Yadda ruwan Naira 20 ya jawo mutuwar matashin da ke gab da aure
An ce sanadi ba ya kadan kuma kowa da irin kaddarar da Allah ya diba masa, kamar yadda wani matashi mai shekaru 22 mai suna Shawilu Shehu Allah Gaba da ke Unguwar Bakin Kura a Bauchi , wanda kuma yake sayar da nama da ake kira tukunya, sayan ruwa da yayi na N20 ya yi […]

An ce sanadi ba ya kadan kuma kowa da irin kaddarar da Allah ya diba masa, kamar yadda wani matashi mai shekaru 22 mai suna Shawilu Shehu Allah Gaba da ke Unguwar Bakin Kura a Bauchi , wanda kuma yake sayar da nama da ake kira tukunya, sayan ruwa da yayi na N20 ya yi sanadin rasuwarsa, sakamakon takaddamar da suka yi da wacce ya sayi ruwan a wajenta kan neman ya canja mata Naira hamsin din da ya ba ta, shi kuma ya ki.
Da yake zantawa da Aminiya, dan uwan mamacin mai suna Yahuza Shehu Allah Gaba, wanda mahaifinsu daya da mamacin, ya ce bayanan da suka samu dangane da sanadiyyar rasuwar danuwannasu shi ne, da farko ya dawo gida ba shi da lafiya , sai ‘yan uwansa suka kai shi asiubiti da kukan cewa zazzabi ne da amai yake damunsa.’’ Bayan ya rasu daga baya sai dan uwanmu Bilal Shehu ya yi mana waya yake cewa sun samu bayani na gaskiya cewa mutuwar Shawilu sababinsa duka ne da ‘yan kwamitin Unguwar Wunti suka yi masa. Shi ya sa ya dawo gida yana aman jinni, har ya kai ga aka kai shi asibiti Allah Ya karbi rayuwarsa.”
‘’Abin mamaki da kuma kaddarar Ubangiji, lokacin da aka kai shi asibitin ba a yi masa komi ba har Allah ya karbi ransa, don Jami’an asibitin sun yi zaton mummunan zazzabin nan ne na beraye (Lassa feber).’’
Ya kara da cewa, ‘’Sai da muka rubuta takardar janye koken rashin lafiyar da muke zaton shi’ke damunsa ga asibitin kafin daga bisani suka amince suka yi mana bincike suka gano ainihin abin da ya kashe shi, inda suka tabbatar mana da cewa, ya rasu ne sakamakon dukan da ya sha.’’
‘’Sai aka ce tunda ina da babban waya in yi sauri in je asibitin kafin a kammala cike-ciken takardu a bude mini gadon bayansa domin inga irin dukan da aka yi masa mu dauki hoton gadon bayan, kuma aka kira babban wanmu, Alhaji Yusuf dan Isubulle, muka je muka fada wa ‘Yan sanda a ofishinsu na yanki (Area Command).’’
‘’Daga nan sai muka koma da su Asibitin har da ‘yansandan, sai wanda yake bin dan Isubullen, wato Bilal shehu, ya bayyana mana ainihin gaskiyar abin da ya faru ya yi sanadin wannan jinya da Allah Ya karbi ransa a ciki. Abin da ya faru tun farko, Rigima ce ta hada shi da wata yarinya, ya sayi ruwa na Naira ashirin (N20), sai ya ba ta N50 ta ba shi canjin N30 , Yarinyar sai ta ce Naira hamsin N50 din da ya ba ta ta tsufa ba za ta karba ba , shi kuma ya ce kudin yana da kyau, don shi ma a wajen da yake sayar da nama aka ba shi, ya ki ya canja. Da ya ki ya canja sai ta zagi ubansa, shi kuma jin zafin zagin sai ya mare ta, ita kuma da ta ji zafi sai ta kira dan uwanta ta fada masa cewa ga wani a kan hakkinta ya mare ta, shi kuma dan uwan nata yana daga cikin ‘yan kwamiti , sai suka zo suka yi ta dukansa , sai wani daga cikinsu ya ce su dauki yarinyar su kai ta asibiti, da tunanin cewa dukan da suka yi wa yaron ya yi tsanani, za a iya daukar mataki, don haka za su nuna sun kaita asibiti har an yi mata jinya. Amma ba rauni ba jin jiki a jikinta. “
Ya ce, ‘’daga karshe aka yi bincike a ofishin yanki na ‘yansanda, daga nan kuma aka koma da mu sashin binciken manyan laifuffuka na yan sanda (CID), daga wajen kuma aka kai su kotu, alkali ya tura wadanda ake tuhuma gidan Yari, ya kuma daga sauraron karar sai bayan wata guda.’’
‘’Abin da muka fahimta shi ne, sun yi amfani da sanduna wajen dukansa, don da sanda suka doke shi a wajen zuciyarsa, shi ne ya jawo yin aman jinin da yake yi. Abin mamaki, kafin ya rasu, shi da kansa ya kai su kotun shari’ar musulunci na Kobi, don mun ga takardar da ya shigar da kara kan haka a dakinsa bayan ya rasu,saboda yana jin tsoro idan ya fada a gida za a ce ya janye .’’
Ya cigaba da cewa, “Wadanda ake tuhuma dukansu babu wanda ya zo mana ta’aziyya. Amma bayan alkali ya tura su gidan Yari sai wadansu suka biyo sawu ta zauren sulhu din na kwamitin da nufin a sasasmta a yi hakuri, amma sai Baba Sallau ya ce musu, ‘’ku naku kuna iya ganinsu, har ma an ba ku dama mutum daya daga cikinku ya kai musu abinci, amma mu namu yana kwance a kabari ba mu da ikon ganinsa, ba ku zo kun yi mana ta’aziyya ba kuma ba ku zo kun ba da hakuri tun da fari ba, saboda ku naku mutane ne, mu kuma namu ba su da gata ko ba mu san darajarsu ba, shi ne za ku zo mu sasanta ?”
Ya ce mamacin bai yi auren fari ba, amma har ya kai sadakin aurensa, ba a kai kaya ba, Allah Ya karbi kayansa, sakamakon dukan da ‘yan kwamiti suka yi masa.
Yahuza ya ce, su dai suna bukatar a hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki. Batun diyya kuma wannan sai idan ‘yan uwa sun zauna sun yi shawara.
Wadanda suka zanta da wakilinmu kan al’amarin, sun ce lokacin da mamacin ya mare ta sai ta fadi, kamar a ce tana da jinnu, ta suma, kuma daga bisani aka kai ta asibiti. Kusan dukkan hukuncin da aka yi wa mamacin ba ta sani ba, daga baya ne ‘yan sanda suka dauki jawabinta aka sallameta, wato bayan an bayar da belinta.
Wakilinmu ya je ofishin kakakin rundunar ‘Yansanda da ke Bauchi, DSP Kamal Datti, don samun karin bayani kan al’amarin, amma ya samu ya yi tafiya, amma mataimakinsa ya ce zai bincika ya ba mu bayani, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wani bayani daga bangarensu.
Wakilinmu ya ziyarci Kotun da ake tuhumar wadanda ake zargi su uku, masu suna Uwaisu Ahmed da Adamu Abdullahi da Shamsuddin Abubakar, dansandan mai gabatar da kara Insifekta Zakari Mohammed, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhuma Kwamishinan ‘yan sanda yana karansu ne bisa tuhumarsu da laifin hadin baki da kuma kisan kai.
dan sandan ya shaida wa kotun cewa, dan uwan mamacin mai suna Bilal Shehu, ya kai koke ofishin ‘yan sanda inda yake zargin wadanda ake tuhuma da hadin baki suka kai shi ofishinsu suka aske masa kai, suka doke shi da dorina, sakamakon haka ya samu rauni a jikinsa kuma suka kai shi asibiti don a yi masa magani amma ya rasu a ranar da aka kai shi.
Ya ce aikata hakan laifi ne da ya saba wa sashi na 96 da sashi na 221 na kundin aikata manyan laifuffuka.
Bayan da ya kammala gabatar da karan, sai Alkalin kotun Aminu Ilelah, ya tambaye su ko sun fahimci tuhumar da ake musu? suka ce eh, sai ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba 2017, ya ba da umurnin a tsare wadanda ake tuhuma zuwa wannan rana, ya kuma ba su dama su dauki lauyan da zai kare su.