Yadda sababbin al’adu suke janyo tsadar aure

A haka ne ake samun masoya su dade suna soyayya, amma auren bai yiwu ba.

Yadda sababbin al’adu suke janyo tsadar aure

Bikin aure

Matasa da dama sukan nuna sha’awar yin aure, amma a lokuta da dama sukan yi korafin cewa tsadar aure tana hana su yin auren, wanda idan ba a yi sa’a ba, yakan jefa wadansu matasan a cikin wani mugun hali.

A irin haka ne ake samun masoya biyu, sun dade suna soyayya, amma auren ya ki yiwuwa.

Aure a da

A baya ana gudanar da bukukuwan aure ne ta hanyar bin al’adun da aka gada iyaye da kakanni masu sauki, lamarin da yake sa a gudanr da komai cikin sauki ba tare da tsawwala wadukan vangarorin biyu ba.

Al’adu irin su kayan na-gani-ina-so ko kayan zance da kayan lefe ana yin su ne daidai karfin mutum ba tare da dora wa kai abin da ba za a iya ba. Yawancin wadanan kaya na na-gani- ina so ko kayan zance tufafi ne da kayan kwalliya da suka kunshi man shafawa da na kitso da katamburi ko jagira da hoda da sauransu.

Haka al’adun da ake yi wajen gudanar da shagulgulan biki su ma a kan saukaka su ba tare da dora wa kai wahala ba.

Misalia da a kan gudanar da bukuwkuwan ne aacikin gida, ko da gidan da ake bikina karamine haka za a yi amfani da sorayen gidajen makwabta don zaman ’yan biki.

Yadda sababbin al’adu suke janyo tsadar aure

Sai dai bayan shigowar bakin al’adu cikin harkar aure wadanda ake ganin Bahaushe ya same su ne daga cudanyarsa da sauran kabilun kasar nan, hakan ya anyo abubuwa sun yi tsauri har ya kai aure yana neman ya gagari mai karamin karfi.

Sabuwar al’adar nan ta yin shagali wanda a mafi yawan lokaci ango ne yake daukar mauyin gudanarwa, ta zama ruwan dare inda ake ganin idan ango bai shirya wannan biki na ‘fati’ ba, ya gaza, wanda kuma zai iya shafar zaman auren nasu idan ma ba a yi sa’a ba daga nan za a iya fasa auren.

Idan mutum zai yi lissafin irin kudin da ake narkawa wajen yin biki kama daga hayar wurin da za a kama da kudin abincin da za a ci da na mai kida (DJ) da na san-kira da na masu daukar hotuna da sauransu kudi ne da za su iya zama jari ga wani.

A wasu lokuta kuma zai kasance ba wai shagali daya za a yi a bikin ba, akwai su Ranar Iyaye Mata na bangaren amarya da na bangaren ango da Ranar ’Yan Uwa Mata da Ranar Larabawa da Ranar Kauyawa da sauransu wadanda dukkansu suke lashe kudi masu yawan gaske.

Sannan a daren aure a tafi liyafar cin abinci, inda nan ma ake cin wasu kudaden.

Kayan lefe

Duk da cewa tun zamanin iyaye da kakanni ake yin kayan lefe, sai dai a yanzu an shigar da wasu abubuwa a cikin lamarin da ya kara tsadar aure ga samari.

A da kayan lefen da ango ko danginsa za su hada ba sa da yawa kuma ba a damu da yinsu cikin wani tsari ba. Kowane kaya aka samu sanyawa ake yi a cikin kwallako kumbo ko fantimoti.

Haka a baya ba a damu da sai an cika kwallaye da kayan ba.

Sai dai a yanzu abubuwan ba haka suke ba, idan ango zai hada lefe komai rashin jarfinsa, sai ya sayi jerin akwatuna wadanda suke farawa daga uku zuwa sama.

Kuma ana tunanin wadanan akwatuna sai an makare su da kaya na gani na faxi, na nuna wa sa’a.

Baya ga tsarin tufafin a gefe guda ga takalma da jakunkuna wadanda dole a samu masu launi iri guda abin da ake cewa “to match.”

Sannan a samu wani akwati a makare shi da kayan shafe-shafe na mata.

Irin wadannan kayan lefe suka sa matasa suna yi wa abin lakabi da “Sa maza olsa” saboda yadda samari suke takura kansu da matse bakin aljihun don ganin wancan bukata ta biya.

Nuna kayan ne yake kawo matsala

Wata sabuwar al’ada ta daban, bayan an kai kayan lefen, sai a kira dangi da makwabta da abokan arziki a zo a ga kayan, wanda hakan ne yake sa dangin amarya su tursasa angon cewa dole ya yi kokari ya fitar da su kunya.

Binciken Aminiya ya gano cewa sha’anin lefe ya kai ga cewa a wasu wuraren har fasa aure ake yi idan aka ga lefe bai hadu ba, ma’ana bai yi daidai da abin da gidan amaryar suke tsammani ba, inda kuma suke gani abin kunyane a gare su, su fito su nuna wannan kaya ga jama’a don haka sukan dauki lefen su mayar gidan angon da niyyar a sake yi musu wani.

Idan an yi rashin sa’a aka hadu da masu zafin kai daga nan maganar aure take lalacewa.

Muna cikin wani hali – Matasa

Matasan da Aminiya ta tattauna da su sun soki wadannan bakin al’adu inda suka yi kira ga iyaye su yi watsi da su tare da kiran hukuma ta shigo ciki don tabbatar da an yi abin da ya dace a kan lokaci tun kafin abubuwa su kara lalacewa.

Usman Abba wani matashi ya nuna takaicinsa game tsadar aure, inda ya ce, “Da a ce gwamnati da gaske take yi to da za ta dauki mataki a kai, to na tabbata za a daina wadannan al’adu da suke hana matasa aure. Yanzu idan kika dauki Gumel tuni Masarautar Gumel ta dauki matakin hana lefe gaba daya a yankin. A yanzu duk wacce za a aura to ba za a yi mata lefe ba sai dai mijin zai iya saya mata kaya idan ta tare a gidansa ya ba ta,” inji shi.

Shi kuwa Sani Jibrin ya bayyana sababbin al’adun da abin da yake kara
tabarbarewar harkar aure yana janyo ’yan mata suna nan suna yawo a gari ba tare da aure ba.

Ya shawarci hukuma ta sa doka cewa a daina yin lefe gaba daya sai dai mutum ya sayi wasu kaya da zai ba matarsa idan ta tare a gidansa don ta riqa yi masa kwalliya da su.

Idan namiji bai kashe kudi ba, raina matar yake yi – ’Yan mata

Sai dai yayin da maza suke sukar wadannan baqin al’adu, a bangaren ’yan mata goyon bayan abin suke yi.

Umma Aminu budurwa ce a Kano ta ce lamarin tsadar aure fa ya danganta da tunanin mutum, domin kowa yana daukar abin da zai iya yi ne.

Ta ce, “A ganina mutane ne suke damun kansu, kowa yana yin abu ne daidai da samunsa.

Idan mutum yana da hali sai a ce ba zai kashe kudi lokacin aurensa ba? Abu ne fa na lokaci daya idan ya wuce ya wuce, ba zai sake dawowa ba. Ni ina ganin komai yawan dukiyar da mutum ya kashe a aurensa bai zama asara ko almubazzaranci ko barna ba.”

Jamila Bature cewa ta yi idan har maza ba su kashe kudi sosai a wurin aure ba, ba sa ganin darajar matar domin suna ganin sun same ta ce a arha. Don haka a ganinta a ci gaba da gudanar da al’adun aure yadda suka kamata.

“Namiji idan ya san ya sha wuya kafin ya samu mace ya fi lallaba ta. Domin ya san jikin da ya ji. Kuma ya san idan ya sake ta, hakan zai sake sanya kudinsa ya auro wata ba za a ba shi kyauta ba. Kuma ba na goyon bayan cewa wai maza su rika saya wa matansu kaya idan sun tare a gidajensu wannan ba abu ne da zai yiwu ba, domin zai ga cewa ai ya riga ya samu matar to me zai sa ya tsaya kashe kudinsa. A takaice dai da wuya a samu mazan da za su cika wannan alkawari,” inji ta.

Ita kuwa Hafsat Ahmad cewa ta yi, “Duk da cewa ban yi aure ba, amma ba na goyon bakin al’adun nan domin wallahi su suke hana mu aure. Yanzu ’yan mata nawa ne suka kammala karatu suke neman mijin aure ba wai don babu masu sonsu ba ne, a’a illa dai tsoron da mazan suke ji saboda abin da za a iya nema daga wurinsu na al’adun aure wadanda suka fi karfin aljihunsu. Kuma a wasu lokacin za ki ga angwayen sun yi lefen amma sun koma suna sace kayan daya bayan daya.”