Yadda ruwan saman awa 11 ya shafi harkoki a Kano
Ruwan ya yi ajalin rayuka, gidaje sun rushe, sannan harkokin neman abinci sun samu matsaloli
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe kusan sa’a 11 ana yi a garin Kano ya yi sanadiyyar asarar rayuka da rushewar gine-gine da sauran matsaloli.
A sakamakon ruwan saman, titunan Kano da dama sun cika da cunkosan ababan hawa, saboda rashin wadatattun ingantattaun tituna.
- A karo na 5 a 2022, wutar lantarkin Najeriya ta sake daukewa gaba daya
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a kauyen Kaduna
An kuma samu toshewar magudanan ruwa da ke makwabtaka da manyana titunan da unguwanni, da sauran matsaloli a banagaren ababan more rayuwa a jihar.
Matsalolin da ruwan saman da aka tafka a ranar Lahadi ya bayyana irin bukatar da ake da ita na maida hankali wajen magance matsalolin, daga banagaren gwamnati har zuwa al’umma.
Tun a farkon faduwar daminar bana dai mutane da dama da masu ruwa da tsaki a Jihar Kano ke ta kiraye-kiraye ga gwamnati da ta dauki matakin bude magudanan ruwa da kuma dagewa wajen tabbatar da jama’a suna gyaran muhallansu, don gudun ruwan ya yi wa kansa hanya idan ba a fitar masa ba.
Da faduwar daminar ba jimawa dai aka wayi gari katangar Ofishin Hukumar Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) da ke unguwar Rijiyar Zaki ya fadi.
Irin abin da ya faru ke nan da doguwar katangar dadaddiyar makarantar Kwalejin Rumfa daga bangaren mahadar Titin Kofar Dan Agundi.
Zuwa yanzu dai an kammala gina katangar Ofishin Hukumar NYSC, ta Kwalejin Rumfar kuma ana kan gyaran ta.
Sai dai alamu na nuna idan har ba duka katangar aka sake ba, to da sauran rina kaba, domin kuwa wani bangare nata da bai rushe ba a baya ya fara tsagewa.
Cunkoson ababen hawa
Aminiya ta lura da yadda wasu titunan Kano ramukansu suka yi yawa da kuma fadi, lamarin da ya sanya motoci suka dinga makalewa a ciki a yayin da ake wannan ruwa.
Hakan ya tilasta wa wasu masu ababen hawa ajiye ababan hawansu su nemi babura masu kafa uku wadanda su ma ke gwagwarmayar laluben hanyoyin da suka sani da ke da karancin wannan matsala.
Masu ababen hawa sun shafe sama da awa biyu a cikin ‘go-slow’, tsakanin sabuwar harabar Jami’ar Bayero da Kofar Kabuga.
Duk da cewa tafiyar ba ta wuci kilomita baiyar ba, amma cunkoson ababen hawa da ramuka da kuma cushewar magudanan ruwan da ke hanyar sun sanya motoci shafe tun daga yammaci zuwa dare kafin samun ficewa.
Bangaren kasuwanci
Haka zalika tituna da suka shuga a unguwanni da dama da ba su da kwalta, an samu makalewar ababan hawa.
Akwai kuma banda masu sana’o’i da suka fito ba su sami ciniki yadda suka saba ba, kasancewar an wuni ana ruwa, kuma wadanda suka fito suna Allah-Allah su isa gida.
Masu kasuwanci a hanyoyi
Aminiya ta zagaya wasu daga wuraren da ake gudanar da sana’o’i a kan hanya irinsu titin zuwa gidan Zoo, da ake samun masu Kayan Gwari da doya da dankali, har ma da masu rataye kayan sawa na siyarwa.
Sai dai mun lura kafin Azahar da ruwan ya fara karfi, wasu sun fito sun baza hajojinsu, amma daga bisani sun kwashe sun bar wurin, musamman ma masu kayan da ba sa son ruwa.
Da misalin karfe biyar dai kofar shiga Ado Bayero Mall da ake fi sani da Shoprite da ya saba cika da matasa musamman mata da dattijai da ke zuwa shan iska, ya kasance tsit, bayan da ruwan da yafi na sauran sa’o’in karfi ya kwace kamar da bakin kwarya.
Hakan ya sanya masu babura masu kafa uku durfafar gurin suna diban fasinjoj suna kara musu farashi — ko hawa ko kuma ruwa ya yi maka duka.
Mun tattauna da wani mai babur din da ake kira A Daidaita Sahu a jihar, inda ya bayyana cewa shi fa sai hamdala duk da ruwan ya yi masa duka, da kuma kudin da ya kashe wajen gyaran babur din nasa washegari.
“Na samu ciniki sosai gaskiya, musamman ma fasinjoji mata da ba su san kananan hanyoyin da za su iya bi su kauce wa cinkoso da ambaliyar ba ko da suna da abin hawa.
“Nakan kara kamar Naira dari kan ainihin farashin da muke dauka saboda lillahi wa rasulihi fetur muke konawa a kaucewa hanyoyin, kuma kowa ya san fetur ya tashi, idan mukamce a farshin ainihin za mu dauka faduwa za mu yi”, in ji shi.
Mun zanta da musu siyar da kayan hatsi da kayan miya da na kananan shagunan cikin unuguwa, inda su kuma suka koka cewa cinkin ranar da aka yi wannan ruwa fa sai dai hakuri.
Wani mai shago a Unguwar Wambai da ke karamar Hukumar Gwale ya ce: “Kafin Magariba da ruwa ya tsinke soai da sosai, dawowa muka yi bakin shago muna kallon ikon Allah.
“Wanna titin namu ya fi shekara bakwai a lalace, duk damuna masu abi n hawa ba sa son bin sa.
“Don haka da aka samu amabliya atitin abin ya kazance, haka muka dinga tare wa mata motocin kurkura muna dora su da yaransu saboda tausayi da kuma yadda ruwa ke jan mutum saboda yawa”.
Ya kuma ce sun taimaka wa masu abin hawa da dama da ko don rashin sani ko kuma don hanyarsu ce ta dole da ababan hawarsu suka dinga mutuwa ko fadawa rami, kuma rabon da ya ga ruwa mai tsawo da yawa irin wannan ya manta.
Samun Rahotannin Ambaliyar a Hukumance
Babban Sakataren Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Kano SEMA Saleh Jili, ya ce babu wani kiran gaggawa da suka samu kan ambaliyar, duk da sun samu rahotannin da ba na hukumace ba kan ambaliya da cunkoson ababen hawa, da kuma rushewar gidaje.
“Mun samu labarin yadda aka samu ambaliya a manyan tituna irinsu Kabuga, da kuma kauyuka irinsu Kumbotso, don yanzu haka ma akwai takarda da aka aiko mana kan samu rusau sakamakon ruwan a kauyen Kumbotso, amma dai magana ta gaskiya ita ce mun sama ba za a rasa samu ba, rahoto ne kawai ba a kawo mana ba”.
Ya cigaba da cewa, “Misali kinga akwai labarin da muka samu na wata gawa da aka tsinto a wata magudanar ruwa da ke kusa da Asibitin Malam Aminu Kano, yanzu haka ma ’yan sanda sun shiga lamarin don binciken ko ambaliyar ce ta yi sandiyar rasuwarta, ko kuma a wani gurin daban ta rasu, ruwan ya turo gawarta zuwa nan”, in ji shi.
Mun tuntubi Kakain Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya ce tuni sun samu iyayen yarinyar har sun mata suttura sun binne ta.
“Amma dai mun a cigaba da bincike duk da ba a samu ko kwarzane a jikin gawar tata ba.”
Mun yi yunkurin ji ta bakin Ma’aikatar Muhaklli ta Kano kan lamarin, da ma shirye-shiryen da suke yi na idan an sami makamancin wancan mamakon ruwan a jihar a gaba.
Sai dai daga Kwamishinan har Kakakin hukumar babu wanda ya daga waya ko amsa sakon da muka tura musu yayin hada wanna rahoton.