Yadda ruwa ya ci matana 2 da ’ya’yana 6 a gabana – Sa’adu Asha

  Ruwa kamar da bakin kwarya da aka fara da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Asabar zuwa karfe 10 na safiyar Lahadi a kananan hukumomin Suleja da Tafa da ke Jihar Neja, ya yi sanadiyyar rasa rayuka 15 tare da bacewar wadansu mutane da har zuwa lokacin rubuta wannan labarin ba a ji […]

Yadda ruwa ya ci matana 2 da ’ya’yana 6 a gabana – Sa’adu Asha

 

Ruwa kamar da bakin kwarya da aka fara da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Asabar zuwa karfe 10 na safiyar Lahadi a kananan hukumomin Suleja da Tafa da ke Jihar Neja, ya yi sanadiyyar rasa rayuka 15 tare da bacewar wadansu mutane da har zuwa lokacin rubuta wannan labarin ba a ji duriyarsu ba.

Matsalar ta fi kamari a unguwannin Iraki da Checheniya da Kusfa da ke Karamar hukumar Suleja, yayin da a yankin Karamar Hukumar Tafa ta auku a Unguwar Hayin Nasarawan-Iku a titin Abuja zuwa Kaduna. Ambaliyar ta shafi gidajen da yawanci aka gina su a kan hanyar ruwa ne da kananan rafuka da ke yankin, kuma ta rusa gidaje sama da 100 baya ga wadanda ta yi wa illa, sai wasu kadarori da suka hada da motoci da kayan daki da gonaki da ke bakin ruwa da kuma dabbobi.

Aminiya ta zanta da Malam Sa’adu Abubakar Asha mutumin da ya rasa matansa biyu da ’ya’ya shida a ambaliyar bayan da ruwan ya shiga cikin gidansa da ke gefen rafi, wanda a yanzu ya zama fili tare da komawa yanayinsa na asali wato magudanar ruwa.

Malam Asha wanda dan asalin Karamar Hukumar Bungudu ne a Jihar Zamfara amma yake sayar da shayi da kuma aikin kafinta a Unguwar Checheniya da ke yankin Suleja, ya shaida wa wakilinmu cewa karfin ruwan ya karu sosai da misalin karfe 12:00 na dare sannan ya shafe malale dakunansu na kwana biyu inda ta nan ne mafitar gidan yake da misalin karfe daya na dare.

Ya ce “Ganin babu ta inda za mu fita sai muka kara matsawa ta baya inda dakuna uku da ban kai ga yi musu rufi ba suke, amma bayan jimawa kadan sai su ma suka rushe, sai muka koma ban-dakin gidan wanda ke da rami da rufi na kankare (sokawe) muka tsaya a kai saboda shi kadai ne ginin da ya rage a gidan.”

Ya kara da cewa, “Ina irake da ’ya’yanmu  biyu daya a hannun dama daya a hagu, uwargida tana goye da guda tana rungume da karama a hannu, sai amarya da ke goye da jaririyar da ta haifa mako biyu da suka wuce, sai kuma babbar ’yarmu mai shekara 13 tana tsaye a tsakiyarmu, ana cikin haka sai sokawen shi ma ya rubza nan ruwan ya janye mu gaba daya muka rabu.”

Ya ce ya yi yunkurin ya riko ’ya’yansu biyu da suke hannunsa bayan ya nutse tare da su a cikin ruwa amma koda ya yi iyo zuwa sama sai ya ga ruwan ya kwace su.

Malam Sa’adu wanda ya ce kamar shekara guda ke nan da karasa gina gidan sannan ya tare cikinsa wata shida da suka gabata, bayan ya shafe kamar shekara uku yana faman gina gidan. Ya ce bai san cewa gidan ne zai zame masa sanadiyyar rabuwa da daukacin iyalansa ba, a lokacin da suka tare zuwa gidan daga inda suke haya a unguwar.

“Ni kaina duk da ruwan da na dan iya da kyar na sha bayan na samu makalewa a jikin wata bishiya da ke gabar ruwan sannan bayan na dan huta sai na kula ashe ina kusa da bakin ruwa daga nan ne na yi tsalle na fito, na rika tafiya ina faduwa saboda kafafuwana sun gaji sakamkon jansu da ruwa ya rika yi a lokacin da na makale a jiki bishiyar,” inji shi.

Ya ce ya koma wurin tare da sauran ’yan uwansa bayan ya sanar da su lamarin, amma ba abin da suka gani in ban da ruwan wanda ya rika karuwa. Ya bayyana sunayen iyalan nasa kamar haka: “Uwargida Suwaiba na auro ta ne daga garinsu Mafara, sai amarya Hajara daga Magami. ’Ya’yana kuwa su ne babbarsu Ikilima mai shekara 13 sai Musa mai shekara 9 da Yusuf mai shekara 6 da Zainab mai shekara 4 da Asma’u tana neman shekara daya, sai kuma jariyar amaryarta mai suna Nana Khadija da ke da mako biyu da haihuwa.” Ya ce da farko lamarin ya jefa shi a cikin rudu sosai amma bayan wa’azi da masu zuwa gaisuwar ta’aziyya suka rika yi masa da kuma bukatarsa ya rika yin addu’o’in neman karin kusanci ga Allah, yanzu ya fara samun saukin lamarin kuma ya maida komai ga Allah.

Ya ce an gano gawar mutum biyar a cikin iyalansa amma har yanzu ba a kai ga gano ’ya’yansa uku ba ciki har da babbarsu.

Aminiya ta samu labarin cewa akwai kuma karin wadansu mutum biyu da aka rasa a unguwar sakamakon ambaliyar da suka hada da wata matar aure da wani matashi, kamar yadda Mai unguwar Checheniya Malam Nuhu Shu’aibu ya tabbatar.

Haka ruwan ya ci mutum guda a Unguwar Kusfa inda wani matashi mai suna Idris Faruk da ya fada a rafin unguwarsu ruwan ya ja shi kuma har zuwa lokacin hada wannan labarin ba a ji duriyarsa ba.

Wani dan uwan marigayin mai suna Alhaji Musa Sahabi, ya ce matashin wanda gwanin ninkaya ne, binciken da suka yi bayan ruwan ya wuce ya nuna cewa ya fada ne a kan wani ginin kankare da ke hade da wani gida da ruwan ya malale bisa rashin sani, inda ake kyautata zaton ya buga kansa ne a kankaren kamar yadda wani yaro da ya rike masa suturunsa bayan sun je bakin ruwan, ya ba da bayani.

A bangaren Hayin Nasarawan-Iku kuwa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a Karamar Hukumar Tafa, mutum hudu ne aka tabbatar da rasuwarsu kamar yadda Dagacin yankin Malam Abdulkarim Samanja ya bayyana. Ya ce mamatan sun hada da: Yusha’u Sulaiman mai shekara 20 da Mu’azu Aliyu wani almajiri mai kimanin shekara 21 da Haruna Adamu mai shekara 18, sai kuma wata jaririya da ba a tantance ta ba.

Ya ce gidaje kimanin 70 sun rushe a yankin sakamakon ambaliyar yayin da wasu da dama suka lalace baya ga asarar amfanin gona da dabbobi.

A zantawarsa da wakilinmu a yayin ziyarar jaje da gani da ido da ya kai Unguwar  Checheniya, Shugaban Karamar Hukumar Suleja, Malam Abdullahi Shu’aibu Maje ya ce garin Suleja wanda ke matsayin alkarya, hurumin ikon tsara gine-ginensa da tsawatarwa a kai na hannun Gwamnatin Jihar Neja ne ta hannun Hukumar Kula da Tsara Gine-Gine. Ya ce a matakinsu na karamar hukuma bai wuce fadakarwa da kuma tuntuba ba. Sai dai ya ce karamar hukumar za ta tattara rahoto a kan al’amarin tare da mika wa gwamnatin jihar don daukar mataki.