Yadda ruwa ya ci ‘yan sanda a kokarinsu na kama ‘yan wiwi
‘Yan sandan sun makale a cikin tabo, sai da aka kawo buldoza kafin a iya ciro gawarwakinsu.
Wasu ‘yan sanda su uku sun gamu ajalinsu a lokacin da suke kokarin kama wasu ‘yan ganye a unguwar Balogun a Jihar Oyo.
Kuratan ‘yan sandan da ke aiki da caji ofis na yankin Atiba, sun yi kokarin kame wasu matasa ne da suka iske suna zukar tabar wiwi.
Nan take matasan suka tsere, su kuma suka bisu domin su kamo su.
Wani shaida mai suna Okunola Abbas, ya ce daya daga cikin matasan da ya ga ‘yan sandan sun kusa cin masa sai ya fada cikin wani kududdufi, nan take ‘yan sandan su ma suka bi shi ciki.
“Yan sandan su hudu sun yi kicibis da mashayan ne a daidai lokacin da suka fito daga cikin motarsu ta aiki, ko da suka bi su a guje sai daya daga cikin matasan ya fada cikin kududdufi, nan take uku daga cikin ‘yan sandan suka bi shi cikin ruwan.
“Shigar ‘yan sandan ruwan ke da wuya sai suka makale a cikin tabo, har sai da aka zo da motar buldoza wacce ta fito da gawarwakinsu”, inji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da faruwar lamarin, da kuma kame mutum hudu da ake zargi da hannu a lamarin.
Ya ce, ‘yan sanda sun je su kamo wasu da ake zargi da aikata laifi ne, sai daya daga cikinsu ya fada ruwa, ‘yan sandan suka bi shi cikin ruwan domin su kamo shi”.
Ya ce lamarin ya faru ne ranar 12 ga watan Yuli, 2020.