓi Hukumar Raya yankin Arewa maso Gabas (NEDC) a matsayin wani shiri na dawo da ayyukan dam din sosai.

“Muna da wani tallafi, wato Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC).

“A farkon wannan shekarar ne suka ziyarci wurin dam din, inda suka yi alƙawarin dawo da shi yadda ya kamata kafin ƙarshen shekara.

“Ina so in sanarwa da al’ummar Gelengu da yankin Gombe ta Kudu baki daya, cewa nan ba da jimawa ba kafin a fara kakar noman rani ina da yaƙinin cewa komai zai koma yadda ya dace,” inji shi.

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta shiga ƙungiyar BRICS

Gwamnatin Kano ta haɗa gwiwa da Media Trust kan inganta harkokin yaɗa labarai

Dokokin Haraji: Matakin gwamnoni bai wadatar ba – Ndume